41

18 2 0
                                    

Aka dauko goro da sauran abubuwan aka matso dasu kusa lokacin masallacin ya cika makil da jama'a, gadan gadan aka shiga hidimomin daurin aure kowa fuskarsa dauke da farin ciki zaa hada sunna, gyaran murya sheikh Abdallah yayi sannan ya fara da bismillah.......
"A'uzubillahis-sami'ul aleem, minash-shaydanir rajeem, bismillahir rahmani raheem, allahumma..."
Kamar wanda aka mintsina sheikh jabbar ya taso ya dawo kusa da sheikh Abdallah, kasa yayi da murya yace;
"Ya sheikh ya ake shirin daura aure ba maganar waliyyai"......
Dakatarwa yayi ya dago ya kalli sheikh jabbar, cikin dan rudani yace;
"Subhanallah! Wallahi na sha'afa saboda labarin da suka bani sheikh, wayennan yara ne masu tinani kwarai".......
"Wani labari sheikh?".....
"Aure zasuyi saboda suna tsoron afkawa zina, kaga kuma a zamaninnan sai yara masu tsoron Allah ne zasuyi wannan tinanin shiyasa suka burgeni suka shiga zuciyata".......
Tsit masallacin yayi saboda kowa so yake yaji dalilin dayasa aka dakatar da daurin auren......
Kallon khaleel sheikh Abdallah yayi yace;
"Bawan Allah ina waliyyanku?"......
Kasa da kai khaleel yayi yace;
"Babu su a kusa dake baa kasarnan muke ba amma sun san da maganar auren".....
Murmushi yayi yace;
"Yanada kyau a samu waliyyi koda kuda dayane"...
Karab fatima zainab tace;
"Dole saida waliyyi zaa daura aure?"......
Kallonta yan gurin suka hauyi suna murmushi, su dayake larabawa masu nuna affection dinsu a fili sai sukayi tinanin san da take masa ne yasata kasa shiru......
"Ba dole sai da waliyyi ake aure ba amma saboda yanayin rayuwa yanda komai ya zama sai a hankali yanada kyau a samu waliyy koda a cikin mahaifa ko yan uwa ko makusanta, da zasu zama shedu gudin bijirowar wani abu daga baya dukda ba fata ake ba".......
"Mudai sheikh ka taimaka kawai a daura mana auren wallahi bamu da kowa a kusa".....
Cewar khaleel kamar zeyi kuka.......
Murmushi sheikh jabbar yayi ya dafa kafadar khaleel yace;
"Gwara ku samo koda mutum daya ne habibee"...
Dan shiru khaleel yayi yana tinanin yanda zasuyi, kawai sai sameer ya fadomasa a rai, ya tina yanda sukayi da sameer akan zeyi supporting dinsa akan komai, yanzu this is the best time for that, murmushi yayi yace;
"Toh sheikh, Insha Allah akwai wanda zezo daga Nigeria"........
"Masha Allah masha Allah".....
Sheikh Abdallah ya fada yana kara yabawa da hankalin yaran.... Nan aka shiga sa musu albarka aka musu addu'a sosai.......
Mikewa khaleel yayi yace ta tashi su tafi.......
Har sun kai bakin kofa sheikh Abdallah ya kirasu, dawowa sukayi suka sameshi, nuna inda aka ajye sadaki yayi yace khaleel ya tafi dashi tukun, girgiza kai khaleel yayi yace a barshi a gurinsa saboda gobe zasu dawo zuwa gobe, ajyewa akayi kamar yanda ya bukata sannan suka sake sallama dasu suka fita.........
Kamar jira fatima zainab take su fita daga masallacin tace;
"Yanzu shikenan ba zaa daura aurennan yau ba?"
Kashe mata ido daya khaleel yayi cikin tsokana yace;
"Haka kika matsu a daura auren?".....
Itama kashe masa ido tayi tana dariya tace;
"Sosai ma".....
"Karki damu akwai wanda zan kira ya mana wakilci, zuwa gobe ze karaso Insha Allah"...
"Ohk Allah ya kaimu "......
Hannunta ya ruko suka fara tafiya yana fadin;
"Kinga sai a daura aure musha amarcinmu sosai, kai can't wait wallahi".....
Ya fada yana dan matsa mata yatsunta cikin tausasawa.....
Kwace hannunta tayi ta rankwasheshi akai, fuska dauke da fara'a tace;
"Koba amarci ba".....
Dafe inda ta rankwasheshi yayi, yana kallonta kamar ze hadiyeta yace;
"It's painful but I love it"...
Dariya tayi tace;
"Idan na fasa kan you'll know that you love it"...
"Serious I love it, honestly I love the new you wifey, I just love everything about the new you".....
Wani killer smile ta mishi da yaji kamar yayi melting a gurin yace;
"If loving you was a job, I'd be the most deserving, dedicated, and qualified candidate. In fact, I'd even be willing to work for free! I love you countlessly!"....
Murmushin dayafi wanchan tayi tace;
"If someone asked me to describe you in just two words, I'd say "Simply Amazing.".....
Murza hannunta yayi yasa idonsa cikin nata yace;
"You are a better part of me and my second half. Without you, I would probably be lost. You complete me, and right now, I could not wish for a better life partner.".......
"Hey you're driving me crazy!"......
Ta fada tana fashewa da dariya"......
Dariyar yayi shima yace;
"I don't mind you being crazy but crazily in love with me hhh".......
Jan hancinsa tayi tace;
"My feet will walk with you anywhere you want.I promise!"........
Hannunta yayi pecking yace;
"Ba zan taba barin ki ba, saboda ke ce -rayuwata. Soyayyarmu tamkar babban lambu' ne ma'fi girma a duniya.' Ina sonki sosai masoyiyyata."
"Ina sonka nima darling khal"......
Saida sukasha soyayyarsu sosai sannan suka koma gida, zubewa sukayi a parlor suka cigaba da soyewarsu kamar ba gobe......
"Wifey kinga shaukin son ki ya mantar dani in kira sameer, let me call him now".....
Khaleel ya fada yana dubanta cikin so da kauna...
"Waye sameer?"....
"Wanda ze wakilce mu"....
"Okay, call him"

WACECE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)Where stories live. Discover now