23

22 2 0
                                    

Tasowa mai gadin gidan yayi da sauri ya leka ta karamin gate dan yaga su waye......
Sameer ganin mai gadi ya leko ya sasa fitowa daga mota yazo ya samesa yana tambayarsa ko mai gidan na nan.....
"Eh yana nan"...
Mai gadin ya basa ansa...
"Toh ko zaka iya mana sallama dashi?"....
"Toh shikenan bari in sanar masa, amma wa zaa ce?"...
"Kace masa sameer ne"...
"Toh ina zuwa"...
Gyada kai Sameer yayi yayinda mai gadin ya shiga ciki dan neman izinin Deen....
Dai dai kofar main parlour sukayi kicibus da Deen daya fito jin karar horn sosai.....
Gaishesa mai gadin ya karayi kamar ba dazun suka gaisa ba, be amsa ba yace masa;
"Ya akayi"
"Sallama akeyi da kai yallabai"....
"Waye?".....
"Yace ace sameer"....
Dan jim Deen yayi yana tinanin su mami dake ciki, baze so sameer ya hadu da mami yanzu ba dan yasan haduwarsu bazatayi kyau ba, sannan bayasan sameer yaga yarinyar, so yake kawai ya maida ita gidansu batareda sameer ya biya bukatarsa ba, sai kuma yasa masa ido karya kuma kai mata hari.......
"Kace masa ina zuwa".......
Deen ya fada yana komawa ciki.......
Juyawa mai gadi yayi dan ya isar da sakon.......
Sameer na hango fitowar Deen ya kalli mutumin dake gefensa yace;
"Gashi ya fito, muje!",,,
Kallon Deen yayi ya girgiza kai yace;
"Bana fadamaka yana nan tareda yarinyar ba? Yanzu ka yarda dani?".....
"Sosai, muje mu samesa"...
"No basai naje ba, duk abinda zece maka karka yarda dan tana cikin gidannan"......
"Toh nagode"....
Fita daga motar Sameer yayi ya karasa inda Deen yake a tsaye a bakin gate......
Mika masa hannu Deen yayi suka gaisa sannan yace;
"Ashe kana tafe"...
"Ka fadi haka mana, wallahi Deen ka bani mamaki, ashe kaima sonta kake shine kake raina min hankali tuntini?"......
Cewar sameer rai a hade.....
"You're very stupid for saying this! An gayamaka kowa shashasha ne irin ku da zaka zo kana gayamin maganar banza daga taimako, kai yanzu kana tinanin zan iya san yarinyar da kuke hauka akai? Toh ka bude kunnuwanka da kyau kaji I can never stoop so low and love the fucking girl you're talking about, now get out of my sight".....
Deen ya fada cikin zafin rai kamar ze mari sameer, dama yana neman wanda ze saukema bacin ran dayake fama dashi sai ga sameer yazo masa da maganar banza......
Ganin yanda Deen ya fusata yasa sameer kama kansa, dama ba wani yarda yayi da zancen ba, amma kuma abinda yake daure mishi kai ya akayi yaga Deen a gidan kamar yanda wancan ya fada?.....
Dafa kafadar Deen yayi yana fadin;
"Calm down man, abin be kai haka ba, I guess i misunderstood, honestly ba laifina bane wani ne ya fadamin haka"...
Nan ya kwashe duka yanda sukayi da wanchan ya fadawa Deen....
Jinjina kai Deen yayi yace;
"Ya yake"....
Describing dinsa yayi kamar yanda Deen yayi expecting, ya kuma fadamasa tare sukazo, yana cikin mota ma......
"Muje na gansa"....
Karasawa gurin motar sukayi, sameer ya zagaya ta inda mutumin yake zaune ya bude kofa yana mishi magana ya fito......
Shiru yaji baa amsa ba....
Lekawa ciki yayi yana tinanin ko ya chanja guri ne, sai yaga wayam, sama da kasa kuma ya nemesa ya rasa a motar.... A birkice ya shiga duba ko ina a motar Deen na tsaye yana binshi da kallon banza....
Ba karamin tsorata sameer yayi ba da ganin baiga mutumin a ciki ba, if he can recall ya fita ya barsa a ciki kuma shida Deen na facing inda motar take so bayanda zaayi ya fita be sani ba, abu kamar magic?...
Dage kafada Deen yayi yace;
"How can you even believe a stranger? Dan iskan ai da yasani ya tsaya danaci ubansa a gurinnan, Well zan baka shawara karka kara bawa shedaninchan face if not kai zaka kwan ciki, ruwanka kuma ka yarda dani ruwanka ka yarda dashi".....
Cikin zaro ido dan harga Allah har lokacin a tsorace yake yace;
"What do you mean by shedani?"......
"You'll see for yourself if you keep on believing him har kana zuwa kana min shouting, kaga bacewar nan dayayi? Kadanne daga cikin abinda zaka gani, just give him chance and see"...
"Boss why're you doing this to me? Kana nufin ba mutum bane, stop giving me uncompleted statement pls, bakaga yanda na tsorata ba wallahi"....
"Bakaga komai ba! I've said enough!"...
"Yanzu gidan waye wannan toh?"..
"Mami, ko zaka shiga ku gaisa? Dama nemanka take!"....
"Ni? Haba? Inaa.. Bazan shiga ba, yauwa why are you here? Tagane ka gudu ne?"...
Sameer ya fada a rikice kamar ze zura a guje, be gama fita daga wanchan rudanin ba ga wani kuma, shiko ina zesa ransa?....
"Yes ta kuma gane dasa hannunka, she traced me even before I get to your house, Allah ne ya rufa maka asiri dan har base taje nemanka baka nan, I'll advice you ka rufawa kanka asiri ka bar garinnan because she's taking this thing beyond your imagination!"........
"Innalillahi kace muna ruwa, yanzu haka tana ciki kace?"....
"You can go in and see for yourself, duk abinda ya faru kuma don't blame be"...,
"Naji naji let me start leaving, but what about the girl? Naje base banganta ba, thought kai ka tafi da ita a daura auren"....
"Wani irin nina tafi da ita? Ina fadamaka ko base banje ba mami tayi attacking dina, kaje dai ka duba inda ka ajyeta, da zaka rufawa kanka asiri daka rabu da yarinyar nan cuz wahala kawai zaka sha a gurin wanchan dan iskan".....
Cikin kwarin gwiwa sameer yace;
"Wani irin wahala, I'll know how to handle everything too, bari dai na tafi yanzu inje in kara duba yarinyar"....
"Ok, don't forget to leave abuja today! If not kasan sauran!".....
"Yes I'll, yanzu zanje in duba yarinyar, I'm very sure tana gidan, kawai saina koma US da ita"....
Daga kafada Deen yayi yace;
"As you wish".....
Sannan ya juya ya shige batareda yajira amsar sameer ba.....
Harya shiga mota wani dan shakku ya shiga ransa akan maganar da Deen ya fadamasa, idan har mami ta kamasa da gaske kamar yanda ya fada zata barshi ya fito kuwa? Sannan dayace a masa sallama da mai gidan meyasa Deen ya fito inba gidansa bane?.... Sai kuma wata zuciyar tace masa Deen baze maka karya ba, musamman bacewar da mutumin chan yayi yasasa karyata abinda ya fada masa, ya dauki maganganin Deen ya yarda dasu.....
Sai kawai ya tada motar yayi ya bar layin.....
Driving yake da sauri yana tsara yanda ya kamata yabar kasar da yarinyar, kamar ance juyo kawai yaga mutum a zaune a bayan mota yana masa murmushi....
Taka burki yayi da sauri yana fadin;
"Na shiga uku, dama Deen saida kace zanga abinda yafi wanchan".....

WACECE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)Where stories live. Discover now