Chapter 6

12.4K 1.3K 44
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SOORAJ*

*Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*

_{United we stand ans succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

*WATTPAD*
@fatymasardauna

*CHAPTER 6*

Tunda ya kwanta bacci bashi ya tashi ba sai da aka soma ƙiraye ƙirayen sallan Azahar. Toilet yashiga yayo wanka. Still riga da wando na jeans yasanya ajikinsa. Masallacin dake kusa da gidansa ya nufa donyin sallah. Tun da yafita yin sallah baidawo ba sai ƙarfe huɗu na yamma, wanka yasakeyi. Combat jeans ne ajikinsa baƙi sai kuma wata farar riga mai ɓaƙaƙen aninaye. Yana tsaye agaban dressing mirror yana taje tulin sumar kansa, wanda yasha aski irin na zamani, screen ɗin wayarsa ya soma kawo haske, ɗan matsawa kusa da yawartasa yayi. Sunan Mas'oud ne ke yawo akan screen ɗin wayar, kasancewar ya sata a silent shiyasa batayi ƙara ba, ɗan ɓata fuska yayi haɗe da ɗaukan wayar yakara akan kunnensa.

"Ina falo" Inji cewar Mas'oud.

"Okay" kawai Sooraj yafaɗa akasalance tare da aje wayartasa, bai fita falon ba yaci gaba da taje sumar kanshi, saida ya kammala duk wani abu dazaiyi kana ya ɗauki wayarsa dakuma car key ɗinsa yafita zuwa falo.

Cike da takaici Mas'oud ke kallonsa, duk da yasan cewa halin Sooraj ne shanya mutane, amma kuma abun da yayi masa yauɗin yayi masa ciwo.

"Inakuma zakaje?" Mas'oud yatambayesa yana me ƙare masa kallo.

"Asibiti"
SOORAJ yabashi amsa ataƙaice.

"Abiti kuma? Baka da lafiya ne?" Mas'oud yajero masa duk waƴannan tambayoyin alokaci guda.

Ɗan ya mutsa fuska yayi haɗe da sanya hanu ya shafi kwantaccen sajen dake shumfuɗe akan fuskarsa.
"Accident mukayi, zanje na duba yarinyar dana bugene kota farfaɗo" ya faɗi haka yana me nufar hanyar fita daga falon, kai kawai Mas'oud ya girgiza haɗe da miƙewa tsaye yabi bayan SOORAJ ɗin. SOORAJ ne ke tuƙa motar yayinda Mas'oud ke zaune agefen mai zaman banza. Tafiya suke babu wani wanda yace da ɗan uwansa wani abu, ahaka har suka kawo asibitin, sam Mas'oud baiwani damu da shirun da SOORAJ ɗin yayi ba, because yasan hakan halinsa ne, bakoda yaushe yacika yawan magana ba, amma idan kafahimcesa yana da daɗin zama, dan bayashiga abun da babu ruwansa...

Atare suka jera suka shiga cikin asibitin. Office ɗin Dr.Salees suka nufa, shiyayi musu jagora zuwa ɗakin... dama yana shirin zuwa dubata kenan suka shigo.

Tananan har yanzu bata farfaɗo ba, wasu allurai Dr.Salees yayi mata, juyawa yayi ya kalli SOORAJ dake zaune akan wata plastic chair.... "Zata iya farfaɗowa akowani lokaci da yardan Allah, Yana da kyau katsaya atare da ita." Inji cewar Dr.Salees.

Kai kawai ya iya jinjina wa Dr.Salees alaman yaji, fita Dr.Salees yayi daga cikin ɗakin.

Kallon Mas'oud daya kafe yarinyar da idanu SOORAJ yayi, tsayawa yayi yana kallon yanda idanun Mas'oud ke yawo ajikin yarinyar ko ƙyaftawa ba yayi, takaicin Mas'oud ɗinne yakamashi, sam shi kam baiga wata mace aduniya dazai tsaya ɓata lokacinsa wajen kallonta ba, yaga manyan mata da suka amsa sunansu mata baiji komai gamedasu ba balle wannan ta tsitsiyar yarinyar, inbanda ƙaddara ma maizai haɗashi da ita, sam shi baya shiga sha'anin mata, saboda yasan menene matsalarsa, wannan ma don dolene kawai, amma dazaran ta farfaɗo zaisa amaidata inda ya ɗaukota.

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now