Chapter 39

15.5K 1K 169
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

             *SOORAJ!!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

                *WATTPAD*
          @fatymasardauna
#romance

             *Chapter 39*

Amatuƙar gajiye ta dawo daga makaranta, gaba ɗaya ƙafafunta ciwo suke, kasancewar yau ɗin kusan awa guda suka ɗauka tsaye acikin Lab,  tana shiga cikin ɗaki tasoma rage kayan jikinta, wani white towel ta ɗaura aƙirjinta wanda ya kawo har kan santala santalan cinyoyinta,  bathroom ta wuce kai tsaye, wanka tayi tare da ɗauro alwala.  Wata pencil tightly skin gown tasanya wanda bayanta taƙasa yake aɗan tsage,  sosai rigan tabi haɗaɗɗiyar surar jikinta ta lafe,   wani ɗan madaidaicin hijab ta sanya ajikinta, kai tsaye tanufi ɗakin Oummu, tana knocking door ɗin,  Oummu ta bata izinin shigowa, Zaune tasameta akan wata luntsumemiyar kujera dake cikin ɗakin, gabanta wasu takardune yayinda hannunta ke ɗauke da pen.  Da murmushi akan fuskarta ta amsawa Zieyaderh gaisuwan da tayi mata, tare da ɗan zare farin glass ɗin dake sanye a idonta tana me cewa  "Ya school ɗin?"  "Alhamdulillah!" Zieyaderh ta amsa aɗan sanyaye, ƙatuwar  leda wanda ke ɗauke da tambarin sunan wani super market  Oummu ta miƙo mata tare da cewa. "Ungo amshi Kayan da kuka saya da Almustapha ne, ashe wai ke ya sayawa sai kimasa godiya"

Asanyaye takarɓi ledan dake shaƙe da kaya, cikin sanyin daya sake zama sabo agareta tace "Oummu kitayani godiya, nagode sosai!"
Murmushi Oummu tayi irin tasu ta manya tare da cewa "Ae kinfi kusa dashi ayanzu zai kyautu kiyi masa godiyan da kanki!"  

Murmushi kawai tayi cike da kunya ta sadda kanta ƙasa tare da miƙewa tsaye,  da ƙyar ta iya jan ledan don tana da nauyi, haka tafita daga cikin ɗakin tanajin wani iri acikin zuciyarta.  Tana shiga ɗakinta ta  Zazzage ledan akan gado, tabbas sayayyan da sukayi ita dashi ne, sam bata wani ji farinciki ba, juyawa tayi ta fice aɗakin don samawa kanta abun da zata ci,  batajin cin wani abu hakan yasa ta tsiyayo fresh milk me sanyi,  kanta aƙasa take haura step ɗin da zai sadata da samannasu,  sam bata kula da cewa shima yana zuwa ba,  haɗuwarsu waje ɗaya ne yasanya gaba ɗaya fresh milk ɗin ya zube masa ajiki, cikin tsautsayi cup ɗin ya faɗi ya tarwatse a wajen.  Aɗan razane ta ɗago kanta ta kalleshi, daidai lokacin shima ya ɗago kyawawan  idanunsa, idanunsune suka sauƙa acikin na juna,  da sauri tayi baya kasancewar sunyi matuƙar kusa da juna, bisa tsautsayi ta aje ƙafanta akan fasassun glass, wani irin ƙara ta sake tare da rumtse idanunta ƙam, beautyful eyes ɗinsa yaɗan zaro waje tare da kallon ƙasa inda ƙafanta tuni har ya soma fidda jini.  Ƙaran da tayi shiya janyo hankalin Oummu, da sauri ta fito tare da ƙarasowa inda suke,  cikin yanayi na damuwa tace
"Subahanallahi me ya faru?"    cikin tsananin zafin dake ratsa har ƙwaƙwalwarta, ta buɗe idanunta da suka tara ruwan hawaye kana sukai ja, yunƙurin ɗaga ƙafanta ta somayi, amma zafin da takeji ya hanata, hakan yasa ta saki wani ɗan siririn ƙaran wahala,   small pink lips ɗinsa ya ɗan ciza tare da raɓawa  ta gefenta zai wuce.  "SOORAJ me kayi mata ne?" cewar Oummu tana me ƙoƙarin kama ƙafan Zieyaderh don ta duba,  fuska ɗauke da ɗan mamaki yasake ɗan waro Idanunsa alaman ni kuma mezan mata, kana ya taɓe lips ɗinsa.
"Subahanallah tayaya haka ta faru? Glass fa ta taka" Oummu tafaɗa tana me riƙe da ƙafan Zieyaderh, wanda har yanzu yake fidda jini, ƙarasowan Almustapha cikin falon kenan ya taraddasu atsaitsaye,  da sauri ya ƙaraso garesu yana me cewa "Lafiya kuwa Oummu me ya faru?"

"Fasashshen glass ta taka, please zoka riƙemin ita naɗauko first aid box sai kayi mata treatment!" Oummu ta faɗa cike da tausayin halin da  Zieyaderh ke ciki.
Babu musu Almustapha ya haura kan step ɗin tare da sanya hannayensa duka biyu ya kama kafaɗun Zieyaderh, wanda hakan yasa harta ɗan kwanto cikin jikinsa.  Sauƙe hannayensa akan kafaɗunta, yayi daidai da bugawar zuciyarsa, da sauri ya rumtse idanunsa tare da dunƙule hannuwansa, lokaci ɗaya yaji wani irin jiri na neman kadashi, aɗan hanzarce ya juya cikin azama yabar falon. 
Da taimakon Almustapha ta iya ɗingisawa zuwa kan kujera, sosai takejin zafi domin kuwa glasses ɗin sun ɗan caketa sosai,  Oummu ne ta dawo hannunta ɗauke da first aid box,  zama Almustapha yayi akan sofa tare da ɗaukan ƙafannata ya ɗaura akan wani ɗan madaidaicin stull,  da cotton yayi using wajen goge mata jinin da ya ɓata ƙafannta, hannunsa yasa ya kama ƙafan, cike da kulawa ya shiga dubawa ko akwai wata ɓoyayyar kwalba dake a
cikin ƙafar, ganin babu yasanyashi ɗaukan hydrogen  ya haɗa da auduga ahankali yake ɗan goga mata akan ciwon, kuka tasanya me sauti tare da rumtse idanunta, sosai takejin zafin hydrogen ɗin,  murmushi Almustapha yayi ganin yanda take kuka tana me cije baki,   cike da salon tsokana yace.
"Haba Bae da zafi ne?" 

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now