Chapter 23

13.4K 1.1K 147
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

          *SOORAJ !!!*

   *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

           *WATTPAD*
    @fatymasardauna

#romance

         *Chapter 23*

Abba da Mas'oud ne suka tashi suka fice daga cikin ɗakin, kasancewar alokacin har ansoma ƙiraye ƙirayen sallan Magriba.  Ummu ne tafito daga toilet ɗin dayake cikin ɗakin, fuska da hannayenta duk ruwa da'alama alwala tayi.

Kallon Ziyada dake zaune jigum tayi.   "Jekiyi alwala" Ummu tafaɗa tana mai ƙoƙarin shimfuɗa darduma akan tiles.  Sumu sumu haka ta wuce toilet ɗin ta ɗauro alwala,  hanu tasanya acikin hijab ɗin dake jikinta, ta zaro ɗan kwalin dake kanta, shimfiɗawa tayi akan tiles, sannan ta hau tare da daidaita tsayuwarta, akan ɗan kwalin ta gabatar da sallan Magriba, ko da ta idar da sallan, samun kanta tayi dayin shiru, tare da jingina kanta da jikin bango,  gaba ɗaya jin zuciyarta take babu daɗi,  babu wani abu da takeson gani sama da Helper ɗinta, sosai hankalinta yake atashe, sannan gefe guda kuma, ga kukan da taga mahaifiyar Sooraj ɗin nayi yasake ɗaga mata hankali. 

Dukansu daga ita har Ummu babu wacce tatashi daga kan abun sallanta, har aka ƙira sallan isha,   baga Ummu kaɗai ba hatta Ziyada saida tasanya Sooraj cikin addu'anta.    Ƙoƙarin ɗaura ɗan kwalin kanta take, aka turo ƙofar ɗakin aka shigo.   Alh.Mansur ne dakuma Mas'oud,  Mas'oud ne ya aje basket ɗin dake hanunsa, tare da kai dubansa gareta.

"Ziyada ki zubawa Ummu abinci taci, kema ki ɗebi naki kici, zuwa anjima likitotin sun tabbatar mana da cewa zamu samu ganinsa!"  Mas'oud yaƙare maganar cike da ɗan yanayi na damuwa.    Alh.Mansur kuwa kasa ma cewa komai yayi, zama kawai yayi akusa da Ummu tare dayin shiru.

Ɗaukan basket ɗin Ziyada tayi tare da zaro wasu plate,  kulan dake cikin basket ɗin ta buɗe tare da sanya spoon ta zuba lafiyayyar jalop rice wacce taji bushashshen kifi acikin plate ɗin. Cike da ladabi ta ƙarasa gaban Ummu, cikin muryarta dake rawa tace.  "Ummu ga abinci"

Kai Ummu tagirgiza cike da damuwa tace.
"Banajin zan iya cin abinci batare da na sanya ɗana a idanuna ba, kici kawai!" gaba ɗaya muryar Ummu rauni kawai take bayyanawa. 

Hanun Ummu Alh.Mansur ya kamo, cike da tsananin so da kuma nuna kulawa ga matartasa yace.   "Ki kwantar da hankalinki Sulaimiyya, Isha ALLAH Sooraj zai samu lafiya, addu'an mu kawai yake da buƙata bakomaiba,  kibar kukannan haka kuka banaki bane."   Kallon Ziyada yayi tare da cewa.

"Miƙomin abincin nan na bata"     karɓan plate ɗin abincin Abba yayi yashiga lallaɓa Hajiya Sulaimiyya akan taci, amma gaba ɗaya ta daburce taƙi ci, hawayene kawai ke silalowa daga cikin idanunta, shima kanshi Abban ƙarfin hali kawai yake amma damuwane ninke aƙasan ranshi. 

Gaba ɗaya itama Ziyada kasa cin abincin tayi,  lomanta uku ta ture plate ɗin abincin gefe, ji tayi ko kallon abincin batasonyi, hawayene suka ziraro daga cikin idanunta, da sauri tasanya gefen hijabinta ta share,  tausayin halin da taga Iyayensa aciki take, musamman yanda taga hawayen mahaifiyarsa ya kasa daina zuba,  jitayi gaba ɗaya zuciyarta ta karye.. 
Da ƙyar Abba yasamu Ummu taci 4 spoon na abincin.   Dr.Mohd ne dakanshi  turo ƙofar ɗakin ya shigo.   Cike da tausayawa ya dubi dukkaninsu, da sauri Alh.Mansur yataso daga zaunen da yake yana cewa.

"Dr.Mohd ya dai, akwai wani cigaba ko kanaga kawai gobe mu wuce Germany ɗin?"    Yanayin yanda Alh.Mansur yayi maganan kaɗai ya isa sanya zuciyar mai sauraro karyewa, domin kuwa kallo ɗaya zakayi masa kasan baya cikin wata nutsuwa, sosai rashin lafiyar Sooraj ɗin ke damunshi. 

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now