15

22 0 0
                                    

"Nace ki fadamin abinda kika gani pls"....
Jamila ta fada tanajin kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a Nigeria.......
"Hmmm wannan maganar bata waya bace!,just come and see for yourself!"....
Numfashi ta sauke daga daya barin tana fadin
"Just tell me,I promise you I'm on my way today,koda hint ne ki bani,har kinsa zuciyata tinani iri iri wallahi".....
"No sis,just calm down,trust me ina da dalilin kin fadamiki a waya,gwara dai in kinzo din we'll figure it out together okay?"....
"Shikenan,toh ya jikinsu Deen?".....
"Alhamdulillah zaace,dan shi ya farka ma,itadai tananan a kwance"...
"Allah sarki,Allah ya tashi kafadunta ya basu lfy duka".......
"Ameen ya Allah".......

Sosai Deen yake kallonta kamar tsohon maye,ayanda yake karewa fuskarta kallo yasan tsap aka basa abun zane ze zanata,kyakkyawa ce ajin farko,irin kyawunnan me shegen daukan ido da kallo daya zaka yiwa mutum kasan yanada kyau,fara ce amma ba chanchan ba,color dinta kamar dai half cast,kallonta ya karayi tindaga goshinta harya karaso habarta,goshinta na dauke da dot din sallah kasancewarta ma'abociyar ibada sosai,hakan sai ya kawata kyawun fuskarta,gashin girarta baki wulik ne da saika dauka tayi brow tint,gashi da curve shaped me kyau,tsabar cika har hadewa girar keyi,it's just a perfect curved brows!.... Murmushi yayi yana kallon dogon hancinta me kyau kamar ka cireshi ka gudu,ana cewa yana da dogon hanci yau sai yaga na wacce yafi nashi kyau?....
"Fatabarakallahu ahsanul khaliqeen"...
Ya fada beneath his breath a yayinda ya kara dora idonsa akan idanunta dake a rufe,ko a haka mutum na gani yasan manyan idanu ne da ita,toh inaga inta budesu?... Dafe kai yayi jin mere thought of bude idanunta is driving him crazy.....
"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel"....
Ya fada yana sauke idonsa akan pouted cute lips dinta,ze iya cewa tinda yake be taba ganin cute attractive lips irin nata ba,infact shi be taba karewa mace kallo irin haka ba sai akanta,sai kuma ya fara tambayar kansa anya shi psychopath ne kuwa kamar yanda ake fada? Cuz what he's feeling is a raw feeling,bawai sonta yake ba dan ba wannan a dictionary dinshi,but he's actually feeling something unusual,kamar magic haka yaji abu na fizgarsa zuwa gareta especially her lips,he just want to know how they feel,a yanda yake kallonsu daga gani zasuyi laushi so he wants to confirm,ba wai kissing dinta zeyi ba,he just want to screen them with maybe his fingers,yasan idan ya shafasu ze gane,karasawa dab da ita yayi yana cigaba da kallonta........
"She's dangerously beautiful!".....
Ya fada yana kokarin dora hannunshi akan lips dinta......... Sallamarta ce ta katseshi,yayi saurin janye hannunsa.....
Karasowa tayi fuskarta ba yabo ba fallasa tace
"WACECE ITA?!"......
A razane yace
"ban wacece ita ba"....
"Bakasan wacece itaba? Har kukayi accident tare?, don't forget you're talking to a judge! My friend explain yourself!".....
"Trust me,mami wallahi bansan wacece ita ba,she only helped me,unfortunately sai mukayi accident"
Deen ya fada obediently,ba itaba har shi kansa saida yayi mamakin yanda ya mata magana with respect yau...
Dan shiru ne ya biyo baya kafin tayi breaking silence din da fadin
"Ka fadamin gsky tin yanzu dan wallahi idan nayi bincike nayi finding out abunda ka fada karyane,I'll deal with you,kasanni sarai!"....
"Yes,bansan taba but I want to know who is she too"....
Girgiza kai mami kawai tayi,a ranta tana fadin 'anzo gurin', as a judge tasan koyaya there's something,sannan one thing she loves about Saifuddeen shine baya karya,very straightforward mutum ne shi,tin farko ta yarda besan yarinyar ba amma tasan akwai wata a kasa shiyasa tace mishi zatayi bincike,shikuma yasan tinda tace zatayi bincike zata gano komai shiyasa kawai ya fada mata abinda ke ransa,yasan kuma she's a very smart person kusan a gurinta ma ya dauko smartness dinsa........
Ganin batace komai ba ya kalleta kamar me tsoron yin magana yace
"Mami don't judge me,amma dan Allah what do you notice about this girl?"...
Kallon fatima zainab mami tayi,tadanyi smiling sannan tace....
"She's very beautiful,nasan abinda ke ranka kenan?"....
Girgiza kai yayi yace
"I know she's so gorgeous but there's something in between that beauty,ki kalleta sosai"....
Girgiza kai mami tayi tace...
"I can only see a young pretty lady sleeping peacefully,no in between!"......
"I know,but she looks dangerous"....
Zaro ido mami tayi tana fadin......
"Dangerous kuma?,what do you mean by that?,how can a person look dangerous Saifuddeen?"...
"Dangerous might not be the right word,but trust me akwai wani abu a tattare da yarinyar nan,bansani ba ko nikadai ke gani,but I'm assuring you she's not okay"......
"Saidai idan you're mistaken,but this lady is perfectly alright,bansan wannan halin naka Saifuddeen, hakanan sai kaga mutum kace he's not ok,da alamu kai kanka you're not ok".....
Murmushi sosai Deen yayi yace...
"Ai ni koda yaushe I'm not ok a idonki mami,amma yarinyarnan hmmm let me just keep quiet,well zakiga abunda nake cewa wataran"........
Mami zatayi magana kenan sukaji sallamar mutane.....
Bude ido mami tayi ganin yan sanda sun zagaye dakin,kafin tace wani abu daya daga cikinsu ya nufi gurin Deen da handcuff a hannu,yana fadin
"You're under arrest sir!,silently follow us to the station".....
"Arrest?, For what?"....
Mami ta fada tana wondering mai Deen ya aikata?
"Yes ma,ganinki a gurinnan ne yasa bamu sa masa handcuffs ba duk da bamusan alakarku ba,so tell him to follow us quietly".....
Ajiyar zuciya mami ta sauke sannan tace
"He's my son!, I'll get him to the station my self,ku muje!"....
Sai a lokacin Deen ya dago,ya kalli doctor yaname nuni da fatima zainab yace
"Pls take very good care of her for me,I'll definitely come back soon for her!"......
Murmushi Doctor yayi yana nodding kansa,mami ko binshi da wani mugun kallo tayi,ace anzo kamaka amma ko a jikinka saima bada wani sako da kakeyi,wani kalan mutum ne Deen?....

WACECE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)Where stories live. Discover now