Chapter 12

11.8K 967 43
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SOORAJ !!!*

*Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*

*WATTPAD*
@fatymasardauna

*Chapter 12*

Arazane ta tashi daga zaunen da take haɗe da waro manya manyan idanunta. Lokaci guda jikinta ya ɗauki rawa, ƙafafunta na rawa haka ta nufi inda yake a yashe baya numfashi.

Hanunta dake rawa ta ɗaga haɗe da kaiwa kan fuskarsa, hanunta tasa adai dai saitin hancinsa, saidai bataji abun da takeson jiba, wato numfashi.

Tsorone yasake kamata, hanunta ta ɗaura akan kafaɗunsa ta shiga jijjigasa, cikin wata irin murya mai ɗauke da tsantsar tsoro haɗe da ruɗewa tace. "Katashi ka buɗe idanunka Don Allah!" wasu hawaye masu zafi ne suka soma sulalowa daga cikin idanunta suna sauƙa akan fuskarta. Ganin jijjigashi da takeyi bazai kawo mata wata mafita ba, yasa aguje ta fice daga cikin falon, wajen mutumin dake zaune a bakin tankamemen gate ɗin gidan ta nufa. Yanayin yanda yaganta abirkice har yaso yaɗan tsoratashi. Kafun yace wani abu ta rigashi cikin haki tasoma cewa.... "Baya numfashi kataimakeni kada ya mutu!"

Zaro idanunsa waje Sammani mai gadi yayi cike da tsoro. Yana ƙoƙarin tambayarta meke faruwa, yaga ta sake rugawa aguje ta koma ciki. Cikin hanzari shima ya rufa mata baya.

Sake zube guiwowinta tayi a ƙasa haɗe da cigaba da jijjigashi, Dai dai lokacin Sammani mai gadi ya shigo, ganin Ogan sa kwance aƙasa baya motsi yasanyashi ƙarasowa cikin falon da sauri har yana jin tuntuɓe.

"Meke faruwa mekikayi masa?" Sammani dake a ruɗe ya tambayi Ziyada wacce gaba ɗaya hawaye sun gama wanke mata fuska.

Cikin tsoro tashiga girgiza kanta cikin sarƙewar murya tace.

"Wallahi banyi masa komai ba, bani bace, kawai nima gani nayi ya faɗi, Allah banyi masa komai ba!" Taƙare maganar tana mai fashewa da wani irin kuka mai sauti.

Da gudu Sammani yafita daga cikin falon, Kamalu driver yaje ya ƙira suka dawo falon a tare, hankalinsu amatuƙar tashe.

Da ƙƴar Kamalu driver da Sammani suka iya ɗaga Sooraj suka yi waje dashi, ganin haka yasa itama ta rufa musu baya, mota Kamalu ya buɗe suka sanyashi agidan baya.

"Kajira gidan, mu zamu kaishi asibiti" Kamalu driver yace da Sammani mai gadi. Kallon Ziyada da har yanzu idanunta ke fitar da ƙwalla yayi. "Muje" yace da ita yana mai buɗe mata murfin motar, da saurinta ta faɗa cikin motar shima Kamalun yashiga. Sammani ya buɗe musu gate suka fice daga cikin gidan, gudu sosai Kamalu keyi hakan yasa basu wani jima ba suka isa asibitin da yasan Sooraj ɗin nazuwa.

Da taimakon wasu likitoti aka ɗaura Sooraj akan wani gado mai ƙafafun taya, sannan aka gungurasa zuwa Emergency Room..

Kai Ziyada ta cusa acikin cinyoyinta, haɗe da sakin wani sabon kuka, addu'a take aranta Allah Yasa ba mutuwa yayi ba, hakanan takejinsa acikin wani ɓangare na jikinta, ko ba komai yayi mata hallacci, ya killace rayuwarta daga gurɓacewa, bazata taɓa son wani abu ya sameshi ba.

A Emergency Room kuwa sosai likitoti suka duƙufa akansa wajen basa taimakon gaggawa, da ƙyar suka samu suka shawo kan al'amuran, alokacin da suka gano matsalar kuwa baƙaramin mamaki sukayi ba, domin sun gano cewa allura akai masa ko yayiwa kansa, wacce take da mugun haɗari sannan tana da ƙarfin gaske, aƙalla idan a kayiwa mutum ita zai iya kaiwa sati ɗaya batare daya san inda hankalinsa yake ba, koda kuwa ya farfaɗo ba zai dawo cikin hayyacinsa da wuri ba, sai dai ma shi Sooraj ɗin yaci sa'a jininsa na da ƙarfi sosai, amma duk da haka ƙarfin alluran yayi tasiri acikin jikinsa. Drip suka ɗaura masa sannan suka wuce dashi wani ɗaki na musamman, kasancewar kusan duka likitotin asibitin sun sansa, don yana zuwa lokaci zuwa lokaci yana dubawa koda akwai waƴanda suke da buƙatar taimako shi yakan zuba dukiyarsa ya taimaka musu.

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now