20

29 3 3
                                    

Sameer besha wahala ba wurin samun wanda zasusa a matsayin Deen saboda irin kudin dayace ze bayar, abu dayane yaso bashi matsala gurin samun me irin stature din Deen... Wani bawan Allah ya samo dake fama da matsalolin rayuwa ga mahaifiyarsa kwance a asibiti rai a hannun Allah, su kuma basu da kudin da zasu biya a mata suggery, batareda da second thought ba yayi accepting offer din ko duba risk din beyiba kasancewarsa namiji kadai a gidansu so komai akansa yake.... A take Sameer ya bada kudin surgery din da zaama mamansu ya kuma masa alkawari da kudi me mugun yawa idan sun kammala, ya sashi yayiwa yan gidansu karyan ya samu aiki zeje interview wanda baze daukeshi sama da kwana uku ba dan Sameer ya tabbatar masa da kwana biyu kachal zeyi a ciki kafin Deen yazo ya karbi position dinsa....
Kiran Deen yayi a waya dan ya sanarmasa komai is set gasunan tawowa sai yaji wayar a kashe, be damuba tinda yasan inda Deen din yake bazeyiwu abarsa da waya koda yaushe ba, wai danma da matsayinsa yasa ake dan bashi yayi amfani da ita.......
Ba karamin rudewa Sameer yayi da aka hanasu ganin Deen ba, wai sai an basu permission din bari a gansa, su kuma baa ce musu wasu zasu zo ganinsa ba.. Rasa abunyi Sameer yayi chan dai yace musu su fadi ko nawa sukeso ze basu su barshi yaga Deen, ba karamin bacin rai suka nuna masa ba na renin hankalin daya musu kamar wasu kananun mutane, wai su zaayi bribing? Ganin fa wankin wula na neman kaishi dare dan harsun fara cewa ya fita ya sashi tambayar gurin wanda ake taking permission, saida suka gama shassharesa kafin su fada masa, bayanin da suka masa ne ya sashi gane mami suke nufi, murmushi yayi ganin abun yazo da sauki tinda mami ce, shida yasan da wannan rules din aida tina ya kirata ya nemi permission din, numberta ya lalubo ya shiga kiranta, bugu biyu ko ta dauka...
"Assalamu alaikum mami"
Ya fada cikin nitsuwa, ba kace su suke shirin aikata danyan aiki ba....
"Wa alaikassalam son"...
Kasancewar itama tanada numbersa a matsayinsa na abokin Deen, gashi kuma da shishshigi dan har kiranta yake ya gaisheta shiyasa akwai mutunci sosai a tsakaninsu...
"Ina wuni mami, ya gida ya aiki?"
"Alhamdulillah son, naga kana kira da Nigerian number, ka dawo kenan?"....
"Eh wallahi mami jiya na dawo, na kira wayar Deen yake fadamin tsautsayin daya faru, yanzu haka ma zuwana daga kano kenan nazo prison din da yake sai suke cemin sai anyi taking permission a gurinki sannan zaa iya ganinsa".......
"Oh Allah sarki, wallahi ninasa rule dinnan not to make things worse, kasan in ana visiting dinsa anyhow, anything can happen"....
Mami ta fada dan har cikin zuciyarta ta yarda sameer jiya yazo kasar, kuma tasan yanda yake son Deen ze iya barin komai a kano ya tawo abujan kamar yanda ya fadamata yazo.....
"Eh gsky hakane, nima naji dadin tsarin musamman da suka cemin ke kika sa"...
"Yeah, bari na musu magana yanzu, they'll let you in now"....
"Yauwa mami, thank you so much"....
"Don't mention"...
Ta fada tana kashe wayar.......
Tana kashe wayar ta kirasu tace they should allow him in he's also her son, sun so su fadamata yayi niyar bribing dinsu amma ganin tace he's her son yasa suka fasa fada.....
A take sukayi leading dinsu zuwa inda Deen yake Sameer ya bisu da harara....
Knocking Sameer yayi suka shiga, hango Deen sukayi a kwance a gado ya baza AC sai shan baccinsa yake yi.. Kafarsa Sameer yaja ya farka dan bashida nauyin bacci sam.....
Dariya sosai sameer ya shigayi, cikin shakiyanci yace;
"Boss gaskiya zaman prison ya karbe ka, har wani bacci kake hankali kwance"...
Batarai Deen yayi yace;
"Ya bazanyi bacci ba kuwa? Aini banga abinda ze hanani bacci a rayuwarnan ba, wani mafarki nake me dadi na wani abu da nake nema wai na ganshi shine kazo ka tasheni"....
"Kaidai fadi gaskiya ko soyayya ka fada bamu sani ba shine kake mafarkinta"...
"You're sick wallahi, a'a abinda yafi soyayya na fada dan rainin hankali kawai, ko an fadamaka kowa ne shashasha irinku kaida abokin ka da zaku tsaya kuna hauka akan mace?".....
"Hmmm na rabaka itafa soyayya baa cika mata baki, sanda kaima zaka rufta ai bazaka sani ba"....
"You dey craze? Sanda zanyi me? Allah ya kiyaye wallahi, wannan yarinyar da kuke hauka akanta Allah sa ba kwaila bace ma"....
Ya fada yana hararar sameer......
Dariya sameer ya shigayi yana fadin;
"Kai Kai kai na rabaka, bangani ba amma nasan wallahi ba kwaila bace, trust me idan ka ganta zaka tabbatar da abinda yasa muke hauka akanta"...
Tsaki yaja yace;
"Ba abinda zan tabbatar, banga kyawun macen daze dagamin hankali ba wallahi!"...
"Well zan iya yadda tinda yan gidanku kunada kyau sosai, da wannan kanwar mamin nan itama naga tanada kyau sosai, wallahi da tanada ya' sai na rokeku kun bani, kaima gashi baka da kanwa gsky ammin fuck up a gidanku"....
"Ai ko inada kanwa ko cousin from Umm wallahi bazan bawa mayen mata irinka ba, zaka iya zaba a dangin Dad dina kila in iya baka".....
Deen ya fada with a very serious face....
"Hmmm maida wukar ni banaso ma, dan wannan danake gayamaka ko a familyn ku bazaa samu ba,I'm telling you".....
Duka Deen ya kai masa yana fadin;
"Karya kake wallahi! Ni tashi muje inga wacce ake zuzutawan nan"....
Dariya sam yayi yana mika masa irin exact kayan dake jin guy din da suka zo dashi, musamman ya siyo guda biyu daya na guy din daya na Deen, dan yasan baze yarda yasa kayan da wani yasa ba....
Karban kayan yayi ya shiga toilet, fitowa yayi bayan yayi changing sannan ya mikawa guy din kayansa shima ya shiga ya chanja ya fito....
Mask din dake fuskar guy din Deen ya karba yasa shi kuma suka basa me irin fuskar Deen yasa,sannan suka masa bayani sosai akan duk wani abu dazeyi ta yanda bazaa gane ba Deen bane ba, gyada kai yayi yana assuring dinsu daze kiyaye komai......
Fita Sameer da Deen sukayi daga prison din hankali kwance dan ba wanda ze kallesu yace Deen ne dan mask din was so perfect kamar real face....
Driving Sameer yake cikin nishadi yanajin kamar bukatarsa ta biya ta gama tinda gashi ga Deen a kusa....
Wani dan tinani ne ya fadowa Deen, ya kalli sameer da sauri yace;
"Ya akayi suka barku kuka shigo?"....
"Wallahi kin yarda sukayi saida na kira mami?"...
"Ka kira wa??"....
Deen ya tambaya yana gyara zama.......
Daga kai Sameer yayi yana cigaba da driving dinsa yace;
"Yeah, karka damu bazata gane ba, na riga na mata wayo"....
Girgiza kai Deen yayi yace;
"You must be joking man! Mamin zakayiwa wayo? Duk yanda kake ganin I'm smart dinnan sai mami ta siyar dani bansani ba wallahi, to make the matter worse Umm na nan? Kasan wayan mutanennan kuwa? Ka riga ka kwapsa daka kirata, you could have used another way! Yanzu dole muyi abinda zamuyi in dawo a yau, if not you're also in soup a gurin mami dan tasan da hadin bakinka!".....
"No man!, sam bata fahimci komai ba believe me, kasan fa akwai mutunci sosai tsakanina da mami, idan kana tinanin zata gane meyasa ka kawo idea din da?"......
Sameer ya fada cike da gwarin gwiwa....
"Kadauka zata nuna maka tagane ne? And let me make this clear to you duk mutuncin dake tsakaninku if you mess up with her she'll deal with you without second thought, bakasan halin judges dinnan bane, yes nasan zata iya ganewa idan na gudu but my plan is kar abun ya shafeka tinda tana maka kallon good boy".....
"To yanzu ya zaayi gashi munriga mun fito"...
"The solution is muje muyi abinda zamuyi na dawo a yau dinnan, luckily enough they're not coming today dan da zasu zo da tini sun zo"....
"Yanda kace haka zaayi boss ko......"
Sameer be karasa ba yaji wayarsa na ringing, Ganin me kiran ya sashi cema Deen;
"P man nefa ke kira, me zanyiwa mutumin nan yake kirana at this time"....
"Toh ka dauka mana sai call din ya katse?"....
Cewar Deen kamar na Allah, shi haka yake baya yarda abokanansa suyiwa iyayensu rashin da'a a gabansa bayan shi tsula tashi tsiyar yake....
Daukan wayar sameer yayi ya karawa a kunne.....
Shiru yayi jin mahaifinsa nata zazzaga masa masifa daga bisani kuma ya yanke wayar......
Cire wayar yayi daga kunnensa yana fadin;
"Wai gsky mutuminnan ya cika masifa, wai dan nazo abuja fa yaketa wannan fadan bansan munafukin daya gayamasa ba, yanzu gashi yace na samesa a guest house dinsa now".....
"Tabb ya shigo gari kenan, sai kaje ka samesa ai"
Cewar Deen yana chanja musu waka...
Cikin rashin amincewa sameer yace;
"Inje in samesa fa kace? A wannan limited time din?"....
"To ya zakayi bayan kasan halin Dad dinka? Ka godewa Allah ba kano yace ka tawo ba, kawai kaje ya ganka saika dawo, we have atleast five hours, so we can get everything done".....
"Yes hakane kuma fah, abinda ya kamata ayi kenan, gashi muna kusa da guest house dinsa, kawai kai ka karasa gidan ni sai na hau bolt naje gurinsa".....
"Ok no prob, karka damu I'll get everything set kafin ka dawo, I'll make all arrangements, har mallamin daze daura muku auren zan dauko, kana zuwa sai ayi"......
Hannu sameer ya basa sukayi shaking yana fadin;
"Thank you buddy"...
Sannan ya fita daga motar...
Deen daya koma driver seat yana shirin jan motar sameer ya dawo, kallonsa yayi alamun how far?...
"Forgot to tell you room din datake shine na dawo in fadamaka".....
Cewar sameer dake kan app dinsa na bolt yana kokarin ordering ride.....
"No need, meye hadina da ita da zaka wani fadamin inda take? In kazo kawai saika fito da ita"..
Bejira abinda sameer zece ba yaja motar a guje ya bar gurin.....

WACECE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)Where stories live. Discover now