Chapter 45

15K 1.4K 215
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

           *SOORAJ !!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

             *WATTPAD*
        @fatymasardauna
#romance

             *Chapter 45*

Wani irin ƙara ta sake yayinda towel ɗin jikinta ya zame ya faɗi ƙasa,  cikin tsautsayi ƙafanta ya bugi jikin gado, suuuuu haka tatafi zata faɗi, cikin abun da baiwuce 1 second ba ya ƙaraso cikin ɗakin,  da sauri yaƙarasa tare da sanya duka hannayensa biyu ya tarota, inda ya zube ƙasa kan guiwowinsa,  cikin tsananin tsautsayin dake jansa ya sauƙe idanunsa akan naked pure white breast ɗinta, da sauri ya rumtse idanunsa yayinda lokaci guda yaji tamkar andoka masa guduma atsakiyar kansa,  gaba ɗaya jikinsa ne ya soma ɓari,
Ita kuwa Zieyaderh tamkar wata matacciya haka gaba ɗaya jikinta ya sandare, yayinda ta kulle idanunta ƙaƙam,  cikin tsananin tsoron  dake ɗawainiya da zuciyarta haɗi da fusgewar numfashi ta ɗan buɗe idanunta kaɗan, wani irin ƙara tasake  sakamakon ganin fuskarsa da tayi, cikin tsananin ruɗewa haɗi da zabura ta tashi daga jikinsa,
aruɗe ta soma ƙoƙarin neman towel ɗinta daya faɗi, don  suturce jikinta, irin yanayin ruɗewan  da tayi yasanya takasa ganin towel ɗin, wanda kuma yashe yake agabanta,  cikin hanzari ta jawo blanket ɗin dake kan gadon na Oummu ta rufe gaba ɗaya jikinta dashi,  zamewa ƙasa tayi tare da sakin wani irin marayan kuka wanda ke ɗauke da tsananin takaici da kuma haushin kanta, wata fitinanniyar kunyace gaba ɗaya ta rufeta.

Jin diran sautin  kukanta  da yayi acikin kunnuwansa,  yasanyashi miƙewa daga durƙuson dayayi, cikin dauriya dason kawar da zazzafan ciwon kan daya kawo maza cafka lokaci guda, ya juya tare da nufan hanyar barin ɗakin.
Kasancewar har yanzu  idanunsa arufe suke,  hakan yasanya sam baikula da Oummu da kuma Aunty Muhibbat dake ƙoƙarin shigowa cikin ɗakin ba,
jin cewa yayi karo da mutum ne  yasanyashi saurin buɗe idanunsa,  nan ya sauƙe su akan fuskar Oummu dake tsaye tana kallonsa,    kansa ya sunkuyar ƙasa tare da raɓawa ta gefenta zai wuce, cike da mamakin yanda idanunsa sukai jajur Oummu tace.
"Kajirani a falon ƙasa".

Kansa kawai ya jinjina  mata alaman.     "To"
Ahankali yashiga taka matattakalan da zai sadasa da falon ƙasan. 

Oummu kuwa dubanta takai ga Aunty Muhibbat,  gane abun da Oummun ke nufi yasanya Aunty Muhibbat murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin ta shiga da sauri, don ta duba Zieyaderh wacce sautin kukanta ke ratsa kunnuwansu.
Oummu kuwa juyawa tayi tare da fasa shiga ɗakin, kaitsaye tanufi matattakala don sauƙa ƙasa.

Da auri Aunty Muhibbat ta ƙaraso inda Zieyaderh'n ke zaune, yayinda ta takure  jikinta waje ɗaya acikin blanket tana kuka.
Kallon towel ɗin dake ƙasa Aunty Muhibbat tayi tare da sakin murmushi, cikin kulawa ta zauna akan gado tare da sanya hannu ta dafa kafaɗa Zieyaderh.

"Jikinne har yanzu?"  ta tambaya tana me ƙoƙarin jawota ta zaunar da ita akan gadon Oummu.

Jin muryar Aunty Muhibbat acikin kunnuwanta, yasanyata sake ɓoye kanta acikin blanket, tare da ƙara sautin kukanta.

Still murmushi Aunty Muhibbat tayi cikin rarrashi tace.
"Kukan ya isa haka, ko so kike  kanki yayi miki ciwo?  maza  tashi ki sa kayanki kinji, ko SOORAJ yayi miki wani abune?" Aunty Muhibbat ta tambaya.

Cikin sheshsheƙan kuka tagirgiza kanta alaman.
"A'a"

Murmushi Aunty Muhibbat tayi tare da cewa.
"To tashi kisa kayanki, ko so kike kowa yazo yana ganinki ba kaya?"

Cikin nutsuwa Oummu ta kai dubanta garesa, murya asanyaye ta ƙira sunanshi.
Amsa mata kawai yayi batare daya ɗago kansa ya dubeta ba.

Cikin kulawa ta gyara zamanta tare da cewa.
"Duk da wannan bashine karo na farko da muka fara yi maka aure ba, amma inaso kasancewa wannan auren daban yake da sauran,  bandamu ba koda zakaji cewa hakan da mukayi rashin kyautawa ne agareka, saidai inason kasan cewa  ban taɓajin ina yimaka sha'awar rayuwar aure da wata mace ba kamar Zieyaderh, 
kamar yanda kaine ka kawota kakuma riƙeta tunkan musan da ita, ayanzuma haka nakeso kacigaba da  riƙeta,  kai ba ƙaramin yaro bane Sooraj,  kamar yanda na gargaɗeka abaya akan sakin aure, to awannan karon ma zan gargaɗeka, Wallahi! Wallahi!! Sooraj idan har ka saki yarinyar nan Zieyaderh kamar yanda kake sakin sauran matan da muke aura ma to tabbas  saina tsinemaka!!"

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now