27-28

29 0 0
                                    

"I know you're fooling me dan Allah ki tashi!"...
Deen ya sake fada a rude yana kara tarota jin yanda ta sake masa jiki gabadaya.....
Ganin bata motsa ba sai abun ya kara rudardashi ya rasa taimakon daya kamata ya bata gashi ya kasa yarda ba wani makircin takeson shirya masa ba.....
Kallon gurin yayi yaga babu wanda yake ganinsu sai kuma ya dawo da kallonsa kan fuskarta, murmushi ne ya subucema beneath his breath yace;
"There's more to this beauty, it's still dangerous!"..

"Ke wa zaki maida wawa? Allah idan baki tashi ba zan sakeki ki fadi a gurinnan, I'm serious!"....
Ya fada trying to distract his heart from abinda yake raya masa, shiyasa bayason kallon fuskarta cuz she's so tempting yanzu saika kauce baka sani ba, since she came into his life komai ya chanja masa, sam baya gane kansa when it comes to her, yasan baya sonta but it seems what he's feeling over her is just 'lust'(sha'awa) which is haram in islam and he can't help it, ya kuma gane hakan ne tun ranar dayayi kissing dinta dan be kara bacci me dadi ba, he just want more and more and more, even beyond kiss, he just want to explore her inner self and see her in her full glory, har ciwon mara ya fara a yan kwanakinnan abinda be tabayi ba.....
Yafi 10mins yana mata kashedi da warning akan in bata tashi ba ze saketa a kasa, as a Doctor he should have known idan suman gsky tayi amma baya fahimtar karatun likitancinsa when it comes to her, saida yaga kamar dagaske bata numfashi sannan ya dauketa ya sata a motar da tazo....
Kwantar da kujerar dake kusa da driver seat yayi sannan ya kwantar da ita yanda zeke ganinta sosai sannan ya shiga yaja motar with the thought of ina ya kamata ya kaita, gashi yanzu bayason kaita gidansa cuz he don't trust himself anymore, a yanda zuciyarsa ke ayyana masa abubuwa dayawa dinnan sam bayasan kebewarsu a inda yasan ba wanda ze iya kawo mata dauki inma wani abun ze mata......
Tada motar yayi yayi reverse ya fita daga harabar hotel din gabadaya.....
Tunda ya hau titi yake tinanin inda ya kamata ya kaita da baze samu problem ba, bama wannan ba a wani yanayi zata farka yanzu? Ze kaita gidan mutane ne ta musu fashe fashen data saba? Ko ze kaita gidan mutane aljanunta su tashi arasa yanda zaayi da ita?... Sai kuma ya kalli zoben daya cire daga hannunta yaga kamar yayi baki ba yanda ya cireshi ba, sai a lokacin kansa ya kawo huta, could it be cire zobennan ne ya sumar da ita? Dan if he can recall yana cirewa ta sume masa, toh meye a tare da zoben? Gashi tabbas ya taba ganin zoben a hannun wani, wanda yaga zoben a hannunshi be kuma yarda dashi ba, sannan according to the tracker taje gidansu alhaji ibrahim mahaifin saurayinta khaleel, toh meya kaita gidan saurayi bayan ancemasa khaleel din baya kasar, toh ko yana kasar ai be kamata taje ba, ko duk rashin kamun kanta ne dan yasan babu abinda bazata aikata ba...
Dan dakatar da tinaninsa yayi ya juyo ya kalleta, yanda ya kwantar da ita haka take saidai kanta yayi gefe wanda hakan yasa hular datasa zamewa daga kanta dayake tanada tsantsin gashi sosai, mayafinta ko dama tinda ya tareta ya zame, da kyar ya daure yaki bawa kansa damar kallon fiye da fuskarta.....
Tsaki yaja kamar tana jinsa yace;
"Wato har attachment kike sawa ko? Tayaya aljanu bazasu dinga bin mutum ba?".....
Sai kuma ya samu kansa da tura hannunsa cikin gashin nata, sosai tsantsi da kamshin gashin ya tafi da imaninsa har besan sanda yace;
"Dama haka attachment din yake so soft? I love the texture!"......
Haka ya cigaba da tura hannunsa a gashin nata at the same time yana driving da dayan hannun.........
Horn yaji anayi masa da karfi ashe yabi one way be sani ba, da sauri yayi gefe da motar inda Allah ya taimakesa space ne da Allah kadai yasan me zasu daka daba karamin accident zasuyi ba, yana cemata bata iya driving ba sai gashi shima ze tapka shirme...
Parking yayi ya daki steering din motar yana fadin;
"Damn it! Kedai komai naki masifa ne, gashi kinsa garin taba artificial gashinki zan kashemu a banza!"......
Sai kuma ya kwantar da kansa ya shiga tinaninta duk da tana kusa dashi.....
Yana cikin wannan hali wayarsa ta fara ringing, dagowa yayi da sauri yana duban me kiran, sosai hankalinsa ya tashi ganin Mami ke kira, yanzu haka an kirasu ko sunje basu gansaba shine take kiransa a waya, wai ya akayi ya manta da consequences din gudunwan dayayi ne, this girl has been putting him in more and more trouble tinda tashigo rayuwarsa...
Yanke shawarar yayi ignoring call din kawai yayi idan yaso in yagama da issue dinta sai yaje yayi facing dinsu.....
Saida ta masa five missed calls sannan ta hakura, ya sauke wani gauron ajiyar zuciya yana addu'ar Allah yasa karta kara kira.... Saidai kash addu'arsa bata karbu ba dan baifi minti uku ta bayar a tsakani ba ta cigaba da kira, duk yanda yaso ya share kasawa yayi saboda kiran is getting out of hand, saida ta mishi 10 missed calls sannan ya daure ya daga wayar.....
"Hello son, kana ina? Can you hear me? Is this you?".....
Shiru yayi yana kokarin tantance yanayin datayi maganar, indai ba kunnensa bane ya jiyomasa ba daidai ba kamar mami kuka take, toh what could have happened?.....
"Dan Allah Saifuddeen kamin magana, tell me you're not dead kar zuciyata ta buga, you won't understand how much I love you"....
Ya sake tsinto muryarta tana fadin haka cikin shasshekar kuka.....
"Relax Mami! It's me meyafaru? Pls stop crying you're breaking my heart".....
Ya fada yanajin zuciyarsa kamar zatayi tsalle ta fado, this is unbelievable! Ace Mami na kuka? No!".....
"Yimin magana sosai inji muryarka, ka tabbata kaine kuwa?".....
"Yes mom, meyafaru dan Allah kidena kuka, tell me what happened?"......
Katseshi tayi da fadin;
"Kana ina yanzu?".....
"Ina prison"....
Ya fada kasa kasa....
"It can't be! yanzu haka muna prison, and I'm glad bakanan, tell me where are you now?".....
"Ina wani guri trying to sort some things out, I'll see you later".....
"Start coming home now please"....
"I can't come home, I have a very big issue"....
"Koma menene just come, I promise to help you out, dan Allah ka taho gida"......
"Bani kadai bane Mami kuma bazan iya barin meshi in tawo ba"....
"Naji koma waye ku taho tare".....
Ajiyar zuciya ya sauke dan har lokacin beji ze iya zuwa da ita gidan ba....
Daurewa yayi yace;
"Promise me you won't judge me ko dawa nazo?"..
"I promise you"
Ta fada without hesitation....
"Kinyi alkawari bazaki min fada ba koda wa nazo?"....
"Nayi"....
Mami da take cikin tashin hankali ta sake fada batasanma ta fada ba......
"I'll be there in 15mins"
Yana fadin haka ya kashe wayar yana tada motar.....

WACECE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)Where stories live. Discover now