Chapter 13

10.8K 894 50
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SOORAJ !!!*

*Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*

*WATTPAD*
@fatymasardauna

#romance

*Chapter 13*

Wani numfashi mai ɗumi ya fesar daga bakinsa, haɗe da maida idanunsa ya rufe, kalamanta ne suka shiga yi masa yawo acikin kunnuwansa, ji yayi tsikar jikinsa na tashi, hakanne ma yasa ya kasa yin koda kyakkyawan motsi ne.

Ban ɗaki ta wuce ta je ta ɗauro alwala, sam bata san ya akayi bacci ya ɗauketa ba, taso ace bata makara ba, kasancewar yanzu har hasken rana ya bayyana. Tana idar da sallan ta gyara zamanta akan sallayan, sai alokacinne ta tuno da cewa aƙasa ta kwanta ba akan gado ba, "To kenan ya akayi ta koma kan gado?" tambayar da tayiwa kanta kenan, ƙaran buɗe ƙofar ɗakin da akayi ne ya katse mata tunaninta. Dr.Haisam ne yashigo cikin ɗakin bakinsa ɗauke da sallama, amsa masa tayi haɗe da gaidashi. Fuska asake shima ya amsa mata gaisuwar. Ƙarasawa gaban gadon da Sooraj ɗin ke kwance yayi. "Ya jikinna ka dai?" Dr.Haisam ya tambayi Sooraj wanda har yanzu bai sauya kwancia daga juya bayan da yayi ba.

Ziyada nashirin ce da Dr.Haisam bai farfaɗo ba, taji muryarsa ta doki dodon kunnenta.

"Da sauƙi!" Sooraj ya bashi amsa ataƙaice, sai alokacin ya juyo ya fuskanci Dr.Haisam ɗin.

"Masha Allah dama kullum haka mukeso, yanzu babu wani inda yake maka ciwo?" Dr.Haisam yatambayeshi cike da kulawa.

"Babu" ya bashi amsa ataƙaice.

"Masha Allah zamu baka sallama zuwa anjima, amma yana da kyau ka riƙa kulawa da lafiyarka, kasan fa lafiya itace komai arayuwa, sai da itane mutum yake sanin daɗin rayuwa, saboda haka kakiyaye abun da zai cutar dakai!"

Kai kawai Sooraj ya jinjina alamar yaji, sam baison magana mai tsawo.

Kallon Ziyada dake zaune tana kallonsu Dr.Haisam yayi. Fuskarsa ɗauke da murmushi yace. "Congrat ƴar ƙaramar ƙanwa, da alama brother ɗinki ya samu lafiya"

Murmushin daya bayyana kyawun fuskarta tayi haɗe da sunkuyar da kanta ƙasa, hakanan taji wani irin sanyi acikin ƙirjinta. Dr.Haisam na fita ta ɗago da kanta takai dubanta ga Sooraj wanda yake ta murza fatan hanunsa, kallon yanda jijiyoyin jikinsa suka fito sukayi raɗa raɗa tayi, gani tayi ya sanya haƙoransa ya danne lip ɗinsa na ƙasa, tamkar wani wanda yakejin wata azaba ta daban, tashi tayi daga kan sallayan cikin sanɗa tashiga takowa zuwa inda yake.

Muryarta na rawa tace "YAH...YAH!!" ita kanta batasan ya akayi ta ƙirasa da wannan sunan ba.

Cak ya tsaya daga murza hanunnasa da ya keyi haɗe da buɗe idanunsa da suka zama jajur dasu, ɗago da kansa yayi ya kalleta.

Sai da taji gabanta ya faɗi alokacin da idanunsa suka sauƙa acikin nata idanun, bakomai ya tsorata ta ba kamar yanda taga idanunsa sun rikiɗe daga farare zuwa jajaye.

Ko second biyu bai ɗauka ya na kallonta ba ya sauƙe idanunsa ƙasa.

Ƙwalla ne suka cika idanunta, murya araunane tace "Dama.... dama.. Bansani ba ne ko kanajin yunwa" tafaɗi haka tana mai murza ƴan yatsun hanunta.

"Miƙomin rigana" yafaɗi haka batare daya ɗago kansa ko ya tanka mata maganan da takeyi ba, babu musu ta ɗauko rigan nasa tazo ta miƙa masa, tashi tsaye yayi daga kan gadon haɗe da sanya rigarsa, Kallon ƙafansa ƴayi yaga ko takalmi baida shi. Hanu yasa ya dafe goshinsa.

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now