Chapter 46

15K 1.2K 208
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

           *SOORAJ !!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

              *WATTPAD*
        @fatymasardauna
#romance

            *Chapter 46* 

Sannu ahankali ƙiran sallan assalatu da akeyi ya ratsa cikin kunnuwansa,  ahankali ya ware manyan idanunsa, ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauƙe,  tare da ɗan cije laɓɓansa sakamakon yanda yaji ƙafafaunsa sun ƙage waje guda, hakan ya faru ne kuma saboda jimawa da sukayi anannaɗe,   ƙasa ya ɗanyi da idanunsa tare da duban fuskarta, baccinta takeyi cikin kwanciyar hankali da natsuwa, yayinda take ta faman sauƙe ajiyar zuciya akai akai,  saurin ɗauke idanunsa wanda suka sauƙa akan breast ɗinta yayi,  tare da ɗan yunƙurawa ya tashi da ita ajikinsa.
Ahankali ya shumfuɗeta akan gado,  tare da juyawa ya nufi hanyar bathroom.
Zip ɗin wandon jeans ɗin dake jikinsa ya zuge, tare da zame wandon nasa yayi ƙasa,
daidaita tsayuwarsa yayi agaban shower, tare da ɗan murɗa makunnin shower'n,  sassanyar  ruwan dake fitowa acikin shower'n ne ke dukan jikinsa, sannu ahankali yakejin wani irin sanyi na ratsa gaba ɗaya jikinsa, cikin nutsuwa yayi wanka tare da ɗauro alwala,  farar bathrobe ya sanya ajikinsa kana yafito daga cikin toilet ɗin.
Kaitsaye gaban sif ɗin kayansa ya nufa,  wani black jeans tare da white long sleeve shirt yasanya, kana ya fesa turarensa mai daɗin ƙamshi, wani ƙaton darduma ya shumfuɗa aƙasa, inda ya gabatar da sallah  raka' biyu, yana idarwa yaji ana ƙiran sallan Asuba a masallaci, shafa addu'an da yakeyi yayi tare miƙewa tsaye,  har yakai bakin ƙofar fita daga cikin ɗakin, sai kuma yaɗan tsaya tare da juyowa ya kalli inda take, haryanzu baccinta take sha cikin kwanciyar hankali,  handle ɗin ƙofar ya murɗa kana ya fice daga cikin ɗakin.  

7:30 am.
Ahankali take buɗe idanunta wanda sukai nauyi kana kuma sukai ja, sake ɗan lumshe idanun nata tayi sakamakon sihirtaccen ƙamshinsa daya samu daman kawowa hancinta ziyara, ahankali tatashi zaune daga kan gadon, ɗakin tasoma bi da kallo, kana ta sauƙe wani irin ajiyar zuciya, ahankali ta zuro da ƙafafunta ƙasa,  wanda suka sha jan lalle gwanin ban sha'awa, direct inda trolly ɗinta yake ta nufa, zuge zip ɗin jakar tayi tare da fito da wata maroon ɗin abaya gown mai kyau wanda aka ƙawata jikinta da adon ƙyalƙyali, cikin sauri ta shige toilet.
Tsayawa tayi  tana me ƙarewa haɗaɗɗen toilet ɗin kallo, komai dake cikinsa nead, sosai aka ƙawata toilet ɗin, gaba ɗaya toilet ɗin ƙamshi yake, ahankali ta ƙarasa jikin wani glass wanda aka jere kyawawan bathrobe da kuma towels acikinsu,  rigar dake hannunta ta ajiye tare da zage zip ɗin rigar,  ɗaya daga cikin towel ɗin ta ɗauko  ƙoƙarin ɗaurawa  ajikinta take,  daddaɗan ƙamshinsa mai sanya nutsuwa ne ya daki hancinta, jingina bayanta tayi da jikin bango tare da lumshe idanunta, sosai ƙamshin nasa ke kashe mata jiki,  ɗaura towel ɗin tayi ajikinta tare da ƙarasawa gaban bathtube ta haɗawa kanta ruwan wanka, cikin nutsuwa tayi wanka inda ta zura abaya gown  ajikinta,  sosai rigar tayi mata kyau ta kuma amshi jikinta, ahankali ta murɗa handle ɗin ƙofar bathroom ɗin tafito,  kaitsaye dressing mirror ta nufa, tsadaddun kayan shafansa ne suka cika gaban mirror'n, gwanin ban sha'awa,  hannunta takai ta ɗauki wani kyakkyawan kwalban turarensa dake kan mirror'n,  jujjuya kwalban turaren tayi ahannunta tare da sauƙe ajiyar zuciya,  nannaɗe dogon gashinta tayi tare da sanya ribbom tayi parking gashin  atsakiyar kanta, nan tashiga kimtsa kan gadon, duk dama nead yake bai wani ɓaci sosai ba,  saida ta gyara komai dake cikin ɗakin, kana ta wuce toilet ta wankesa  tsab,  zama tayi akan gado haɗe da jingina bayanta da jikin gadon, lumshe kyawawan idanunta tayi sannu ahankali wasu daga cikin abubuwan da suka faru atsakaninsu jiya da dare suka soma dawo mata,  tabbas Ƙaddara tayi mata sauyi, Ƙaddara ta canza duk wani tunaninta, wasu irin sanyayyun hawayene suka samu damar gangarowa daga cikin idanunta, kwanciya tayi akan gadon tare da cusa kanta cikin pillow ta saki wani irin marayan kuka,
tayaya zata fara koyawa kanta zama dashi? wani abu takeji na daban acikin rai da zuciyarta dangane dashi.

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now