18

22 1 0
                                    

"You must be joking sis! Toh wai meya miki hakane?".....
Cewar jamila da mamaki ya isheta.......
"Can you believe ni Saifuddeen yayi saving numberta da 'this woman'?"....
Mami ta fada cike da takaici.....
Wata muguwar dariya Jamila ta fashe da ita tana fadin;
"Yanzu dama abinda yasa kikayi fushi dashi kenan? Haba you shouldn't take it that serious ai".
"Ai dama you never take anything serious, bakya san lefinsa na riga nasan wannan karatun"......
Dariya ta karayi tace;
"Niba haka nake nufi ba, yanzu dai we're so sorry, in kika cire hannu a lamarinmu bamu san ya zamuyi ba".......
Mami batace komai ba, amma har zuciyarta maganganun Jamila sun sanyaya zuciyarta...
Jamila is the real definition of a calm person, gata very jovial da wuya kaga tayi fushi amma fa intayi fushi ba wanda yake iya controlling dinta......
Parking mami tayi a harabar mansion dinta da kallo daya zaka masa kasan ba karamin dukiya aka narka gurin ginashi ba....
Fitowa sukayi a tare, mami tayi leading dinsu ciki....
Bayan sun gama kintsawa sun gama komai suka sake fitowa....
Direct hospital suka tafi domin su dubo yarinyar ganin yanda Jamila ta kagu taga abinda mami take fada akan yarinyar.....
Office din Doctor suka nufa straight dan already mami tayi waya dashi akan suna hanya, shi ya dauka patient ma zasu kawo.....

Knocking sukayi ya basu izinin shiga.......
Zama sukayi suka dan gaggaisa sannan mami tace;
"Doctor ya patient din tamu? Kajimu shiru ko, wallahi muna dan settling abubuwa ne"....
Murmushi yayi yace......
"Yeah nasan dole zaku shiga busy dama, I hope dai sun sakeshi?"....
"Zadai su sakeshi Insha Allah".....
"Ok, Allah ya yadda, about the other patient, wani yazo ya dauketa yace shi dan uwanta ne, na dauka ku kuka turoshi"......
"Ayyah Allah sarki, toh ba damuwa".....
Mami ta fada tana mikewa ganin tinda ba sanin yarinyar sukayi ba tayiwu yan uwanta sunji labarin accident din sunzo sukazo suka dauketa, so ba amfanin jan maganar kuma, saidai har zuciyarta bataji dadin yanda basu sami yarinyar ba, taso ace yar'uwarta jamila ta ganta wallahi.......
Godiya sukayiwa Doctor din sannan suka fita.....
Suna shiga mota jamila tace;
"Gaskiya banji dadi ba da akace an dauke yarinyar, kinsan gidansu toh muje dan gaskiya I'm eager to see the girl gashi haryanzu baki fadamin abinda kika gani atattare da ita ba".......
Ajiyar zuciya mami ta sauke tace;
"Wlh bansan gidansu ba, gashi Deen yace shima besan 'WACECE ITA BA' even though he has met her before, sannan na manta abinda nagani a tattare da ita wallahi! Kamar wacce aka rikewa baki naji na kasa gayamiki ranar kuma shiyasa nace kizo ki gani da kanki".........
Zaro ido tayi tace;
"Ikon Allah! Toh dan Allah muje gurin Saif din sai ya fada mana inda ya taba haduwa da ita, I'm so curious right wallahi, hankalina baze kwanta ba inba ganin yarinyar nan nayiba nima".......
"I want to teach him a lesson! Bayanzu zamuje ba, sai ya gane kuransa!"....
"No sis, this is a serious case ko yaya muka matsa akai zaa iya cin galaba akanmu, kiyi hakuri agama case dinnan then punish him later, hannunka baya rubewa ka yar fah".....
Girgiza kai mami tayi tanajin ko two days ne ya kamata tabashi ta yanda sai yayi losing hope kafin suje even though tasan ba lallai ya damu ba.....
"Kinji sis, ko bazaki ba ki kaini pls, do it for the sake of baby tee inni bazakiyi dan ni ba"......
Shiru mami tayi jin an tabo dayan weak point dinta ko tace weak point dinsu duka, haka sukewa juna in suka kula dayansu bayasan abu, sai suyi using baby tee as a weapon......
Tada motar tayi batareda tace komai ba.....
Bata tsaya ko ina ba sai cell din da Deen yake ciki......

Zaune yake abun duniya ya ishesa, so yake ko yayane ace masa she's fine, tinda yazo ba abinda yakeyi sai tinaninta, kota farka yanzu? Is she alright? Isn't she injured? Ana kula da ita?..... Wa'yannan tambayoyin su suka taru suka cika brain dinsa, hakan saiyasa masa ciwon kai, yana cikin wannan hali kuma saiga mami, yaji dadi sosai saboda yasan koyaya ze samu information a gurinta dan yasan mami da tausayi dole zataje ta kara duba yarinyar, amma sai stupid mistake dinsa ya janyo mami ta wuce ta barsa, abun dariya tana tafiya ya chanja sunan daga 'this woman' to 'birth giver' (ni ko nace daga baya kenan😹).....
Tinani yake kawai ta hanyar da ze gudu daga cell din ya samu yaje ya ganta, daya ganta ze kawo kansa da kansa, shidai kome ze faru ya faru bayan yasan ' WACECE ITA',.....
Yana cikin wannan halin ya hangota, abu kamar a mafarki cuz she's the last person he's expecting, mikewa yayi da sauri ya karaso inda take yanajin abinda ke damunsa na raguwa kadan kadan.... Hugging dinta yayi sosai kamar jaririn dake neman taimako a gurin uwarsa....
"I miss you so much Umm na"......
Shida kansa ya rasa wani kalan so yake mata, yanda yakejin maganarta ko iyayensa bayajin maganarsu haka, hakan kuma baya rasa nasaba da irin son da itama take nuna masa.......
Turesa jamila tayi tana fadin.......
"Ni matsa chan mara kunya kawai".....
Dariya yayi sosai yana kama kunnensa yace....
"I'm sorry Umm, tell her that I'm sorry pls"..
Kunnensa ta kama ta murde sosai tace;
"Ni ina ruwana, you thought you're doing the right thing ko? Ka fiso kata dagawa mutane hankali ko? To wlh baka isa ba, kasan da yaya ta yarda ta kawo ni kuwa?".....::
"Ouch da zafi fa Umm na, it was a mistake, I promise you bazan karaba, nafa maida mata sunan to 'birth giver' yanzu"......
Ya fada yana janye kunnenshi........
Dariya tayi sosai sannan tace;
"Ai gwara ya maka zafi sosai, kace ka maida mata me? Ba birth giver ba saura 'labor doer', ja iri kawai"......
Shima dariyar yayi ganin tana dariya, shiyasa yake sonta dan akwai ta da saukin kai, tana da wasa kuma sosai.......
Sunkuyar da kai yayi kamar wani na Allah yace;
"Nafa tuba sosai"....
Rankwashi ta kai masa tace;
"Karma ka tuba ka tsaya kana hadasu fada da ubanka sai kace wani karamin yaro, besides inace dai nima ba 'that yeye woman' kamin saving ba ko"..
Dariya ya fashe dashi harda rike ciki, da kyar ya daure ya tsagaita dariyar yana fadin;
"Nooo, my love nasa miki"......
"Karya kake wlh, better save that name for your future wife dan mudai ba sanmu kake ba, kila ita ka sota".......
"Haba Umm na ya zakice haka, niko nake sanku, musamman ke sonda nake miki is special, kuma ni ki dena min maganar wata future wife, nifa bazanyi aure ba".......
"Ah lallai, toh in ciwo ne Allah ya yaye maka, ka dai gamawa yan mata rashin mutunci ka kwaso yar mummuna abunka".......
Ta fada tana dariya......
Bata rai yayi yace;
"Niba ruwana da mata be it me kyau or mummuna".........
"Yayi kyau, you'll repeat that again"....
"Umm ina mami toh?"....
"Tana waje, I doubt in zata shigo, da kyar ta kawo ni, saida na hadata da little tee!".....
Murmusawa yayi yace.....
"Kunfiya ji da little tee dinnan, shiyasa nake kishi da ita".....
"Gwarama ka taimaki kanka ka dena, kato dakai kana kishi da yar yarinya"....
"Zan kamata ne ai very soon"....
Shiru Umm tayi jin wani memories na dawo mata..
Kallon Umm yayi ganin yanda yanayinta ya chanja a lokaci daya, yasan hakan kuma baya rasa nasaba da maganar baby tee da sukayi, a kullum yana mata addu'a akan Allah ya yaye mata damuwarta, sai kaga mutum koda yaushe cikin farin ciki amma deep down shiyasan me yake going through.....
"Umm na ni kadai"....
Ya fada to cheer her up.....
"Yes son"....
"Dan Allah ki taimaka min mami ta shigo, I want to apologize to her".....
Ya fada yana marairaice fuska dan taji tausayinsa, nan ko so yake ya tambayeta kota koma asibiti ta duba masa distraction dinsa......
Tausayi Umm taji ya bata ta kallesa tace......
"I'll try"...
"Kisake hadata da baby tee pls, nasan zata yarda"....
Harararshi tayi ta fita.....
Saida suka kai ruwa suka kai tsaki kafin mami ta yarda tashiga, nanma wai for the sake of baby tee ne......
Tinda tashiga bata kulasa ba, tana dai sauraron ranting din da yakeyi da sunan bada hakuri, hakurin da yake bayarwa har cikin zuciyarsa kuma, ance uwa da da' sai Allah, nan da nan taji zuciyarta tayi sanyi harya fara bata tausayi......
A yatsine kamar bata damu ba tace;
"It's ok"...
Murmushi me fadi yayi yace;
"Thank you mom, na chanja miki to sweet name, in baki ki gani?"....
Wani harara ta watsa masa, Umm na tsaye tana musu dariya.....
"Ba wannan ne ya kawoni ba, dan inta kaine bazan zo ba wlh"....
"Toh Nagode"....
Sai taji ya kara bata tausayi ganin yayi sanyi kamar ba stubborn Saifuddeen dinta ba, kasa hakura tayi tace.......
"Are they maltreating you here? Naga duk kayi wani iri!".......
"Not at all mami! Ko kallon banza basamin under their boss custody, boss dinsu yace akwai mutunci tsakaninku sosai, har waya suke kawomin for some minutes everyday, abinci ma sai an kawomin menu, na zaba, ancemin it's from you, thanks alot".....
Numfashi ta sauke tanajin hankalinta ya dan kwanta tace;
"Kaci gidanku, ni kake cewa thank you kamar wata stranger?".....
Cike da ladabi yace;
"Not at all ma'am"...
"Saifuddeen meya canzaka haka? Sam na kasa gane kanka, where the respect and everything comes from? Kodai you're hiding something ne!"........
Dagasken mamaki yake bata kwanannan shiyasa ta kasa hakuri harta tambayesa.....
"I'm not hiding anything wlh mami, I'm sorry for all that I've caused for you, na tuba sosai"........
"Idan duk jikina kunne ne bazan yarda da wannan tubar ba"....
Cewar Umm tana dariya......
Murmushi mami tayi tace;
"Ah toh nima ban yarda taubatun nasuha yayi ba, well got some questions I wanted asking you dazu"......
"Umm hardake, nafa tuba da gaske nace, mami proceed with your questions"......
"Hmmm, so nake ka bani labarin how you were kidnapped, da kuma yanda lady din ta taimakeka har kukayi accident tare"........

WACECE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)Where stories live. Discover now