29

25 3 0
                                    

"Wayyo Allah billy my husband to be is back, shirya ki rakani dan Allah".....
Eesha ta fada cike da murna....
"Iyee na tayaki murna, Dr dinne ya dawo?"....
Dayake eesha na yawan basu labarinsa, su sun dauka soyayya suke sosai dan har waya take nuna musu tanayi dashi....
"Eh wallahi shine, ke tashi mu fara shiri zuwa anjima zamu tafi, kunyar zuwa gidan surikai nake ni kadai".......
Karab Umaima tace;
"Dan Allah nima zani, in shirya muje?".....
"A'a wallahi yi zamanki kafin muje kimin wuff da saurayi, waye baisan halinki na snatching ba? Gwara billy nasan maza basa gabanta so hankali kwance zanje da ita"........
"Mtssss sai kije ki cinyeshi ai, in snatching din zanyi sai in miki? Kila ma be hadu ba mtsssss"....
"Karki kuskura ki gayamin maganar banza, nasan har ki mutu bazaki taba haduwa da kamarsa ba wallahi, ke tsayawa miki describing dinsa bata lokaci ne shiyasa zan tafi da billy atleast zata baki testimony mtsssss"......
"Rabu da ita eesha, waye besan halinta ba? Niko dama anything that has to do with man kinsan I'm out so baki da case, dama dai wata fine babe dince ehnn, anyway mu fara shiri toh"....
Billy ta fada tana dariya.....
"Karki batamin rai kema, da anfara maganar arziki dake saikin nuna hali ko kunya bakyaji"....
"Sorry ma'am, zo in fara miki kwalliya yanda zaki rudasa ya kasa ganin kowa saike kawata"....
Cikin farin ciki eesha tace;
"Yauwa shiyasa nake sonki wallahi, zoki tayani zaban kayan daya kamata nasa"....
"Bakida case kawata"....

Tinda suka gama waya da eesha take zaune tana tinanin yanda zata billowa al'amarin, damuwarta daya yanda Deen ze karbi lamarin amma abu daya ta sani ko yanaso ko bayaso dole ya amince, ta dade da sanin eesha nasan Deen dan aminiyarta wato mahaifiyar eesha tasha nuna mata su hada ya'yansu aure kuma ta amince da hakan dari bisa dari dan ta yarda da tarbiyyar eesha sosai....
Tana cikin wannan hali Umm tashigo ta sameta..
Dafa kafadarta tayi tace;
"Meyafaru? Why are you looking disturbed?"....
"It's Saif's dad!"....
"Shi yazo?, meyace miki toh?".....
"Wai aure zeyiwa Saifuddeen, kuma yana san dansa ya dawo kusa dashi, kinji wata maganar banza?"....
"Toh menene dan ya masa aure? Inace ya isa auren? Yanada aikinshi da arzikinshi da komansa so why bothering?".......
Cikin bacin rai mami tace;
"Kinji wai auren mafa he has someone for him, bansan wacce ze hadashi da ita bama".....
"Bangane someone for him ba? Ina lefin abar yaro ya zabo abarsa da kansa"......
"Nima dai shi nagani, nasan bazai wuce fitsararrun ya'yan abokansa ba shiyasa nace masa be isaba nima inada wacce zan hadasa da ita kuma saidai ya hakura ya bari ya auri zabina dan bazan yarda ya auro wacce ban yarda da tarbiyarta ba".....
Tinda ta fara magana Umm ta sake baki tana kallonta kamar hoto, saida ta dire sannan tace;
"So what do you guys mean by trying to make your son's life a game, so kuke kuyita playing dinshi kamar wani toy? Bazaku bari fadanku ya tsaya iya ku kadai ba sai kun sashi? Haba yaya!"......
"Huh idan baki fahimce niba wazai fahimceni Jamila, why are you always like this in my hard time?".....
"Ni bawai ban fahimceki bane the thing is that he has his right to choose a wife bawai kuyi masa auren dole ba kamar a kauye?"......
"Nidai tinda kika koma UK you start thinking like foreigners! Da anyi magana kice right right!, shikenan yaro bazeyiwa iyayensa biyayya ba?, just tell me you're not ready to support me kawai, dama kinsaba bin bayansa ba yau kika fara ba"......
Murmushi Umm tayi tana girgiza kai tace;
"No pls karkice haka yaya, you know I got your back anyday anytime, idan banyi supporting dinki ba wa zanyi supporting? Yanzu ya kikeso ayi toh?"....
Wani ajiyar zuciya Mami ta sauke tana dan murmushi, dama tasan inba haka tayiwa Umm ba tsap sai tace ba ruwanta kuma Deen sai yafi saurin amincewa idan Umm tasa baki dan Umm akwai dabara.....
"Yauwa ko kefah yar'uwa, yanzu so nake ki tayani shawo kan dan naki ya amince"......
"It's ok yanda kikace haka zaayi, amma wa zaki aura masa?".........
"Eesha! Yar gidan Hajiya Saratu".....
Dan jimm Umm tayi sannan tace;
"Toh shi Saif din yana sonta ne?".....
"Gsky rabonsa da ita tun tana karama, I just want them to bond now, I believe it'll work out!"....
"Toh Allah yasa, niko sai naga kamar yana san yarinyar nan daya kawo fah, ko zamu kara tambayarsa ne?"......
"Wlh be isaba I've given him enough chance and you were the witness! And I'm sure zeso eesha dan tanada kyawawan hali".......
"I am not against eesha din tinda nasan mahaifiyarta mutuniyar kirkice same with itama but I want you to give him one last chance about this girl, nida kaina zan masa maganar eesha zan kuma nuna masa ya fadamin gsky idan har yana san ita fatima zainab din I'll help him ayi canceling maganar eesha, anything he says will be the final say I promise you!"..
"Shikenan! Anjima eesha zata zo"....
"Allah ya kawota lafiya"......

WACECE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)Where stories live. Discover now