31

31 1 0
                                    

Alhamdulillah Alhamdulillah Allah yasawa wannan aure albarka!.......
Daddy ya juyo muryar mallamin na fadin haka... Sai kuma ya farka firgit daga dan baccin daya kwashesa, ashe mafarki yake har lokacin baa gama daura auren ba, ajiyar zuciya yayi yana jin kamar ya janyo lokaci, burinsa kawai a daura auren a wuce gurin, chan sai yaji gabansa na faduwa kamar wanda yayi tsere, babu wanda ya kula da yanayin da yake ciki aka cigaba da hidindimun daurin aure......
Alhaji habibu na shirin bada shedar an basu ita a matsayinsa na waliyyinta sukaji karar kofa.....
Sai kuma baa shigo ba, tinani sukayi ko iska ne hakan yasa suka cigaba da harkokin gabansu....
Alhaji habibu na shirin kara yin magana kenan sukaga an banko kofar parlourn da karfi......
Kallon juna suka shigayi kowannensu na tinanin waye dan meshi be shigoba har lokacin.......
"Dama baka rufe kofar ba dazun?"........
"Wallahi na manta, ashe ban rufe ba, bari na duba naga waye sai mu cigaba".......
Daddy ze mike kenan idonsa ya sauka cikin na khaleel da kallo daya zaka masa kasan har lokacin be dawo daidai ba.......
Tsabar rudewa besan sanda yace;
"Auren ka ake daurawa son".......
"Bangane aurena ba? Dad what's going on here?"
Cewar khaleel idonsa na sauka akan fatima zainab....
"Wifey what's happening here?".....
"Bansani ba"...
Ta bashi amsa tana mikewa.....
"Can anyone tell me what's really going on here?!"
"It's nothing serious son".....
"Daddy stop telling me it's not serious, how comes wifey ita kadai a cikinku?"......
"Nace maka auren ku ake daurawa".......
"Wifey is that so?"......
"No! Ba auren mu ake daurawa ba and I don't know what's going on here too, I just found myself here!".....
"Dad just know that I'm not ready to listen to you in kasan bazaka fadamin gskyr abinda kuke shiryawa ba! Wifey taso mu tafi"......
Ba musu ta mike tabi bayansa suka fita daga parlourn..........
"Yanzu kana ganin danka ya fita da ita amma bazaka tsawatarmasa ba? Yanzu wannan shirin shima ya kara rugujewa kenan?! Alhaji Ibrahim you're playing with your life! Ku tashi mu tafi!"........
Cewar alhaji habibu rai bace.....
"Dan Allah ku zauna mu nemo solution, ku bani last chance nayi alkawari ba zaa kara samun matsala ba..........
"Bamu da wannan lokacin yanzu, mu hadu a house anjima kawai!"......

Tinda suka fito daga part din daddy aka rasa me magana a cikinsu, kowanne yayi shiru yana fama da abinda yake tinani....Shi khaleel na tinanin abinda su daddy sukeyi dan haka kawai zuciyarsa taki aminta da abun alkhairi suke kullawa, harda masa karya wai aurensa ake daurawa ya tambayi fatima zainab kuma tace ba haka bane, she even seem so lost kamar batasan abinda ake ba tanadai zaune ne a gurin.......
Ita kuma tinanin irin ramar da taga khaleel yayi take, tabbas taso taje ta dubasa dukda batayi tinanin ciwon nasa yakai har yayi rama haka ba.......
"Ya jiki?"....
Tasamu kanta da fadin haka......
Surprisingly yace;
"Dama kinsan banida lafiya?"....
"Nasani! Koda bansani ba your look said it all"....
"Shine ko kizo ki dubani wifey? I was sick because of you, kinsani kikayi kamar baki sani ba".....
"I don't know if you would believe this but I intended coming to check on you, bansan abinda yasha min kai ba".....
"Wow for real? Am I dreaming? Anya fatima zainab din danasani ce kuwa?".....
Murmushi me kyau ta masa tace;
"Itace mana, I hope you're better now?"....
"Even if I'm not better ganinki da maganganunki sun sani na warke rass and I still can't believe it's you".....
"Come on it's me mana!".....
Kawai saita ganshi ya duka kasa yayi sujuda yana godewa Allah.....
Dariya tashigayi sosai.....
"Sujudush-shukur nakeyi, you won't understand how I'm happy having a nice conversation with you".
"Ya isa haka toh tashi"....
Ta fada still dariya dauke akan fuskarta......
Dagowa yayi yana kallon yanda dimples dinta yake lotsawa a yayinda take dariyar, be taba sanin tanada dimples ba sai yau, toh ta ina ze sani shida be taba ganinta tana dariya ba?.... It felt like a dream come true, yanzu addu'ar shi daya Allah ya dasa mata koda rabin son da yake mata ne, har imagining suna soyayya me zafi ya farayi........
""Your beautiful laugh makes my heart melt; I can't imagine a life without you. I love you dearly."
Dauke kai tayi tana juya masa baya....
Dariya yayi sosai yace;
"Wai kunya kike ji? Wayaga wifey da jin kunya"..
"Kunya? Naaah, you're kidding man!"....
"This is the fatima zainab I know!"....
"Hmmm"....
"Whenever I see you, I feel like I'm looking at the most beautiful angel on earth. You are loved. You are wonderfully made wifey!"......
"You're so sweet khal!"....
Tafada murmushi dauke akan kyakkyawar fuskarta, sannan tashige part din momma da sauri....
Wani melting yaji zuciyarsa nayi, sai kuma ya shiga bubbuga kansa da hannunsa yana fadin;
"Wake up khaleel! Wake up! You're dreaming!"......
Sai kuma ya Girgiza kai yace;
"It's real! Kamar fa I'm not dreaming".....
Chan kuma saiya bita ciki......
"Shine muna hirarmu me dadi kika gudu ko?"....
"You talk too much, my head is aching already"....
"Oh sorry love! Kin ki yarda muje a duba kannan naki?".....
"It's not serious! Can you excuse me?"......
"Of course yes! Take care love"......
Harya fara tafiya ta dawo dashi da fadin;
"Ina momma?".....
"She has travelled, kamar sun dan samu issue da daddy".....
"Ban tambayeka wannan ba"....
"Allah ya baki hakuri sarauniyata, yauwa I heard you guys are starting exam tomorrow, hope you're prepared?"........
"No!"...
"Why?"....
"Hakanan!".....
"No pls, let's go get the materials, I'll assist you muyi karatun tare"....
"Babu inda zani!"....
Ta fada tana bata rai.....
"Toh let me get the material sai muyikaratun?".....
"Bafa zan karanta komai ba, dan Allah ka fita ka bani guri, why do you talk too much?".....
"Sorry, sorry, yanzu zan fita"....
Ya fada yana stammering ganin yanda ta fara zuciya daga magana kadan, kamar ba itace harda ce mishi he's so sweet dazu ba, well koma menene shiya janyo daya sata surutu kuma yasan bataso saboda yaga ta kulashi yau......
Fita yayi da niyar yaje ya siyo mata handouts din koda bazatayi karatun ba kamar yanda ta fada, sannan ya kamata ya binciko mata time table dan yasan kila batasani ba.......

WACECE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)Where stories live. Discover now