Chapter 4

14.5K 1.3K 62
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SOORAJ*

*Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*

_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

*WATTPAD*
@fatymasardauna


*CHAPTER 4*

Tunda ya zauna ya tallafe kansa da duka hannayensa biyu baisake wani ƙwaƙƙwaran motsiba, numfashi kawai yake fitarwa a hankali..

Mas'oud dake tsaye akansa tuntuni yasanya hanu ya dafa kafaɗansa.

Jin sauƙar hanu akan kafaɗansa ya tabbatar masa da cewa Mas'oud ne, ɗago kansa yayi ya kalli Mas'oud da rinannun idonsa.

Yanayin yanda Mas'oud yaga cikin idanun SOORAJ saida ya tsorita, saboda bai taɓa ganin abokinnasa acikin matsananciyar damuwa irin wannan ba. Zagayowa yayi ya zauna akusa da SOORAJ ɗin. Cike da kulawa yace.
"Basai na tambayeka ba RAJ nasan kana cikin damuwa, amma kuma bantaɓa ganinka acikin irin wannan yanayin ba, ina fata dai ba halinnaka kasake gwadawa ba?"

Sauƙe hannayensa dake kansa yayi ƙasa, haɗe da furzar da wani irin iska mai zafi daga bakinsa, kallon Mas'oud ɗin yayi kamar zaice dashi wani abu saikuma ya fasa, kawai ya kawar da kansa gefe.

Murmushi Mas'oud yayi tare da girgiza kansa, tun suna ƙanana suke tare shida SOORAJ saboda haka kusan gaba ɗaya halayyar SOORAJ ɗin Mas'oud yasani, idan SOORAJ bayason yin magana, akwai wani irin kallo dayakeyi, dazaran Mas'oud yaga SOORAJ yayi irin wannan kallon, to yasan mene kallon ke nufi.

"Bazan tilastaka kacemin wani abuba RAJ amma kuma kada kamanta cewa nidakai tamkar ƴan uwan juna ne, har sai yaushene zaka tsaya kana ɓoye damuwarka? yanada kyau ko bazaka faɗa duniya tasani ba, muda muke tare dakai, muncancanci musan damuwarka, amma maiyasa ako da yaushe kake ware kanka? idan har bazaka iya faɗamin damuwarka ba RAJ banda wani amfani awajenka, haka tarayyata dakaima bata da wani amfani!" Mas'oud yafaɗi haka cikin ƙunan zuciya, saboda shi kansa al'amarin SOORAJ yasoma basa haushi, koda yaushe SOORAJ acikin damuwa yake, abune mawuyaci kaga dariyan SOORAJ, gaba ɗaya yasamo wani banzan hali ya arawa kansa, baida aiki sai zaman ƙunci.

Kallon takaici Mas'oud yashiga bin SOORAJ ɗindashi, ganin ko alamar ɗaukar maganarsa baiyi ba, azuciye yatashi zaibar wajen. Riƙo hanunsa SOORAJ yayi, cikin wata irin murya mai sanyi yace.

"Bazan iyaba Mas'oud, niba namiji bane dazai iya riƙe mace, itama Nasaketa!"

Idanu Mas'oud yazaro waje cike da mamakin jin kalaman dake fita abakin SOORAJ ɗin.

"Kasaketa fa kace?" Mas'oud yatambaya cike da mamaki.

Kai kawai SOORAJ ya kaɗa masa alamar "Eh"

Wani irin tuƙuƙin baƙinciki da takaicin SOORAJ ɗinne suka turnuƙe Mas'oud, yanzu kam ya yarda cewa akwai matsala a ƙwaƙwalwar SOORAJ domin maihankali bazai aikata irin abun da SOORAJ ke aikatawa ba.

"Anya kuwa kana cikin hankalinka RAJ? kodai asiri akayi maka ne? shin kakuwa san abunda kake aikatawa? kasaketafa itama kace? mata huɗu fa kenan yanzu ana aurama kana sakinsu, daga ankai maka mace yau washe gari kake sakota, wai kodai aljanune dakai ??" Mas'oud yatambayesa cike da tsananin mamaki, saboda duk wani maihankali dole ya tsoraci lamarin SOORAJ.

Kallon Mas'oud ɗin SOORAJ yayi da jajayen idanunsa, araunane yace "Inada hankali Mas'oud kamar yanda kaima kake dashi, abu ɗaya kawai nasani shine wannan itace ƘADDARATA!" yana kaiwa ƙarshen zancennasa ya miƙe tsaye tare da soma tattara kayan training ɗinsa, Mas'oud na kallonsa ya tattara komai nasa yafice daga cikin ɗakin training ɗin. Mas'oud kam kasa tashi yayi yazauna daɓas, sosai al'ajabi da kuma mamakin abokinnasa RAJ ke ƙara kamasa, shikam yanzu yayarda cewa aljana ce tashafi Abokinnasa.

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now