Chapter 35

12.8K 1.2K 214
                                    


              *SOORAJ!!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

              *WATTPAD*
           fatymasarduna
#romance

              *Chapter 35*

Sunkuyar da kansa ƙasa yayi tare da ɗan ciza laɓɓansa, idanunsa ya mayar kan wayansa,  samun kansa yayi da kasa cigaba da amfani da wayan, ji yayi gaba ɗaya jikinsa yayi weak.

"SOORAJ!" Oummu taƙira sunansa.

Ɗago kansa yayi ya kalleta batare daya amsa mata ba, itama bata nemi amsawar nashi ba taci gaba da cewa  "Kaji abun da muka tattauna akai, amma bakace komaiba, sannan kuma inaso na yaba maka game da namijin ƙoƙarin taimakon da kayiwa Zieyaderh, insha Allah, Allah Zai baka lada!" Oummu tafaɗi maganar tana murmushi.

Ko Uhumm  baice ba, sai ma kallon Oummu'n daya keyi, ganin damuwarta dana Almustapha zasu kasheshi yasanyashi tashi gaba ɗaya yabar musu gidan.

Kwance take luf akan bed ɗinta, biscuit ne ahannunta tanaci da kaɗan kaɗan, turo ƙofar ɗakin da akayi ya sanyata tashi zaune da sauri,   ganin Oummu yasanya tasakin murmushi tare da cewa       "Barka da shigowa Oummu"

Murmushi Oummu tayi tare da zama akan wata kujera,   cike da kulawa tace.  "Magana nazo muyi dake Zieyaderh!"

Gaban Zieyaderh ne ya faɗi, amma saita dake tare da cewa "To"

Murmushi Oummu tayi tare da dafa kafaɗun Zieyaderh'n tace  "Inaso kishirya ƙarshen wannan week ɗin zamuje ƙauyenku dan inason naga mahaifinki!"

Dummm haka ƙirjin Zieyaderh ya bada wani irin sauti,  hawaye ne suka cika idanunta alokaci guda,  bakinta na rawa tace "To!"
Murmushi Oummu tayi don tafahimci cewa tsoron zuwa ƙauyen Zieyaderh keyi, cikin son kwantar mata da hankali tace "Kar kisanya tsoro aranki idan munje bazan barki ahannunsu ba zandawo dake nan, kawai dai naga ya kamata ace mahaifanki susan inda kike ne!"

Ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauƙe tare da gyaɗa kanta kawai, alaman ta gamsu.   Oummu na fita daga ɗakin. Zieyaderh ta fashe da kuka, sosai tayi kewar babanta, ko awani hali yake ciki Allah masani?  duk da cewa bai nuna mata ƙauna ba, amma ita har gobe, akwai ƙaunarsa acikin jininta, saboda koba komai Uba Uba ne koda baikasance na gari ba.

MONDAY

Cikin yanayi naɗan sauri sauri yake tafiya, don 8 daidai jirginsu zai ɗaga zuwa garin Lagos.  Sanye yake da black and white suit wanda suka matuƙar yi masa kyau, black cover shoe ne ƙiran kamfanin Gucci sanye aƙafansa me tsadan gaske. ƙamshi kawai yaketa zubawa, yayinda gashin kansa keta shinning na mayukan da aka shafa masa,  yau kam masha Allah Yayi kyau har ya gaji da haɗuwa. 

Manta biology text book  ɗinta da tayi, yasanya ta taho cikin sauri don komawa ta ɗauka, sam bata kulaba saiji tayi sunyi karo da juna,  wanda hakan yajawo zubewan documents ɗin dake  hannunsa.  Da sauri taja da baya ƙirjinta na bugu da ƙarfi, idanunsu ne suka faɗa cikin na juna, hakan yasanya taji tamkar an jona mata shocking,      kallonta yayi sannan ya kalli ƙasa inda documents ɗinsa suka zube,  da sauri ta durƙusa ƙasa hannunta har rawa yake wajen harhaɗa documents ɗin waje ɗaya.    Agogon hannunsa ya kalla yaga 7:30 kuma sai ya biya ta office kafun ya wuce airport, gashi duk gani yake kamar bata sauri wajen tattara documents ɗin.  Itakuwa bakomai ke cinta ba face tsoro hakan yasa gaba ɗaya bata sauri, ƙamshin mayen turarensa dake zautar da ita ne, ya daki hancinta sosai, hakan yasa ta ɗan ɗago da kanta, daidai lokacin shi kuma ya ɗan ranƙwafo don tattare documents ɗin, kanta ne ya bugi haɓanshi wanda hakan yasashi rumtse ido, ahankali yace "Auchhhh!!"  dan ya ɗanji zafi sosai.
Sakin documents ɗin tayi tare da sanya hannuwanta ta rufe bakinta, wani sabon tsoro ne  yasake kamata, baki na rawa tace "Kayi haƙuri Wallahi bansaniba ne!!"

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now