50

15 1 0
                                    

Shiru tayi batace komai ba.....
Ganin shirun yayi yawa mami tace;;
"Muna sauraranki baby tee".....
Shiru ne ya sake biyowa baya yayinda zuciyoyin wasu ke bugawa, ba Deen kadai ba har khaleel dayasan ba'a daura ba hankalinsa a tashe yake jin tayi shiru......
Da mamaki umm ta kalleta tace;
"Why are you taking time to respond, ko abinda kika fadamin ba gaskiya bane?".....
"Gaskiya ne!"....
Ta fada tana sunkuyar da kai...
"Then answer us!"....
Dagowa tayi suka hada ido da deen da yake mata pleading look, sai mata signal yake akan tace eh, dauke kai tayi tace;
"Ba'a daura ba!"......
Ai deen ji yayi kamar ya shaketa tsabar takaici, ta gama ce masa ta yarda zatace an daura all of a sudden ta chanza baki without second thought, seriously he felt betrayed, duk sai yaji zaman parlourn ma ya ishe shi, ba dan yanasan komai ya faru a idonshi ba daya tashi yayi tafiyarsa, dole ya zauna ita kuma sai ya tabbatar yaci ubanta da kyau idan suka hadu, saita gayamasa dalilin yaudaransa datayi........
Gyaran murya abby yayi yace;
"Toh Alhamdulillah munji daga bakinta dukda nima nasan ba'a daura auren ba saboda wakilci da suka nemi in musu wanda nayita jan abun saboda banaso suyi aure batareda amincewar iyayansu ba, ashe ya'yana ne bansani ba"......
Gyada kai dad yayi yace;
"Masha Allah! Haka muke fata dama, ina amfanin yara suyi gaban kansu?".....
"Gaskiya ne, toh nidai inaso zan bawa khaleel auren fatima dan na masa alkawarin tsaya masa akan haka tin ba yau ba amma saida amincewarku duka!".....
"Na amince! Allah yasa ayi damu!"....
Mami ta fada tana murmushi......
Gyada kai dad yayi yana murmushin amincewa yace;
"Ameen ameen".....
Kallon umm Abby yayi yace;
"Baki ce komai ba boddi?".....
Wani irin bugawa kirjin deen yayi kamar shi aka tambaya, umm ce last hope dinshi akan kin yuwuwar aurennan, idan tace ta amince ai ya shiga uku, kallon Umm yayi yanata addu'ar Allah yasa su hada ido ya mata signal ko Allah zesa tace bata amince ba deep down kuma yasan be isa ya sata yin abinda batayi niya ba, saidai sam ko inda yake bata kalla ba........
"Ban amince ba!".....
Deen ya jiyo muryar umm kamar a mafarki tace hakan, gyara zamansa yayi yanajin kamar an zare masa wani abu daya tokare masa kirji, ze iya cewa tinda yake umm bata taba abinda ya burgeshi ba irin wannan.....
Da sauri kowa ya dago ya kalleta suna mamakin jin furucinta dan basu taba expecting haka daga gareta ba duba da irin kokarin da shi khaleel yayi har tonawa mahaifinsa asiri yayi sannan a gabanshi aka ciwa mahaifinsa mutunci amma dukda haka rokonsu yake a bashi baby tee.....
"Baki amince fa kikace boddi?"....
Abby ya tambaya dan ya sake tabbatar da abinda tace....
"Kwarai!"...
Ta fada ba alamun wasa....
Abinda basu sani ba kuma shine da gangan tayi hakan badan bataso a bawa khaleel ba sai dan son ganin reaction dinsa da ita baby tee din, shin dagaske tana sonsa data bisa wata kasar a daura musu aure ko kuwa a giyar hauka tayi hakan?.....
Ai kawai sai ganin khaleel sukayi ya rarrafa ya tafi gaban umm, hawaye ne suka shiga zubo masa yayinda yakejin wani zafi a zuciyarsa, ko bacci beyi jiya ba saboda damuwa data masa yawa, ba karamin karfin hali yayi jiya ba na ganin halin da daddy yake ciki, yes yasan cewa daddy me laifi ne amma hakan bazesa ya manta irin soyayyar daya nuna masa ba, ga momma itama ya manta when last sukayi waya dan ko ya kira bata dauka kuma duk saboda tace ya rabu da wifey ya ki, wifey din da yake tinanin itace only hope dinsa ake nema a hanashi itama, inaa zuciyarsa bazata iya dauka ba....
Hannayensa biyu ya hade alamar roko hawayen na zuba a idonsa yace;
"Dan Allah dan annabi umm ki taimakamin, idan kika hanani fatima nasan rayuwata tazo karshe, nasan abinda mukayi bamu kyauta ba but it was the only way out a lokacin saboda daddy ya ki daura mana aure, in baku bani auranta ba mutuwa zanyi, dan Allah ki taimaki rayuwa wallahi ina sonta tsakani da Allah".....
Ya kareshe da fashewa da kuka.....
Sosai ya bawa umm tausayi ta kuma gane duk abinda yake fada is coming directly from his heart, amma ta girgiza kai tace;
"Kayi hakuri khaleel na riga na mata miji ba tin yau ba"......
Baby tee na jin haka itama ta rarrafa gaban Umm, dafa kafafuwata tayi kamar zatayi kuka tace;
"Umm dan Allah ki amince, ni wallahi shi nakeso".....
Ba umm ba harta Deen da yake ganin ta yaudareshi tace ba'a daura ba beyi tinanin zata iya cewa tana son khaleel a gaban kowa ba.....
Dauke kai umm tayi kamar bata jita ba, sai kawai ta fashe da kuka itama, suka hadu sukaita rusa kuka ita da khaleel suna rokon umm akan ta amince, deen ko ji yake kamar yaje ya hadasu duka ya zane, shi khaleel din nema yafi bashi mamaki yanda yake kuka kamar mace, yanzu ita coward dinnan takeso ta aura? Ace kana grown up man ka tsaya kana kuka akan mace, wannan shine abun duka ba sanda, ita ko baby tee dama baya sata a lissafin mutanen dan haryanzu gani yake batasan me yake mata yawo akai ba.....
Tausayi suka bawa mami sosai harta kasa shiru, ta kalli umm tace;
"A taimaka mana a amince umm, ko nima sai nazo na duka na tayasu kukan ne?"......
Cikin tausayi Abby shima yace;
"Wlh kuwa boddi na dan Allah a duba lamarin"......
"Ya kamata kam tinda suna son junansu"..
Dad shima ya fada.....
Murmushi umm da duk take sauraransu tayi sannan tace;
"Na amince! Allah yasa hakan shi yafi alkhairi!".....
Deen na jin haka da sauri ya zabura yace;
"Toh ni ban amince!"....
Harararshi mami tayi tace;
"Da wa yake bukatar amincewarka?".....
Bata rai yayi yace;
"Toh kuna nufin kun basa ita kenan? Haba mami!".....
"Insha Allahu, me za'a fasa da yardar Allah tinda itama tanaso".....
"Wannan me ta sani akan soyayya? Ya ma zaayi ku biyemata?".....
"Wannan kuma kai ta shafa".....
Cije lips dinsa yayi yana tuno da plan b dinsa, kamar yasan za'a samu matsala shiyasa yazo a shirye, in wanchan beyi working out ba sai a koma wanchan...
"Toh haka ake bawa mutum aure ba'ayi tests ba?".....
Deen ya fada yana murmurshi ganin ya samo yanda ze dankesu cikin ruwan sanyi dan tsarin bappa ne ba'a taba bada aure sai anyi tests both mace da namiji....
Saida gaban khaleel ya fadi jin wannan furuci na deen, addu'arshi daya Allah yasa ita ba irin shi bace.....
Cikin gamsuwa umm ta gyada kai tace;
"Hakane, gobe sai aje ayi"...
Budar bakin deen yace;
"Ba sai sunje asibiti ba, their genotype is both SS, technically be kamata suyi aure"....
Kafin kowa yayi magana baby tee tayi saurin fadin;
"Naji ni inason sa a haka".....
Throw pillow din dake kusa dashi Deen ya dauka ya saita daidai dan bakinta ya jefa mata sannan a tsawace yace;
"Dalla yi mana shiru manya na magana kina wani sa baki, inji kin kara cewa kina sonshi wallahi saina fasa miki baki fitsararriya kawai!"......
Mami ce ta dakatar dashi da fadin;
"Sai me dan tace tana son sa? Karka kuskura ka kara mata tsawa dama!"...
Dad ne ya kalli Deen cikin rashin yarda da abinda ya fada yace;
"Ya akayi kasan genotype dinsu?"...
Shafa kansa yayi yace;
"I'm a Doctor dad, I have treated both of them before!"......
"Baka taba treating dina ba kuma ni ba SS bane!"....
Khaleel ya fada yana jin haushin deen......
"Probably kana dan yaro lokacin kuma wallahi kai SS ne!"....
"Kai kuma kana me a lokacin?!"....
Deen zeyi magana kenan umm ta dakatar dasu da fadin;
"Enough! Gobe kawai suje suyi test duk wani required tests, abar zancen haka".....

WACECE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)Where stories live. Discover now