Chapter 14

11.6K 959 42
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SOORAJ !!!*

*Written by*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*

*WATTPAD*
@fatymasardauna

#romance

*Chapter 14*

Basu wani jima ba suka fito daga ɗakin da akeyiwa duk wani ɗalibi da yakasance sabon zuwa interview. Direct office ɗin principal ɗin suka koma zuciyar Ziyada cike take da farinciki da kuma jin daɗi, addu'anta ɗaya Allah yasa hasashen da takeyi yazamanto gaskia.

"Har kun gama interview ɗin?" Mr. Isyaka Nuhu ya tambayi Sir. Yusuf wanda shine ke yiwa duk wani sabon ɗalibi dazai shigo makarantar interview.

"A'a Sir ai ma bata taɓa zuwa makaranta ba, inaga kawai sai dai afarayi mata lesson"
Sir.Yusuf yafaɗi haka cikin siga irinta bada shawara.

Jinjina kai Mr. Isyaka Nuhu yayi haɗe da dawo da kallonsa ga Sooraj wanda har yanzu wayarsace riƙe ahanunsa yana latsawa.

"To kaji abun da yace, ya kagani ko za'a fara yi mata lesson ɗin, idan ta ɗan soma iya wasu abubuwan sai abata ko s.s.one ne"

Sai alokacin ya ɗago kansa, wannan murmushin nasa da baya wuce kan laɓɓansa yayi haɗe da cewa.
"Bakomai hakan yayi, yaushe za'a fara lesson ɗin?"

"Ai tunda kusan munkammala komai ko yau ma idan kun shirya sai afara yi mata" Inji cewar Mr. Isyaka Nubu (Principal).

"Okay ba damuwa, ni zan wuce" Sooraj yafaɗi haka yana me miƙewa tsaye, hanu yabawa Principal ɗin sukayi musabaha, kana yabawa Sir. Yusuf ma suka gaisa, ko kallon gefen da take baiyiba ya fice daga cikin office ɗin.

Principal ne yace da Sir.Yusuf suje ya samo mata malamin lesson su fara tun yau, hakan kuwa akayi, Wani Teacher Abdallah Sir.Yusuf ya samo mata, wanda shine zaina koyar da ita lesson everyday, hatta ranan saturday da sunday zai na zuwa koya mata gida, domin biyanshi za'ana yi.

abubuwa masu sauƙi Teacher Abdallah yafara koya mata, sam babu wani abu da ta fahimta tana dai jinsane kawai, duk kuwa yanda taso ta fahimci abubuwan sam ƙwaƙwalwarta takasa ɗauka.
***
Zaune yake atamfatsetsen office ɗinsa, dagashi sai dogon wandon suit da kuma rigan parking shirt dake sanye ajikinsa, laptop ɗinsa ne agabansa yana shigar da wasu bayanai gaba ɗaya hankalinsa nakan laptop ɗin, turo ƙofar office ɗin akayi tare da shigowa, yaji motsin buɗe ƙofar amma sam baiɗago kansa ya kalli wanene ya shigo cikin office ɗin ba, yau sosai ƴan miskilancin nasa suke kusa.

Jingina bayanta tayi da jikin ƙofar tana kallonsa, wani irin murmushine ya bayyana akan fuskarta, kallonsa kaɗai idan tayi yakan sanya mata nutsuwa, sosai take jin son sa acikin ranta, komai nasa yana burgeta tana son duk wani abu nasa, musamman yanayin yanda yakeyin adonsa, uwa uba kuma kyau da kwarjininsa dake tafiya da imanin duk wata mace da zatayi tozali dashi, cikin takunta nason ɗaukar hankalinsa tasoma takowa zuwa cikin office ɗin. Ƙaran takalman dake ƙafanta shiya fara sanar dashi wacce ta shigo cikin office ɗin nasa, jiyayi wani abu ya toshe masa maƙoshi, sam yatsani ganinta ko kaɗan bayaso tana raɓarsa, baisan ita wace irin mace bace wacce bata da zuciya ko kaɗan. Harta ƙaraso gaf da inda yake bai ɗago dakansa ya kalleta ba, cikin muryar shagwaɓa tace.

"Barka da hutawa ranka ya daɗe"

Kamar ma baisan da mutum a wajenba haka yayi banza da ita, bakinta da yaji pink lips stick taturo gaba. "Maiyasa kakemin hakane wai Raj? at least dai ko kallona yakamata ace kayi wajenka fa nazo" taƙare maganar tana ɗan bubbuga ƙafafunta, alaman shagwaɓa.

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now