24

27 0 0
                                    

     Da sauri fatima zainab tayi kanshi tana kokarin shako wuyarsa kozata samu ta kasheshi ta wuta, kamar ana zugata so take kawai taga baya numfashi.....
Fuzgota yayi da karfi yana damke hannayenta da suke kokarin shakesa, hugging dinta yayi sosai yana mannata da bangon kofar.....
Fizge fizge tashigayi tana neman kwace kanta yasa mata karfi sosai ya matseta sannan yayi bismillah ya fara karanto suratul mulk kamar haka;
    "Tabaarakal lazee biyadihil mulku wa huwa 'alaa kulli shai-in qadeer
Allazee khalaqal mawta walhayaata liyabluwakum ayyukum ahsanu 'amalaa; wa huwal 'azeezul ghafoor
Allazee khalaqa sab'a samaawaatin tibaaqam maa taraa fee khalqir rahmaani min tafaawut farji'il basara hal taraa min futoor
Summar ji'il basara karrataini yanqalib ilaikal basaru khaasi'anw wa huwa haseer
Wa laqad zaiyannas samaaa'ad dunyaa bimasaa beeha wa ja'alnaahaa rujoomal lish shayaateeni wa a'tadnaa lahum 'azaabas sa'eer
Wa lillazeena kafaroo bi rabbihim 'azaabu jahannama wa bi'sal maseer
Izaaa ulqoo feehaa sami'oo lahaa shaheeqanw wa hiya tafoor
Takaadu tamayyazu minal ghaizz kullamaaa ulqiya feehaa fawjun sa alahum khazanatuhaaa alam ya'tikum nazeer
Qaaloo balaa qad jaaa'anaa nazeerun fakazzabnaa wa qulnaa maa nazzalal laahu min shai in in antum illaa fee dalaalin kabeer
Wa qaaloo law kunnaa nasma'u awna'qilu maa kunnaa feee as haabis sa'eer".........
Ihu tashigayi cikin wata iriyar murya mara dadin sauraro tace;
     "Wayyoooooo, dan Allah kayi hakuri"....
Gyaran murya yayi yace;
     "Da wani shaidanin nake magana tukunna"....
Cikin wata kalan murya tace;
      "Ni ba shaidani bane, ni musulmi ne, ka fita sabgarmu"....
      "Bazan fita ba! Waye kai!"...
    "Yusuf ne".......
"Menene matsalarka da ita da kake takurawa rayuwarta haka?!".....
   "Matata ce!"....
Hannu ya daga ze wanka masa mari dan ya shiga saitinsa, sai kawai ya naushi bango tuno da cewa ita zataji a jikinta ba dan iskan ba....
    "Matarka a gidan ubanwa? Wani mahaukacin ne ya daura muku auren?"....
    "Babana ne ya daura mana, aurenmu yau shekara uku, yayanmu biyu"....,
    "Oh yanzu nagane, kaine wahalallen da nacewa ka fita sabgarta dazu ko, amma baka daddara ba kazo ka biyomu harda hada munafurci ko, toh zakaci ubanka yau"....
Cikin shesshekan kuka tace;
    "Ka bani matata kawai mutafi, ni babu ruwana dakai"....
     "Wallahi ka sake kiranta matarka saina kona duka danginku banza mugu kawai, in banda mugunta ta ina aljani zeyi tarayya da mutum?"...
  Deen ya fada a zuciye yana kara mata rikon tsauri tsabar yanda ranshi ya baci, kai dole ma taji a jikinta daga baya.....
      "Eh mu munayi, dan Allah kayi hakuri ka kyaleni"...,
    "Kai har kasan wani Allah dan uwarka, idan kanaso na kyaleka toh akwai sharuda"...
      "Zan bi, zan bi"...
Ta fada da sauri....
     "Kafinnan kai kake sata take rashin kunya da rashin ganin girman nagaba da ita?"....
     "Aa bani bane ba, wallahi bani bane"..
  "Karya kake, aiba gaskiya ne daku ba!"...
"Wallahi bani bane, bani bane ka yarda dani"...
     "Hmmm naji, sharadun farko ka saketa daga gantalallan aurenku da kake fada, sannan kuma ka fita daga jikinta ka rabu da ita na har abada".....
     "Gsky bazan iya ba saboda ina sonta sosai, auren zobe mukayi ba rabuwa ba saki, inaji da ita sosai dan tana da kyau, tafi duka matan garin mu kyau".....
      "Shikenan dan mutum yanada kyau sai ku takura masa saboda kagu mayu?"....
     "Aa kawai ina sonta ne sosai kuma ina kishinta"...
Kwafa Deen yayi yace
       "Zakaci ubanka"...
Sannan ya fara karanto suratul jinn kamar haka
     "Bismillaahir Rahmaanir Raheem 
Qul oohiya ilaiya annna hustama'a nafarum minal jinni faqaalooo innaa sami'naa quraanan ajaba
Yahdeee ilar rushdi fa aamannaa bihee wa lan nushrika bi rabbinaaa 'ahada
Wa annahoo Ta'aalaa jaddu Rabbinaa mat'takhaza saahibatanw wa laa walada
Wa annahoo kaana yaqoolu safeehunaa 'al allahi shatata
Wa annaa zanannaaa al lan taqoolal insu wal jinnu 'al allahi kaziba
Wa annahoo kaana rijaalun minal insi ya'oozoona bi rijaalin minal jinni fa zaadoohum rahaqa
Wa annahum zannoo kamaa zanantum al lany yab'asal laahu 'ahada
Wa annaa lamasnas samaaa'a fa wajadnaahaa muli'at harasan shadeedanw wa shuhuba
Wa annaa kunnaa naq'udu minhaa maqaa'ida lis'sam'i famany yastami'il 'aana yajid lahoo shihaabar rasada
Wa annaa laa nadreee asharrun ureeda biman fil ardi 'am 'araada bihim rabbuhum rashada"...
        "Wayyoooooooo zan fita, zan fita zan fita, dan Allah karka konani, nace maka zan saketa"...
Be kulashi ba ya cigaba da karatu har saida yakai karshen surar lokacin harta fara wani irin kuka me ban tausayi sai ihu take tana san kwace kanta ta kasa.......
Saida ya tabbatar tayi mugun laushi ko yace yayi mugun laushi sannan yace;
      "Me kace?"...
   "Nace zan fita dagaske"....
  "Yadai fi maka, kayi alkawarin inka fita bazaka dawo ba?".....
     "Eh bazan dawo ba"....
    "Idan ka dawo in maka me?"....
    "Duk abinda kaga dama"....
   "Yayi kyau,idan ka isa ka dawo nida kaine, yanzu ka fita ta inda kasan bazaka chutar da ita ba"...
     "Toh na fita"....
Tana fadin hakan tayi wani atishawa me karfi sai kuma ta sume a jikinsa, rungumeta yayi yana shafa bayanta cikin tsananin tausayinta, zai iya cewa betaba ganin wacce yaji yana mugun tausayinta kamar itaba, he's just imagining what she has been going through, how he wish zatayi hira dashi kamar yanda yaji tanayi dasu Umm dayaji dadi, he had always suspect there's something behind her ashe he was not mistaken, yanzu kuma he's feeling like bayan wannan aljani daya ke claiming ya aureta there's another thing, da zata fadamasa 'WACECE ITA' da komai yazo masa da sauki....

WACECE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)Where stories live. Discover now