22

20 1 0
                                    

Juyowar da Deen zeyi sukayi ido hudu da mami da Umm da sukayi mutuwar tsaye a gurin suna bin parlourn da kallo da sakekken baki.....
Ba karamin tashin hankali Deen ya shiga ba da ganinsu saidai bazaka gane hakan a fuskarsa ba, sai a lokacin ya fara dana sanin kawota gidan bayan ya san mami tasan gidan, shi a plan dinsa ze mayar da ita a yau ya samu ya koma kafin su mami su gane ya fita ashe mahaukaciya ya dauko be sani ba, gashi yanzu har sun gane bayanan sun biyoshi, abun kunyar kuma sunganshi rungume da ita, shikuma ya kasa sakinta kamar wanda aka yiwa baki....
Har bayan minti biyar anrasa me magana tsakanin Umm da Mami, kowannensu was just speechless with lots of questions, kada ma Umm taji labari that was more than disappointed, koda yaushe ita take kare Deen idan mami na complain akansa, koda tana masa fada bata wani ganin stubbornness dinsa da mami ke fada sai gashi yau idanta ya mata kyakkyawan gani da batasan a mazaunin da zatasa saba, wai Deen ne rungume da wata haka? Yana ganinsu kuma ya kasa sakinta?........
Itako mami rasa abinda zata kama tayi, gadai gida kamar anyi barin mahaukaciya ko film din dakin amarya albarka, toh wayayi wannan danyen aikin? Sannan kuma wacece haka da yake rungume da ita kamar zaa kwace masa ita?.......
Haka kawai zuciyarta ta bata suzo gidan dukda tasan bayanan dan baze zauna inda yasan zaayi saurin ganesa ba, but to her greatest surprise sai gashi sun samesa a gidan, a'a bama shikadai suka samu a gidan ba sun samu abubuwa dayawa, sannan ko ina is messed up bata inda zasu bi su karasa ciki ma, toh ya bazasu shiga shock ba?.......
Guilty conscious ne ya kamasa sosai ganin sunki cewa wani abu, sai binsu da kallo kawai sukeyi, shikuma tsoron sakinta yake karta karayin wani hauka a gabansu, nan ko tini allurar daya mata ya sumar da ita besani ba sai kara kankameta yake.....
Ganin shirun ba shine mafita ba yasashi tattaro sauran kwarin gwiwar daya ragemasa yace;
"I'm sorry Mami, I'm sorry Umm, It's not what you're thinking wallahi, don't judge me pls, I can explain!".......
"Are you for real? Har kanada gout din da zakace we shouldn't judge you? after everything we're seeing? Meka mayar damune? Shashashun da basu san me sukeyi ba? I am seriously disappointed in you! Wallahi Saif ka bani mamaki".......
Cewar Umm da maganar Deen ba karamin kara bata mata rai yayi ba, saboda rainin hankali wai they shouldn't judge him bayan duk abinda suka gani".....
"Umm please, Taimakonta kawai nayi, infact budurwar sameer ce ma, ni ban santa ba"....
Deen ya fada a rikice batareda yasan ya fadi haka ba........
Wata muguwar harara ta zabga masa tace;
"Taimakonta? I see! Budurwar sameer ce haka kamar wacce aka shafa muku fatiha, wa zaka renawa hankali, wawa kawai mara tinani!"....
Sosai hankalin Deen ya tashi ganin yanda Umm ta zuciya, yasan da yana kusa da ita ma da Allah kadai yasan mari nawa yasha yanzu, sannan kaji Umm tayi zagi to akwai matsala dan ta tsani zagi komin kankantarsa....
Cikin kokarin kare kai still yana rungume da ita yace;
"Trust me it's not intentional Umm, idan na saketa komai ze iya faruwa, she has mental illness kamar harda aljanu a lamarinta, dan Allah ku yarda dani".....
"Deen meka yiwa yar mutane, what are you hiding?!!!"...
Sai a lokacin mami ta fada strictly ganin rainin hankalin daya keso ya kara musu, suna kallon yarinya kamar bata numfashi amma zece inya saketa komai ze iya faruwa, it means he's hiding something kenan....
Cikin rashin sanin abunyi yace;
"Mom believe me I'm not hiding anything and.... Be karasaba idonsa ya sauka akan hannunta da jini keta zuba, a rude yace;
"Innalillahi her hand is bleeding, kinga abinda kika jawo ko? gashi kinjiwa hannunki ciwo yanzu ya zanyi? Will you even allow me to treat you?".....
Sai kuma ya dorata a kan three sitter ya tafi bedroom dinsa da sauri dan dauko first aid box, Mami da Umm na tsaye suna kallon ikon Allah.....
Fitowa yayi da sauri ya nufi inda take hankali tashe har lokacin begane a sume take ba, hannunta ya kama yana kokarin tsaida jinin yace;
"Just stay still bazan miki da zafi ba, kar kimin kuka irin na dazu".....
Shifa harga Allah ya manta da wasu mami dake tsaye a gurin, burinsa kawai kar wani abu ya sameta dan ya tsorata da ganin yanda hannunta ke fitar da jini.....
"Na tambayeka mekayiwa yarinyar mutane kaki cewa komai sai fadin we should believe you , what nonsense?"......
Muryar mami ta dawo dashi senses dinsa bayan ya samu ya tsaida jinin dake zuba daga tafin hannunta .....
Cikin murya me rauni kamar ba Deen the stubborn brat ba yace;
"Wallahi ba abinda na mata"....
"And meya sumar da ita, second why is she bleeding?, I just hope it's not what I'm thinking that happened"....
Umm ta fada cike da takaici....
"No no no, plsssss, it's just her hand that is bleeding, and she's not unconscious".....
Hade rai tayi sosai tana fadin;
"Hala idonka na maka ciwo ne, ko duk salon fooling dinmu ne? Baka ganin jini na zuba down her legs? And wani kalan nonsense Doctor ne kai da baka gane mutum ya suma? Well kana sane ai"....
"Rabu da dan rainin hankali yagani ai, wai mu ze renewa hankali, wallahi rufe ido zanyi na makaka a kotu, she deserves Justice!!!"
Sai a lokacin Deen ya kalleta sosai yaga da gasken bata numfashi ga jini nan facha facha down her legs, toh garin yaya? Ya akayi be kulaba? Gashi yanzu suna masa wata fassarar da ban thinking he raped her?!!.... "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"
Ya fada yana shaking head, yanzu ta ina ze fara bata treatment? What causes the bleed down? Shidai ya shiga uku bejiba be ganiba daga taimako.........
Ganin she's bleeding more gashi baze iya treating dinta a gabansu ba yasa ya kalli Umm pleadingly yace;
"Doctor please, dan Allah kiyi treating dinta, karta mutu, kinga she's bleeding profusely, I have all materials here".....
Dauke kai tayi dukda ba karamin tausayi yarinyar ta bata ba dan Umm akwai tausayi sosai, tace;
"Even if I want to treat her flying zanyi in sameku a gurin? Ko cikin messed area dinnan zan bi inzo, besides bazan tabata ba saika gayamin gaskiyar abunda ya faru!".....
"Ok ok bedroom din dake kusa daku is clean bari in kawota nan, Just treat her for me Doctor, I promise you zan fadi duk abinda ya faru please"......
Ya fada yana kokarin daukar fatima zainab....
Batace komai ba dan gaskiya yarinyar ta bata tausayi itama, and rayuwarta ya kamata a fara cetowa before anythin, ganin batace komai ba ya samu kwarin gwiwar nufarsu, yanajin kwalba na chakar kafarsa yana masa zafi, ga yanda jinin da take zubarwa yake bata gurin amma yaki tsayawa har saida ya sadata da gadon dakin.... Yana ajyeta ya fita da sauri dan ya dauko duk wani needful abubuwa dukda yasan beyi mata komai ba haka dai ya kwaso harda surgical suture if it happens da dinki dukda besan garin yaya ba......
Yana tsaye akanta harsuka shiga dakin, tausayi yarinyar ta basu sosai har Umm ta kasa bashi dirty slap din datayi niyar basa ta fara kokarin treating yarinyar ... Bin yarinyar da kallo mami tayi tace;
"Wannan ba ita bace kukayi accident tare ba?"...
Ajiyar zuciya me karfi ya sauke sannan ya gyada mata kai yace;
"Itace mami, she was kidnapped! I only intended helping, shine na kawota nan na boyeta dan nemanta sukeyi haryanzu......."
Be karasa ba sukajiyo muryar Umm na fadin;
"Ya akayi ka bari ta taka kwalba haka sosai?".....
Bashi ba hatta mami da ita Umm din dake treatment din saida suka sauke ajiyar zuciya gane cewa it's not what they're thinking.... Shiko Deen ji yayi kamar anzuba masa ruwan sanyi da jin hakan dan harga Allah ya tsorata dukda yasan ba abinda ya faru, wani kalan rudewa yayi ne da har ya kasa gane abinda ya sameta kamar ba Doctor ba?.....

WACECE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)Where stories live. Discover now