48

13 1 0
                                    

"Ban amince ba! Afterall babu aure a tsakaninsu!!".....
Umm ta katse abby da deen dake shirin magana.....
"Bangane babu aure a tsakaninsu ba?"....
Abby ya tambaya mamaki dauke akan fuskarsa.....
Deen ne ya karba da fadin;
"Eh babu! Bayan sunyi aure a dubai, yanzu kuma ya saketa saki uku! I have the paper with me!"......
Ya fada yana zaro papern da yaba khaleel ya saketa a cikin jirgi....
Da sauri khaleel yace;
"Wallahi ba'a daura mana aure ba, abby ka manta we followed you here saboda a daura mana aure?".....
Abby zeyi magana kenan Deen ya riga sa;
"Karya kakeyi wallahi! Abby karka yarda dashi! Da bakinshi ya fadamin an daura auren sannan hand to hand ya bani takardar sakin!"..
Ya fada yana mikawa abby papern yana wani cin magani yana kuma bin khaleel da wani mugun kallo......
Karba abby yayi ya bude paper, karanta content din ciki yayi a fili kamar haka;
"Ni Ibrahim khaleel Ibrahim na saki matata Fatima zainab saki uku!!".......
Da mamaki abby ya kalli khaleel ya mika masa takardar yace;
"Is this not your handwriting?".....
Saboda ya taba bawa khaleel wani takarda ya cike masa a asibiti, kuma be manta handwriting dinsa ba, sak irin wannan....
A daburce khaleel yace;
"Yes amma wallahi bansan sanda na rubuta ba abby, banma aureta ba bare in saketa, ya zaayi in auri kamar wifey in saketa?".......
Fizge takardar Deen yayi a hannun khaleel cikin kunan rai yace;
"A gidan ubanwa ta zama wifey din? Matarka ce zakana ce mata wani wifey? Wallahi na sake jin ka kirata da wannan sunan saina aikaka inda aka kai ubanka! Nonsense!"..
Ruko hannun Deen abby yayi yace;
"Ya isa haka, khaleel fadamin gaskiya an daura muku auren?"......
Girgiza kai yayi kamar zeyi kuka yace;
"Wallahi ba'a daura ba abby, trust me da an daura bazance ka zama waliyin mu ba, ka tambayi wifey Allah baa daura ba"....
Deen ya bude baki zeyi magana mami ta daga masa hannu tace;
"Shikenan abar zancen haka, khaleel ka dawo gobe, Insha Allah kafin nan ta warware sai a tambayeta aji"......
Godiya sosai khaleel ya musu abun tausayi sannan ya nufi kofa yana taku a hankali saboda kafarsa dake masa ciwo.....
Juyawa mami tayi ta haura sama, ganin haka yasa daddy barin parlourn shima dan yasan she needs time kafin ta bashi dama suyi magana.......
Juyawa Deen yayi shima zebi bayan mami ganin Abby a durkushe a gaban Umm da baby tee dake bacci har lokacin, Umm tayi saurin yafitoshi da hannu, komawa yayi ya tsuguna a kusa da abby suka hadu duka su ukun suna kallon baby tee that is sleeping peacefully tana sauke numfashi a hankali.....
Hannun deen Umm ta ruko tana kallon baby tee tace;
"She became part of me tin ranar dana fara ganinta! Bansan ya'ta bace but what I was feeling for her was a motherly love har naji ina son adopting dinta ta zama ya'ta despite everything going on then, duk wannan abun ya faru ne a sanadinka saif! I just can't thank you enough! Badan kai ba da rana irin wannan bazata taba zuwa ba! I can't count how many times kake ce mana ka fita sabgarta but you still never give up on her! Ashe kamar kasan jininka ce? Ni ko me zan saka maka dashi ne a duniyarnan saif?"......
Murmushi Deen yayi me kayatarwa yana kallon baby tee yace;
"I have always feel like she's part of us that's why I couldn't give up on her, ashe she's my blood! Alhamdulillah words alone can't express my happiness! Ba sai kin sakamin da komai ba umm addu'arki kawai ta ishe ni kamar koda yaushe!"......
"A'a saif just mention anything, ba lallai materialistic abu ba kawai ka fadi koma menene kakeso ni kuma zan maka"........
"Haba kamar ba umm dina ba! Gaskiya you should stop saying this, ni babu abinda nakeso, I have always wanted to help her fisabilillahi!"........
Dafa kansa abby yayi yace;
"Masha Allah! Allah ya maka albarka son! May you continue to be the apple of our eyes, mungode mungode! Allah ya saka maka da gidan aljanna Saifuddeen"....
"Ameen dan alfarmar annabi, bari nima in kara Allah ya bashi mata tagari mar'atussaliha"......
Umm ta kara tana murmushi....
Kallonta abby yayi yace;
"Kamar ke ko ameen"....
Shiru tayi batace komai ba, ganin haka yasa deen saurin chanja topic din yace;
"Kallonka kawai nake Abby kai bazaka bani offer din ba, dan kar ince wani mad private jet nakeso ko?"....
Dariya Abby yayi yace;
"Kwantar da hankalinka a sirrince naso muyi amma tinda ka fadi abinda kakeso sai ka nemo port insa a sauke maka jirgi.....
Shafa gemunsa yayi yace;
"Ni wasa ma nake".....
"Ai baka isa ba because your wish has been granted!".....
"Talaka dani bani da gurin ajye jirgi, ni kunga tafiyata ma".....
"Hhhh in dan wannan ne karka damu zamu rushe daya daga cikin mansion din Umm dinka kasa a ciki"......
Dariya yayi kawai ya haura sama.....
Dawo da kallonsa kan Umm abby yayi bayan Deen ya bar parlourn, maida idonsa kan baby tee yayi sai kuma ya sake dawo dashi kan Umm, gyada kai yayi yace;
"She's so beautiful just like you boddina! Amma kamar hancinnan nawa ne ko?".....
Ya fada yana jan hancin baby tee....
Gyara zamansa yayi a kasa jin taki cewa komai yace;
"I don't know how to explain myself boddi amma wallahi ba laifina bane! Nasan dai kinyi forcing dina inje gidan huraira on that faithful day which is the very first day I started eating her food, at times idan kikayi forcing dina inje gidan huraira wallahi bana zuwa a hotel nake kwana, saida ta kai karata sannan nake zuwa kuma shima in naje bana kulata, but that day tin daga kamshin gidan naji komai ya chanzamin, and it got worse bayan naci abincinta, it was more like I lose my memory dan bansan na sakeki ba wallahi..... I know you must have gone through a lot knowing ba abinda kikamin na sakeki amma dan Allah kiyi hakuri and I'm really sorry for all that you must have gone through...Inaso mu dau hakan a matsayin kaddararmu but I don't know if you can find a spot in your heart to forgive me, dan Allah ki janye Allah ya isan da kika min!"......
"It's okay!"...
Umm ta fada a sanyaye dan tasan dagaske ba laifinsa bane aikin asiri ne kawai, and waye asiri baze iya cinsa ba tinda yaci annabinmu ma?......
"Kice kin yafe min dan Allah boddi!".....
"Na yafe".....
Cikin farin ciki Abby yace;
"Thank you so much my one and only boddi!".....
Yi tayi kamar bataji ba ta cigaba da caressing gashin baby tee da mayafin abayar ya zame....
"How about we fixing our marriage dan Allah?".....
Abby ya tambaya a hankali kamar da wani a parlourn.....
"I am not interested!"....
Ta bashi amsa har cikin zuciyarta dan dagaske tanajin kamar bazata iya sake aure ba saboda yanda ta zama so dedicated and occupied yanzu, sometimes ko time din kanta batada shi musamman in akwai interns da take training, yanzu ma annual break tayi taking, she owns her hospital but she's an attending physician you can expect her not to be always busy......
"Why pls?"....
Abby ya tambaya yanajin wani iri a ransa....
"You don't have the right to question my opinion! Ko bappa nasan baze yimin maganar aure yanzu ba bare kai so karka kara!".....
"Angama ranki shi dade"....
Shiru ne ya biyo baya sai suka koma zaman kurame, shi be tashi daga inda yake ba ita kuma bata motsa ba.....
Suna a haka har baby tee ta fara motsi alamun ta tashi, abinda basu sani ba kuma tinda suka fara maganganunsu ta farka ta dai lafe ne tana jin komai, bude ido tayi tana bin parlourn da kallo, umm ce ta dagota da sauri ta zaunar da ita a kusada ita, murmushi dauke akan fuskarta tace;
"Hey beautiful! Kin tashi? How're you feeling now?"....
Murmushin ta maida mata tace;
"Na tashi, I'm okay umm".....
"Ni ba za'a kulani ba daughter?"....
Abby ya fada yana kallonsu lovingly.....
Da sauri baby tee ta juyo jin muryar da bata kaunar ji years back....
Tinda ta tashi take jinta kamar wacce aka dawowa da lost brain, duk wata azaba da ammy ta gana mata harda abby da yayi acikin rashin sani taji komai ya dawo mata sabo fil, a hargitse ta rungume umm tana fadin;
"Kice mishi ya tafi! Bana san ganinsa! Duka na yakeyi shida ammy! Kice ya tafi banasoooo".....
Cikin karyewar murya kamar zeyi kuka yace;
"Ki yafemin daughter I know I was never a good father, but wallahi it wasn't my fault, dan Allah ki yafemin".....
"You're not my father! Kace in nemi wani uba bakai ba, ka kuma koreni daga gidanka, nima banasan ganinka yanzu, umm karki sake tafiya ki barni kinga a dakin me gadi nake kwana"....
Zaro ido Umm tayi ta kalli Abby tace;
"Whaaat? A dakin me gadi kuma? It's that true? Muhammad kana me ya'ta take kwana a dakin me gadi?!".....
Hawaye masu zafi ne suka shiga zubowa abby, wato shi abu irin wannan ko ba'a cikin hayyacinka kayi ba you still have to pay for it?, a raunane yace;
"Bansani ba boddi and the day I found out har sakin huraira saida nayi".....
Ihun da baby tee tayi ne ya katsesa....
"Ka tafiiiiiiii, I don't like youuu"....
"Just excuse us!"....
Umm ta fada tana nuna masa kofa, ze sake magana kenan ta kuma tace;
"Ka fita kawai mallam!".....
Fita yayi hawaye na zuba a idonsa yana jin kamar ya dawo da hannun agogo baya ya goge huraira daga tarihin rayuwarsu, tabbas ta cucesu irin cutar da har su mutu bazasu taba mantawa ba, sannan kome zasu mata bazasu huce ba.......
Yana fita Umm ta kara rungume baby tee hawaye na sauka akan kuncinta itama, tabbas tayi farinciki mara misaltuwa da Allah ya sadata da yarta amma kuma dole taji ba dadi duba da irin wahalar da baby tee tashiga suna duniya kuma, da gatanta da komai amma tashiga gararin rayuwa haka saboda mugunta irin na dan adam, babu abinda yake daga mata hankali irin abinda ammy tace wai tayi degree a karuwanci, tsoro take kar Allah yasa hakan ya faru dan she'll be completely shattered, budurcin dasu daddy keta hauka akai waya sani ko ya riga ya watse a titi?, bazata taba dena cewa an cuceta ba har abada, right now tana bukatar charje baby tee tsap inba hakaba hankalinta baze kwanta ba, from all indications tasan ba'a daura aurenta da khaleel ba probably Deen ne yayi provoking dinsa har yayi sakin auren da babu shi, amma zata tambayeta taji gaskiyar lamarin, indai ba'a daura auren ba toh babu abinda ze hanata yi mata allurar bacci ta duba ta tsap ko zata samu nitsuwar zuciya......
Dagota tayi ta kamo hannunta suka haura sama.......

WACECE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)जहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें