Chapter 9

12K 1.5K 45
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SOORAJ !!!*

*Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*WATTPAD*
@fatymasardauna

*(Banso cigaba da rubutunnan ba amma yazanyi daku😥 My Wattpadians sun sakoni gaba, waƴand sukace aci gaba sunfi waƴanda sukace a dakata yawa... Nagode da nunawa littafina ƙauna. Inayinku hundred percent My Wattpadians Allah yabar Ƙauna!!)*

*Chapter 9*

Sake lumshe gajiyayyun idanunsa yayi, aransa yanaso yaje yasanar da mahaifiyarsa matsalan dake damunsa, saidai kuma sosai wata zuciyar ke gaya masa hakan badai dai bane. Jikinsa asanyaye ya nufi wajen da yayi parking motarsa.
***
Bacci tasha sosai ba ita tafarka ba sai lokacin da aketa ƙiraye ƙirayen sallan la'asar. Banɗaki tashiga ta ɗauro alwala, kan lallausan carpet ɗin dake malale a gefen gadon ta hau haɗe da tada Sallah, bayan ta idar da sallan ta zauna jigum haɗe da sanya hannayenta ta tallafi kyakkyawar fuskarta. Jitayi ruwan hawaye sun cika idanunta, tausayin kanta take, musamman ma yanzu da take cikin rayuwa irin ta BULAYI.
***
Kallon Mamaki Mas'oud ke yiwa SOORAJ, da ƙyar ya iya cewa. "Me hakan yake nufi kenan SOORAJ? kakuwa san illan abun da kake shirin aikatawa? ajiye mace'n da ba muharramanka ba acikin gidan ka fa abune da baidaceba sannan kuma hatsarine babba"

Murmushin gefen baki SOORAJ yayi, haɗe da ɗaukan cup ɗin fresh milk ɗin dake aje agabansa yaɗanyi sipping kaɗan, miƙewa tsaye yayi tare da kai dubansa ga agogon dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa.

"Ni zan wuce" yace da Mas'oud ataƙaice.

Kallonsa kawai Mas'oud yayi haɗe da girgiza kansa.
"Nasani dama SOORAJ ba zaka taɓa sanjawa ba" Mas'oud yafaɗi haka acikin zuciyarsa. SOORAJ baisake bi takan Mas'oud ba yanufi wajen da motarsa take.

Yana shiga cikin motar ya murza mata key haɗe da cillata kan titi. Direct babban asibitin dake cikin Garin Kaduna ya nufa.

Ajiyar zuciya mai ƙarfi Dr.Waleey yayi haɗe da gyara zamansa, kallon SOORAJ yayi cike da tausayawa.... "Ka kwantar da hankalinka SOORAJ, akwai wani sabon magani idan na ɗauraka akai wata ƙila adace"

Kallon Dr.Waleey Sooraj yayi da shanyayyun idanunsa.

"Banatunanin akwai wani maganin da zan ƙarasha Dr.Waleey, zan haƙura kawai, zamana ahaka wata ƙila shine abu mafi alkhairi!" yafaɗi maganar cike da raunin zuciya.

"Karkace Haka SOORAJ, kada ka karaya, sauƙi zai iya samuwa ako da yaushe, kasan Allah Babu yanda baya ikonsa, amma nikaina al'amarinka yana matuƙar girgizani, nasha samun case ire iren wannan, amma naka yayi worse." Ɗan tsagaitawa daga maganan Dr.Waleey yayi, haɗe da sauƙe ajiyar zuciya, cigaba yayi da cewa.
"Kada kadamu Sooraj Insha Allah watarana sai labari." ya ƙare maganar cike da son ƙarfafawa Sooraj guiwa.

Murmushi Sooraj yayi haɗe da cije lips ɗinsa, jin Dr.Waleey kawai yake, amma ji yake ajikinsa kamar shikam ahaka zai mutu, ahaka zai ƙare rayuwarsa babu wata ingantacciyar farinciki.
Sunan wasu magunguna Dr.Waleey ya rubutawa Sooraj a ƴar wata farar takarda. Hanu Sooraj yabasa sukayi musabaha, kafun ya fice daga cikin office ɗin.

Direct Pharmacy yaje yasaya maganin, sannan yabar cikin asibitin.
***
Idar da salla'n isha ɗinta kenan ta zauna akan gado, haɗe da kama cikinta daketa yi mata kukan yunwa, gawani tsoro daya lulluɓeta, ayanda tafahimta shine ita kaɗaice ke rayuwa acikin gidan, domin kuwa tunda ta zauna bataji motsin kowa ba. Sam bata saba irin wannan zamanba, tasaba gaba ɗaya rayuwarta cikin aiki take, sam bata da hutu, yi wancan ɗauko wancan, da haka ta saba, shiyasa gaba ɗaya takejinta amatuƙar takure.

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now