43

27 2 1
                                    

Dagowa Abby yayi ya kalli deen da yabi hanyar da ba nan bane rest room din ba.....Nuna dayan side din yayi yace;
"That's the rest room over there".....
"Okay"....
Deen ya fada yana fasa yaye labulen......
Shiga yayi ya gama harkokin gabansa sannan ya dawo ya zauna inda ya tashi......
Sai a lokacin fatima zainab ta zame jikinta daga na khaleel jin abinda takeji ya ragu saidai har lokacin tanajin kirjinta na bugawa kadan kadan.......
"Relax love, Nothing's gonna happen, relax okay?"......
Khaleel ya rada mata a kunne cikin tausasawa......
Gyada mishi kai kawai tayi sannan ta lumshe ido kamar me jin bacci, khaleel be kara cewa komai ba duk a tinaninsa bacci take nan ko wani tashin hankalin takeji a ranta.......
Tinda Deen ya dawo ya zauna ya nemi nitsuwarsa ya rasa, ko dazu daya shiga toilet yaje ya danyi clearing mind dinsa ne saboda false abu da take gayamasa, ya ma zaayi ace yanajin irin abinda yake ji idan tana kusa dashi bayan yasan daga shi sai Abby a cikin jirgin, abun mamaki koda ya dawo be samu nitsuwar da yake so ba sai ma bunkasa da abinda yakeji yayi, daurewa yayi ya cigaba da kame kansa dan in zebi ta zuciyarsa tashi zeyi ya duba lungu da sako na jirgin saidai hakan babu tsari sam tinda Abby na nan, abin ne yaci karfinsa ya fara juye juye be sani ba, rikicewa yayi ya fara kalle kalle daga zaunen da yake kamar wanda yake neman wani abu.......
Abby da yaga sai kalle kalle Deen yake ya tabasa yace;
"Wani abun kakeso ne?"......
Girgiza kai yayi da sauri cikin san waskewa yace;
"No, not at all, I was just surveying the plane dake akwai wani project da nake akan aircraft cabin so I was using the opportunity".....
"Okay nagane, that's very good, I'm proud of you son"......
"Thank you Abby".......
Murmushi Abby yayi cikin sanyin murya yace;
"tell me about her".....
Kallonsa Deen yayi cikin rashin fahimta yace;
"Who?"......
"Boddi na!"....
Abby ya fada yana blushing.....
Yake Deen yayi yace;
"She's fine! Ai zamu je kaganta".......
Murmushi Abby yayi sannan cikin wani irin yanayi daya tsinci kansa yace;
"Is she still gentle?"....
Gyada masa kai kawai Deen yayi alamun yes.....
"I'm glad she still is"....
Deen be basa amsa ba ya jewo masa tambayar datake ransa tin farkon ganin daya masa saidai abinda yake kansa yasa ya sha'afa.....
"Ina baby tee?"......
Dan shiru abby yayi sai chan kuma kamar wanda ake bawa umarnin magana yace;
"She's fine".....
"Good, zan bika in ganta kafin na dawo dubai"....
Cikin sanyin murya abby yace;
"Okay"......
Daganan kuma sai shiru ya biyo baya, ba wanda ya sake cewa komai amma kowa da abinda ke damunsa a rai, haka suka cigaba da tafiya in silence duk bayan after 30 mins air hostress ke kawo musu menu su zabi abinda sukeso dan long journey ne, likewise su khaleel da fatima zainab saidai akwai direct entrance ta chan da ba sai anbi ta gurin su deen ba........
"Wifey?".....
Khaleel da yaji tanata motsi ya kirata.....
"Yes honey"....
Ta amsa masa cike da so da kauna......
Murmushin jindadi yayi yace;
"I am the luckiest person in the world to have you, my love. Every day I realize how lucky I am to have your love, your kindness and your devotion. You make my life better by existing. I hope you know how every little thing you do makes my life better and brighter; I value you so much that sometimes I just stop and look at you thinking about how very lucky I am to have found you. My heart just swells up with love for you, with every day in my heart, I cherish your love!".........
Wani irin kallo ta masa with much adoration tac;
"I looked around the world and I've not seen any man as great and caring as you are, having you has made me the Luckiest woman darling".......
Ai ji yayi kamar ya tashi sama dan dadi, besan sanda ya zage ya cigaba da zubo mata dadadan kalamai ba;
"Kin wadata zuciyata da farin ciki, kin haskaka rayuwata da haskenki, kulawarki a gare ni ta musamman ce, hakan ya sa nake jin kaina tamkar sarkin wata masarauta mafi girma da ƙarfin iko. Ina Son Ki Sosai My Wife To Be!"......
Kasa magana tayi tsabar yanda kalaman dayake mata yake tsumata yake sata farin ciki da nishadi....
"Koda a ce za ki sa wuta a jikina na babbake na zama toka, ba zan damu ba, matuƙar zaki ɗauke ni, ki kasance tare da ni a duk inda kike. Fatana mu kasance tare da juna a cikin wuya ko daɗi. Ina Son Ki Wifey"......
Khaleel ya sake fada yana kallon kwayar idonta cike da shauki da kauna......
Ware idanunta tayi yanda zasuji dadin saka ido cikin na juna tace;
"Na maka alkawari darling khal, na maka alkawari zan kasance da kai duk rintsi duk wuya, Ina Sonka nima!"........
"Har in mutu bazan taba mantawa da wannan ranar ba, kin gama min komai wifey! I love you is an understatement"......
Tini ta manta da wani bugun zuciya da tsoro da takeji suka cigaba da soyayyewarsu while jirgi nata tafiya.......

WACECE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)Where stories live. Discover now