Chapter 42

11.3K 1K 83
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SOORAJ !!!*

*Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*WATTPAD*
@fatymasardauna
#romance

*Chapter 42*

Tana shiga cikin ɗakin tasoma rage kayan dake jikinta, wani mini pink towel ta ɗaura kana ta wuce bathroom, cikin nutsuwa tayi wanka tare da ɗauro alwala. Kasancewar yanayin na yau ana ɗan zafi yasanya komai bata shafa ba ta zura wata jallabiya irin ta mata wacce take da adon duwatsu haɗi da zanen beuty's followers agabanta, sosai rigan ta amshi jikinta kasancewar rigan nada kalan ja hakan yasa taƙara bayyana hasken fatarta, ɗan ƙaramin trolly ɗinta tajawo, sif ɗin kayanta ta buɗe ahankali tashiga ɗiban kayan tana zubawa acikin trolly ɗin, wani irin tunanine ke yawo aƙasan zuciyarta, hakanan taji batason barin gidan, duk da kasancewar acikin ƴan kwanin bata ko ganinsa bare jin labarinsa, wani irin kewane ke cinta azuciya, tanaso taji wannan daddaɗan ƙamshin nasa mai ratsa zuciya, tanaso taga koda gilmawansa ne, da tunani iri iri acikin ranta haka ta kammala haɗa ƴan kayanta wanda tasan zata buƙata, gyalen jallabiyan ta yafa akai zuwa jikinta kasancewar yana da ɗan girma, ahankali take sauƙowa daga kan step hannunta riƙe da trolly da kuma school bag ɗinta dake rataye akan kafaɗunta.

Oummu naganinta tace.
"Yauwa kin kimtsa ko, kici abinci sai ku wuce" da "To" kawai ta amsa kana ta aje jakakkunan nata ta nufi dinning area, ɗaya daga cikin kujerun wajen taja ta zauna tare da ɗaukan plate tayi serving kanta, ahankali take tsakuran abincin tana kaiwa bakinta, sam batajin test akan harshenta, sama sama take jiyo hiran Oummu da Aunty Muhibbat inda duk maganan tasu akan auren nata ne sukeyi, itakam har yanzu ganin abubuwa take kamar al'amara, don bata taɓa ganin aure irinnata ba, sam ta rasa awani matsaya take, don ita kanta takasa gane kanta, ahankali take ɗiban abinci acikin spoon tana kaiwa bakinta, wani irin baƙon ƙamshin turaren daya shigo hancinta ne yasanyata ɗago kanta takalli cikin falon, idanunta ne suka sauƙa akan sa wanda shigowarsa cikin falon kenan shiɗinma kuma kallonta yakeyi, tarine ya sarƙeta yayinda abincin da takeci ya shaƙe maƙoshinta, da sauri ya ƙaraso kan dinning ɗin tare da ɗaukan bottle water, ɓalle murfin yayi kana ya miƙo mata, da sauri ta amsa takai bakinta, saida tasha har kusan rabin goran sannan ta ajiye tare da sunkuyar da kanta ƙasa ahankali take maida numfashi don har idanunta saida suka sauya kala sukayi ja.
"Are you okay?" Almustapha wanda yasha ado cikin jan shadda ya tambayeta.
Kanta ta kaɗa masa alaman "Eh"
Murmushi yayi tare da ɗan ranƙwafowa gaf da ita cikin yin ƙasa da murya yace "Ehem ƴan mata kin ruɗe ne saboda kinga nayi miki kyau ko?"
Da sauri ta ɗago kanta ta kalleshi fuskarta ɗauke da mamakin jin maganarsa. Idanunsa ɗaya ya kashe mata tare da zura hannayensa cikin aljihun wandonsa, haɗa idanu da suka sakeyi yasanya ta murguɗa masa baki, murmushine ya suɓuce masa tare da ɗan zaro idanunsa, ƙasa ƙasa yace "Ni kika murguɗawa baki ko, watarana zaki murguɗawa wanda zai cire bakin gaba ɗaya" yafaɗi haka yana me ƙoƙarin komawa cikin falon, bayansa tabi da kallo harya ƙarasa kusa da Oummu ya zauna, miƙewa tayi itama tare da ƙarasowa cikin falon, dubanta Oummu tayi cikin kulawa tace "Harkin kammala?" murmushi tayi tare da ɗaga kanta alaman "Eh"
Miƙewa Aunty Muhibbat tayi tare da ɗaukan mayafinta cikin kulawa ta dubi Almustapha tare da cewa "Muje ka sauƙe mu ko!"
Trolly ɗinta ta ɗauka tare da kallon Oummu, itama Oummun kallonta takeyi murmushi tayi mata tare da cewa.
"Ki kwantar da hankalinki nima gobe zanzo insha Allah!"
asanyaye ta gyaɗa kanta alaman to.
Almustapha ne ya fara yin gaba, sai Aunty Muhibbat yayinda tarufa musu baya, har jikin motar Almustapha Oummu ta rakosu, inda Aunty Muhibbat tabuɗe gidan baya ta shiga, hakan yasa dole ta shiga gaba badon taso ba. Koda suka ɗauki hanya Almustapha da Aunty Muhibbat ne keta hiransu, ita kuwa shiru tayi tana kallon hanya.

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now