21

23 1 0
                                    

Cikin bacci me nauyin daya dauketa takejin wani bakon al'amari da bata gane kansa ba, sam ta kasa tantance wani yanayi take ciki hasalima bata gane meke faruwa ba, kamar dai lips dinta ake tabawa tadai rasa me takeji gashi ta kasa motsawa, haka ta daure tanaji tana gani aka cigaba da mata abinda akaga dama akan lips, jin kamar an shaketa dan har lokacin bata gane abunda yake faruwa ba yasa ta kasa jurewa ta fara mutsu mutsu tana kokarin farkawa amma kuma saita kasa......
Jin motsinta ne yasa Deen janyewa da sauri yana ayyana irin karfin jininta, wannan abun da sameer ya shaka mata sai mutum yayi 24hrs be farkaba inba allura aka masa ba shine ita take motsi within few hours? It's surprising!, sai a lokacin kuma yagane aika aikan dayayi, meya hadashi da kissing yar mutane? Shida yakeso ya taimaketa ya fitar da ita daga gidan kafin wanchan dan iskan ya dawo shine ze bada kansa? dauke idonsa daga kan fuskarta yayi yana istigfari a ransa.....
Shafa lips dinsa daya jike yayi yanaji kamar har lokacin yana cikin bakinta, sai a lokacin yayi realizing ashe babu mask a fuskarsa, dube dube ya shigayi har ya gano mask din a kasan gado, mamaki ne ya kamasa dan ko zaa kashesa besan sanda ya cire mask din ba, he was lost indeed, shima kenan da ba ruwansa da mata couldn't control himself, toh inaga in sameer ne mayan mata? Kai anya ma be tabata ba? Wani mugun bacin rai ne yazo masa dan haka kawai yaki yarda sameer betaba yarinyar ba, koma dai menene yayiwa kansa alkawari ba wanda ze kara tabata, inta farfado kuma ze tambayeta WACECE ITA? Sannan ya sadata da iyayenta ya kuma basu shawara su mata aure kar a lalata musu yarinya, dan sameer ba kyaleta zeyi ba inba gani yayi tayi aure ba, ze kuma gaya musu karsu bawa khaleel dan duk basu dace da yarinyar ba, gwara su nemi wani nitsattse su ba......
Zagaye dakin ya shigayi yana tinanin mafita dan gaskiya bayaso sameer yazo ya samesa be fitar da yarinyar daga gidan ba, toh amma ina ze kaita? "Ka kaita gidanka mana" wata zuciyar ta fada masa haka, gyada kai yayi kamar yana magana da wani, ya yarda da shawarar kaita gidansa dari bisa dari dan it's the best solution for him tinda ba wanda yasan gidan a friends dinsa, wata zuciyar ce ta kuma ce masa "to amma mami ta sani ai, what if she come looking for you?"..... Girgiza kai yayi yana fadin "no zan fitar da ita daga gidan kafin mami tayi tinanin ina chan"....
Wani lissafi ya kumayi yaga alamun komai ze tafi masa daidai , abinda zeyi shine ya kai yarinyar gidansa ya ajye sai ya dawo ya renawa sameer hankali yace shi dayazo bega kowa ba.... "Yes" ya fada yana kokarin daukarta.....
Daukarta yayi kamar wata yar baby a zuciyarsa yana fadin gata dai a haka kamar a cike amma she's weightless, kodai batacin abinci sosai ne?, tsaki yaja yana tamabayar kansa ina ruwansa?....
Carefully yake rike da ita gudin having body contact da ita amma duk da haka be tsiraba dan yanajin dumin jikinta sosai kamar wanda yake rungume da ita, haka ya daure ya karasa bakin mota da ita....
Bude gaban motar yayi ya zaunar da ita still tana nan a sumen da take, sannan ya kwantar mata da sit din sosai yanda zataji dadin kwanciyar ya kuma gyara mata zaman hijabinta.....
Bude gate yayi kasancewar babu me gadi a gidan tinda ba wani zama suke ba, ya fita da motar waje sannan ya kara dawowa ya rufe gate da gidan gabadaya ya nufi mota.....
Kamar a mafarki yaga mutum ya bude masa gaban mota harda zira hannu yana kokarin zaro ta.......
Saida jijiyoyin wuyarsa suka fito tsabar bacin rai, toh shikuma wannan dan rainin hankalin daga ina?....
Fincikosa yayi da karfi sannan ya hankadasa chan gefe, cikin bacin rai da takaici Deen yace;
"Who the hell are you da kake kokarin zaro min mata daga mota? You must be very stupid"....
Tasowa yayi da sauri yana kakkabe jikinsa, cikin jin haushi shima yace;
"Kai ya kamata in tambaya ina zaka kaimin mata, dagayin tafiyar kwana biyu shikenan saiku sata a gaba?, bame tabamin ita ya zauna lafiya wallahi!!!"....
"Ji wani shashasha mahaukaci, a masallacin ubanwa aka daura muku auren da zakace matarka ce, kai dalla ware dan wallahi ka bari na fusata sai na zubar maka da hakoran gaba duka, ba kunya ba tsoron Allah kazo kuna claiming matar mutane!"....
Deen ya fada yanajin kamar ya daddalla masa mari, saidai bata wannan yake ba, burinsa kawai ya gudu da yarinyar kafin sameer ya dawo, gashi wani dan iska yazo ze rena masa hankali ya bata masa lokaci .....
"Idan kana san rayuwarka ka bani matata mu tafi".....
Deen besan sanda ya zabga masa wani wawan mari tsabar bacin rai jin ya kara maimaita kalmar matarsa ce, ko a gidan ubanwa aka daura musu aure oh........
Wata muguwar dariya ya fashe dashi yace....
"Ni ka mara? Hhhhh karshen ka yazo yaro"...
Wani marin ya kara masa dan ba karamin haushin dariyar yaji ba, sannan cikin masifa yace;
"An kara maka wani, do your worst karamin dan iska kawai, now bani hanya!"....
Yana fadin haka ya shige mota yasa lock, kokarin tada motar yayi mota tace to tadani kagani, babu kalan dabarun da beyiba amma shiru mota taki tashi, jin yana juyo dariyar dan iskan chan ne yasasa whining glass dan yaga meyake yiwa dariya....
Yana bude glass din ko yajuyo shi yana fadin;
"Hhhhhh kai ka dauka zaka mareni har so biyu kaci bulus? Inaaa, ai in fadamaka kome zakayi motarnan bazata tashi ba, bama motar ba babu inda zaka iya motsawa daga nan inba bani matata kayi na tafi ba".....
Wani agogon sameer me tsada da yake cikin motar Deen ya dauka ya cilla masa a goshi, a take goshin ya fara zubar da jini, murmushi Deen yayi yace;
"Ka kara kiranta matarka a gurin nan wallahi saina kasheka, na kuma kashe banza a banza! Wato kai shedani ko? Toh ko bude idonka da kyau kaga yanda zan bar gurinnan da ita akan idanunka, duk shaidancin da kakeji dashi na fika wallahi"........
Sai kuma ya kalli fatima zainab ya harareta yana fadin;
"Ashe a cikin kwashe kwashen naki harda shaidani? Ba dole kita abu kamar mara hankali ba, zamu gamu ne in kika farka, saina saitaki da kyau kafin in kaiki gun iyayenki!"..
Sai ya maza ya zuge glass dan bayason jin abinda wanchan wawan zece, wani cassette din Quran yasaka ya kunna suratul baqarah yayi bismillah ya sake tashin motar, cikin ikon Allah ko motar ta tashi, figarta yayi a guje ya bar wanchan da sakekken baki..........

WACECE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)Onde histórias criam vida. Descubra agora