33

25 1 0
                                    

Driving Deen yake a nitse har yana tsokanarta wai ta kalli yanda ake driving ba irin nata ba mesa ayi accident, bata kulashi ba hakan yasa yaja bakinsa yayi shiru...
"Kinsan abinda so called daddyn chan yakeso a gurinki?"...
Deen ya tambaya yana breaking silence din .....
"Bansani ba!" ......
"Baki sani ba? You're fooling me ko? Wato hardasu zancen aure a tsakaninku? Ko kunya bakyaji zaki auri uban so called boyfriend dinki?"......
Harararshi tayi tace;
"Haka na gayamaka zan aureshi? Why won't you learn minding your business?"......
"Anki ayi minding business din! Idan ba wani abu meyasa zakije part dinshi ku kebe daga ke sai shi?"....
"Wannan kuma kayi kadan kaji dalili"....
"Naga alama idonki na miki ciwo ko! Har bakiga abinda yayi niyar shaka miki ba, he'll just rape you and use you for nothing wawuya kawai!"........
Da sauri ta juyo ta kalleshi jin wani abu banbarakwai namiji da suna hajara, even in her wildest thought bata taba kawo daddy ze iya tabata ba koda auren sukayi bare wannan, sannan lokacin da suke magana kanta na kasa so batasan abinda ya faru ba, itadai kawai taji anyi sama da ita, suna zuwa tsakiyar farfajiyar gidan kuma ya sauketa ya shiga janta yana mata masifar da batasan na menene ba, ita kuma shiyasa tadinga tirjewa dan batasan me yake nufi da ita ba, fin karfinta kawai yayi amma da babu abinda zesa ta biyoshi.........
Ganin kamar jikinta yayi sanyi sai ya kara samun kwarin gwiwar tambayarta abinda yake ransa;
"Menene tsakaninki da Alhaji Ibrahim?!"
"Nothing!".....
Cikin rarrashi yace;
"Dole akwai abinda suke shiryawa akanki and remember I promise to protect you with all my life, ki fadamin gskyr abinda yake tsakaninku dan insan ta inda zan billowa lamarin?".......
"Ni nace inaso ya aure ni!"......
Wani uban birki ya taka tsabar yanda maganar ta dakesa, yana tinanin so ake a cutar da ita ashe ita takai kanta, nan da nan yaji mood dinsa ya chanja.....
Dukan steering yayi a fusace yace;
"Uban me ze miki idan kin aureshi?!"....
Sosai yanayinsa ya dan bata tsoro, ita ta rasa wani kalan mutum ne shi, yanzu saiya maka magana a hankali, anjima kadan kuma ya birgice har ka kasa gane masa, babban abin haushin sai ka kasa gane abinda ya bata masa mood...
Tsoro taji karya kuma shaketa tayi kokarin fita ta gudu, fizgota yayi ya dawo da ita inda take yana sawa motar lock.....
"Where do you think you're going to?"... If you provoke me wallahi baza kiji da dadi ba! Now answer me meyasa kikace zaki auresa?"......
Cikin son cusa masa haushi dan tasan abinda zata fada beyi making sense ba tace;
"Son shi nake!"....
Jinta kawai tayi ta tafi flat ta kwanta, ashe kwantar da kujerar da take kai yayi sannan ya zaro wata doguwar igiya itadai batasan mezeyi dashi ba, cikin sauri tace;
"Karya nake, wallahi ba sanshi nake ba"....
"It's too late baby girl"....
"Dukana zakayi? Nace fah karya nake wallahi"....
"Duka?Abinda yafi duka zanmiki, just wait and see, next time idan na tambayeki abu baza kimin gardama ba!"......
Sosai tasha jinin jikinta ganin ba alamar wasa a fuskarsa, yana ce mata mahaukaciya amma wallahi ko gabanwa zaaje ya fita hauka, in banda haka toh me yake nufi da dauko waya kamar wacce ze daure?........
Zatayi magana kenan sukaji harbi daga gefensu, dagowa sukayi a tare suna neman ta inda harbin ya fito....
Nan sukaga mutane zagaye dasu kowannensu dauke da manyan bindigogi.....
Murmushi Deen yayi ya ajye igiyar dake hannunsa yana dago mata seat dinta, ya kalleta yace;
"Kinga kinmin baki gashi anzo zaa kasheni, saiki bada gudunmawar da kikayi niya ai!".......
"Ni kuma?".....
Ta fada kamar bata gane abinda yake nufi ba....
"Harkin manta kenan?"....
"Ko kuda bazan iya kashewa ba bare mutum!"...
"Karya kike!".....
"To ai in kashewar ne mu biyu zasu kashe ba kai kadai ba"....
"Waya fadamiki zan bari a kasheki?"......
Shiru tayi aranta tana fadin kamar bashine me yawan cemin ze kasheni ba.....
Ganin tayi shiru ya sashi fadin;
"Kina jina? I have a gun here, zan fita inyi attacking wa'yenda suke side din da motarnan zata bi ta wuce, just make sure ina fita ki dawo front seat, ki taka motarnan kibar gurinnan a guje and karkije ko ina sai gidan mami, kinji ko?"......
"To kai fah?".....
Ta tambayesa tanajin wani iri aranta....
"Karki damu, zasu kasheni at the end cuz sunada yawa kuma so suke su kasheni dama, yauwa karki sake ki kara zuwa gidan daddy"... And...
Sai kuma ya dauko wata yar takarda yayi rubutu yayi signing......
"Ki kaiwa Umm, kice mata nace it should be done as soon as na mutu, a cire duka biyun sabodameshi is at danger"......
"Yauwa forgot to tell you something bakida HIV, forgive me for that, I just did that ko zaki fadamin wacece ke, unfortunately baki fadamin ba and it's totally fine, just make sure you leave here as soon as possible, karki damu ko sunyi harbi bazai fasa glass din ba, just be safe okay?"........
Sosai jikinta yayi sanyi da maganganunsa, sai itama ta samu kanta da san sanin wanene shi da yake willing to sacrifice his life for her haka?, saita rasa abinda zatace haryasa mata paper a hannunta...
Daukan bindigar yayi ya bude kofar.....
Da sauri ta janyoshi tana zama kan cinyarshi at the same time tana janyo kofar daya fara budewa, daidai nan aka saki harbi a daidai gurin, Allah ya takaita ta riga ta rufe kofar........
Fashewa tayi da kuka ta chakumeshi, cikin futar hayyaci tace;
"Meyasa zakayi haka? Niya kamata in mutu ba kai ba! Idan na mutu babu wanda yake da asara, but you deserve to live ba zaka mutu ba! Babu inda zaka fita!"......
"Shhhhh! Relax baby girl!, stop crying".....
Ya fada yana goge mata hawaye, yana kuma gyara mata zamanta akan cinyarsa......
Janye hannunsa daga fuskarta tayi har lokacin bata dena hawaye ba tace;
"Stop touching my face!"....
"Nadaina, stop crying toh and ki koma ki zauna"....
"Promise me bazaka fita ba?"...
Murmushin daya dade beyi irinsa ba yayi yana dan jan kumatunta yace;
"I can't! We need to act fast karsuyi attacking dinmu mu biyu, ki sauka daga kan cinyata".....
"Wallahi bazan sauka ka fita ba!"...
"Okay"....
Ya fada yana kokarin daukarta ya maidata seat din da take, da sauri ta rungumeshi tana kara sakin wani kukan, bata tabajinta clueless irin haka ba, she was just so confused, burinta kawai karya fita daga motar su kashe shi dan tasan koya fita kamar yanda yace bazata iya jan motar ba saidai itama suzo su kasheta....
A lokaci daya yaji kamar an zare masa laka tsabar yanda dumin jikinta ya ratsasa, ga tudun kirjinta daya sashi jinsa kamar a cloud nine, ga kamshin fitinannan turarenta da sai kazo dab da mutum zakaji yanda yake hawa kai, abubuwan da yakeji kawai bazasu fadu ba....
Sai ya manta da masifar da suke ciki ya koma ita kawai yake gani a duniyarsa, sai labari ya nemi ya chanja Allah yasa tinted glass ne......
Bata fargaba saida ya warware mata nadin lifayarta tass, Allah ya taimaketa doguwar rigace me dan kauri a jikinta, kokarin janyewa tayi shikuma a lokacin ya nuna besan zancen ba, saida tayi dagaske sannan ta samu ya sassauta mata....
kokarin sauka daga cinyarsa tayi, da sauri ya daura hannunsa a faffadan ugunta yana kara matseta a jikinsa....
Lumshe kyawawan idanunsa yayi da suka dan chanja launi zuwa wata kalar sannan cikin kasalalliyar murya me nuna tsantsanin sha'awar da yake ciki yace;
"Baby girl!"...
Bata rai tayi sosai dan ba karamin haushi sunan take ji ba, ta rasa meyasa yake cemata 'baby girl' dinnan, sai kace wata jaririya, ga takaicin matsetan daya sakeyi bayan duk abinda ya gama mata, yana cewa daddy dan iska ne ai gashi babban dan iskan, idan daddy beyi raping dinta ba ai gashi shi yana kokarin yi, saita kudirta aranta in basu mutu a yau ba zata fita sabgarshi na har abada...
"Yanxu ya kikeso muyi da kika hanani fita?"....
"Ni in fita sai kai ka wuce"....
"Not even in your dreams baby girl!"....
"Toh mubi takansu kawai mu huce"...
Dariya sosai yayi kamar wanda bashida damuwa...
"Allah ko baby girl?"....
Ya fada yana dan sassauta rikon daya mata....
"That's not my name"...
"Toh Zainab?"....
Kada Kai tayi alamar ita ba sunanta Zainab ba.....
"Fatima?"...
Nanma Kada Kai ta sakeyi....
"Toh menene sunanki?"
"Fatima Zainab!".....
Zeyi magana Kenan suka farajin harbi ta ko ina, kara kwantar da ita yayi a faffadan kirjinsa yana lalubo bindigar da besan inda ya jefata ba, chan kuma sai sukaji jiniyar motar yan sanda na tashi a gurin, ashe harbi ake tsakanin Yan sanda da wa'yenda suka tare su......
After like 5mins kuma gurin yayi tsit bayan yan sandan sunci galaba akansu dukda wasu sun gudu amma ankama wasu, sai a lokacin Deen ya hango khaleel dayake tsaye kusa da wani dan sanda....
Dagota yayi yana fadin;
"Your boyfriend came to save us, but he still doesn't deserve you!.....
Dagowa tayi da sauri idonta ya sauka akan khaleel itama, da sauri ta sauka daga kan cinyarsa ta murda kofa da niyar ta fita kawai ta jita a rufe, ashe yayi maza yasa lock kamar yasan fita zatayi......
Bece mata komai ba ya figi motar a guje ya bar gurin.....
Khaleel dayaga haka yace subi motar da sauri Dan ya tabbatar Fatima Zainab na ciki.....
Tinda daddy ya fara waya yake bayansa, babu abinda beji ba har wayar da daddy ya sakeyi na biyu yaji yana cewa a tabbatar an kashe yaron dan ya riga yasan sirrinsu, ita Kuma Fatima Zainab a kawota kar aikin da aka basa akanta ya lalace, he was so heartbroken ace daddy ne yakesan cutar da abinda yasan yana tsananin so, labewa yayi da sauri ganin daddy ya juyo, daddy na barin gurin ya tafi straightly ya kwaso yan sanda, haka sukayita tracing mutanen daddy har Allah yasa suka gano inda suke sukayi attacking dinsu....
Yana kokarin yaje ya duba motar kuma yaga anja motar alamun babu abinda ya samu wayenda suke ciki, sosai ranshi ya baci dan besan waye ya tafi da itaba saboda daddy be kama sunan meshi ba, shiyasa yace su bisu da sauri kar suje Shima kokarin cutar da ita yake, ya Kuma kudirta aransa saiya gano duk abinda su daddy suke sannan ya tona musu asiri....

WACECE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)Where stories live. Discover now