Chapter 25

11.9K 1.1K 115
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SOORAJ!!!*

*Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

*Wattpad*
fatymasardauna

#romance

*This Page Is Dedicated To You My Habibtie Niesher Jay. Love yhu Habibtie💘🔐*

*Chapter 25*

Cikin sauri tasoma tattara glass bowl ɗin daya tarwatse akan tiles ɗin, gaba ɗaya jikinta ɓari yake. Baiko kalli inda take ba ya juya ya koma toilet. Jiki asanyaye haka ta tattare wajen. Moper taɗauko tazo tasoma ƙoƙarin goge wajen da fruit salad ɗin ya ɓata, gashi gaba ɗaya glass bowl ɗin da fruit salad ɗin ke ciki ya tarwatse awajen.

Wanke hanunsa yayi acikin sink tare da ɗaukan wani ɗan ƙaramin towel ya goge gumin dake fesowa ta goshinsa, atunaninsa zuwa yanzu bata cikin ɗakin don haka ya murɗa handle ɗin ƙofar toilet ɗin ya fito, ganinta a durƙushe tana tattare fasassun glasses yasan yashi saurin ɗauke kansa daga gareta, direct gaban closet ɗinsa ya nufa, wani Pencil Combat jeans black ya ciro sai kuma wata white button shirt, kallon agogo yayi yaga har lokacin sallan Magriba yaɗan gota, tsuka yaja ahankali tare da ɗan cizan laɓɓansa.
Gaba ɗaya jikinta ɓari yake, tsoro takeji kada yayi mata faɗa ko yace zaiyi mata wani abun. Jin takunsa na isowa gareta yasanya batare data kulaba ta sauƙe hanunta akan wani fashasshen kwalba, yana cakanta kuwa saiga jini, wani ƙara ta sake cike da ɗan tsoro, dubanta takai ga hanunta wanda har yaɗan fara fitarda jini, take tasoma jin wani irin raɗaɗi. Sooraj dake tsaye agaban dressing mirror yana dressing hanunsa daya yanke, baiko waiwayo ya kalleta ba, yi yayima tamkar baiji ƙaran nata ba, yana kammala dressing ɗin, ya ɗauki kayansa ya wuce toilet.

Haka tacigaba da gyara wajen, duk da cewa hanunta nayi mata zogi amma haka ta daure.
Yana fitowa daga cikin toilet ɗin sassanyan ƙamshin turaren dake fita ajikin kayansa ya daki hancinta, cikin takunsa na isa yaƙaraso ta bayanta ya raɓa yafice daga cikin ɗakin batare da ko kallonta yayi ba. Tanajin rufewar ƙofarsa, tasaki wata ƙatuwar ajiyar zuciya, sai alokacin ruwan hawayen da suka cika idanunta suka samu daman gangarowa. Cikin mintuna ƙalilan ta gama gyara wajen, tattara fasassun glasses ɗin tayi tazubar a durstbin, daganan ta wuce ɗakinta duk raɗaɗi ya isheta.

Yana fita kaitsaye babban masallacin dake gefe da gidannasu kaɗan ya nufa, anan yayi sallan Magriba, haka ya zauna har aka ƙira sallan Isha. Koda ya idar da sallan bai ko motsaba, istigfari yashiga yi acikin zuciyarsa, duk ƙoƙarinsa nason kawar da tunanin dake neman addabar zuciyarsa abun yaci tura, kansa ya jingina ajikin bango tare da lumshe idanunsa, numfashi yake fitarwa ahankali yayinda yake furta kalman "Astagfirullah!" daga bakinsa ahankali. Ahankali nutsuwa ke sauƙa ajikinsa, yayinda yaji damuwarsa na gushewa, sosai yaɗanji sanyi acikin zuciyarsa. Ƙarfe 9 daidai yabaro cikin masallacin ya nufo gida.

Ziyada

Gaba ɗaya ɗan yankewan da tayi ya ɗaga mata hankali, sosai yake mata zafi da zogi, fitowarta daga toilet kenan tana ta faman hura iskan bakinta adaidai saitin wajen data yanke, zama tayi akan gado, tare da jawo school bag ɗinta, gaba ɗaya zaman kaɗaici ya isheta sam batajin daɗin zaman da take yanzu burinta shine akoma makaranta. Tajima tana dudduba littatafanta kafun daga bisani bacci ɓarawo yayi awun gaba da ita.

_SOORAJ_

Yana dawowa daga masallaci direct ɗakinsa ya wuce, gaban Computer ɗinsa ya ƙarasa tare da soma lallatsata, koda ya kunna wayarsa kuwa saƙon gaisuwane da kuma na jaje waƴanda abokai da ƴan uwa suka tara masa suka dinga shigowa, bai tsaya wani duba saƙon ba yamaida wayar ya ajiye, har ƙarfe 11 yana kan computer. Aɗan gajiye yaƙarasa gaban fridge, bottle water ya ɗauko tare da ɓalle murfin, magungunan dake hanunsa ya watsa abakinsa tare da bin kansu da ruwa, long jeans ɗin jikinsa ya cire yasanya wani 3 guater, hanunsa yakai kan makunnin wutan ɗakin ya kashe take duhu ya mamaye gaba ɗaya ɗakin. Kan lafiyayyen gadonsa ya hau tare da danna makunnin bedside lamp, take wani ɗan haske dark blue yabayyana acikin ɗakin. Lumshe idanunsa yayi tare dajawo pillow yaɗaura kansa akai, wata ajiyar zuciya ya sauƙe tare da sanya hanu ya shafi ƙasan maranshi, wanda yakejinsa aɗan kumbure, duk yanda zuciyarsa taso sanyashi dogon nazari yaƙi aminta da hakan, haka kuma yaƙi bawa brain ɗinsa daman yin tunani kamar yanda yasaba akoda yaushe, dayake acikin magungunan dayasha akwai maganin dayakesa bacci sosai, hakan yasa acikin mintuna kaɗan bacci ya ɗaukesa.

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now