Chapter 34

11.3K 1K 155
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

              *SOORAJ!!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

            *WATTPAD*
        @fatymasardauna

#romance

                *Chapter 34*

A hankali idanunta ke lumshewa da alama bacci takeji, amma kuma har izuwa wannan lokacin bata daina hura masa iskan dake bakinta ba.   Ahankali yake  fitar da numfashi, yana mejin sanyi na sauƙa acikin zuciyarsa, juyo da kansa ɓangaren da take yayi  tare da sauƙe gajiyayyun idanunsa akanta,   itama ɗago manya manyan idanunta tayi ta kalleshi, hakan yabawa idanunsu daman sarƙewa acikin na juna,  wani irin mimmiƙewa gashin dake jikinta sukayi, take tsikar jikinta ya shiga zubawa, tamkar wacce aka watsawa ruwan sanyi,  ba komai ya haifar mata da hakan ba kuwa, face arba da sexy eye balls ɗinsa da tayi,  wanda suke lumshewa ahankali tamkar na mejin bacci.  ƙasa tayi da idanunta, batare da ta sake hannunsa dake cikin nata ba,  ƙofar ɗakin aka buɗe hakan yasa ta ɗago kanta da sauri ta kalli ƙofan, Almustapha ne ya shigo bakinsa ɗauke da sallama,  da sauri tatashi daga zaunen da take tare da sakin hannunsa ta koma gefe.   Ƙarasowa cikin ɗakin Almustapha yayi yana me ƙare mata kallo, cikin muryarsa me sanyi yace.  "Ya tashi ne?"

Kai kawai ta iya gyaɗa masa alamar "Eh" Raɓawa tayi tagefenshi ta fice daga cikin ɗakin.    Binta yayi da kallo harta fice, ajiyar zuciya ya sauƙe tare da juyowa ya kalli Sooraj wanda ko motsawa baiyi ba.

"RAJ" Almustapha yaƙira sunanshi.

"Ummm!" Sooraj ya amsa masa akasalance yana meƙoƙarin tashi zaune.

Kallonsa Almustapha yayi sosai sai kawai yayi murmushi tare da cewa.   "Ya jikin naka?"

"Wani yace maka banida lafiya ne?" Sooraj ya faɗa yana me ƙoƙarin sauƙa daga kan gadon.

"No ni ne kawai nake tunanin baka da lafiya, ko dai mutanen naka ne suka motsa?" Almustapha ya tambaya yana me ƙoƙarin gimtse dariyan dake bakinsa.

Hararansa Sooraj yayi baice dashi komai ba ya nufi hanyar da zai sadashi da bathroom, sarai  yasan iskancin Almustapha yawane dashi, yanzu idan ya tsaya yadinga ɓata ransa kenan.

Dariya Almustapha yayi tare da jawo laptop ɗin Sooraj ɗin yashiga amfani dashi.

Luf tayi akan gado tana me sauƙe ajiyar zuciya akai akai,  ƙwayan idanunsa ne keta yiwa nata idanun gizo,  lumshe idanunta tayi tare da sakeyin hugging pillow'n dake hannunta,  hancinta takai kan hannunta wanda tariƙeshi dashi, sosai hannunnata ke ƙamshinsa, wani irin kasalane taji yana sauƙa mata,  tabbas ayanzu tayarda da cewa shiɗin na musammanne, kamar yanda komai da ya shafesa yake na musamman. 

Tari yake sosai acikin toilet ɗin, wanda har hakan yaɗauki hankalin Almustapha dake zaune akan gado,  ɗan tsayawa yayi ajikin ƙofar toilet ɗin,  tare da cewa  "RAJ are you Okay?"  shiru baiji ya amsa masa ba, hakan yasa ya tura ƙofar bathroom ɗin,  da sauri ya ƙarasa wajen Sooraj dake tsaye agaban sink yana goge bakinsa da tissue. 

Idanu Almustapha ya zaro tare da duban tissue ɗin dake hannun Sooraj hankalinsa amatuƙar tashe yace
"RAJ jinin mene wannan?"

Hararansa Sooraj yayi cike da ƙosawa yace
"Amma dai ban gayyatoka ba ko?"

Fuskar Almustapha babu alaman wasa ko tsokana yasake cewa. "RAJ jinin menene wannan? please tell me dama baka da lafiya sosai har haka ne?" Gaba ɗaya Almustapha ya ɗaga hankalinsa.

"Bakina ne ya fashe!" Sooraj yafaɗa ataƙaice yana me sanya ruwa ya shiga wanke bakinsa. 

Kamar statue haka Almustapha ya tsaya yana kallon Sooraj, sam bai yarda da cewa wai bakinsa ne ya fashe ba, cikin yanayi me ɗauke da tsananin damuwa yace

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now