Chapter 19

11.6K 1.1K 90
                                    


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

             *SOORAJ !!!*

   *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*
_{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

           *WATTPAD*
     @fatymasardauna

#romance

          *Chapter 19*

Tsaye take ajikin window tana mai jiran shigowanshi,  amma kuma sai dai ga mamakinta har anshare sama da mintuna 10 baishigo cikin falon ba, sake gyara tsayuwanta tayi,  tare da soma murza ƴan yatsun hanunta.    Buɗe ƙofar falon yayi ya shigo, yana mai ƙoƙarin cire suit ɗin dake jikinshi,  idanunsa ne suka sauƙa akanta, amma saiyayi saurin kawar da kanshi gefe, tare da ƙarasawa cikin falon,  aje suit ɗinnasa yayi akan kujera tare da cire agogon dake ɗaure atsintsiyar hanunshi,  gaban fridge yaje tare da buɗewa ya ɗauko goran ruwa, ɓalle murfin yayi tare da kaiwa bakinsa, saida ya tabbatar da cewa babu komai acikin goran,  sannan yayi wurgi da goran cikin dustbin, dawowa cikin falon yayi ya ɗauki suit ɗinshi kana ya nufi hanyar bedroom ɗinsa, gaba ɗaya ma yi yayi kamar baisan da zamanta acikin falon ba,  tana ganin shigewarsa cikin ɗaki.  Ta saki wani gauron  numfashi, sam bazata iya yi masa magana ba, kwarjininsa ya wuce gaba ɗaya tunaninta, sumu sumu haka ta wuce tayi ɗakinta.

Kwance yake acikin jakuzzie ɗinsa, wanda yasha haɗaɗɗen ruwan wanka,  daga kan ƙafafunsa zuwa ƙirjinsa, gaba ɗaya lume suke acikin ruwa, kansa da hannayensa ne kawai suke waje, yayinda kyawawan idanunsa suke alumshe, kana ya ɗan jingina bayan kanshi da jikin jakuzzie'n,  gaba ɗaya hankali da tunaninsa baya tare dashi,  sam kwana biyunnan baya cikin wata gamsashshiyar nutsuwa, tunani da damuwa sune abun da suka sakoshi gaba,  akullum kuma ako wacce rana jin kansa yake tamkar wani baƙon halitta, ya sani acikin rayuwarshi akwai tawaya sosai, amma kuma baison ya zamanto mai rauni saboda hakan,  baiso yazama ɗaya daga cikin irin mutanennan da basa iya riƙe damuwarsu,   shikansa ya sani da ace lafiyarshi ƙalau, to da bazai taɓa iya kai wannan lokaci mai tsawo haka, batare da mace akusa dashi ba, "Menene matsalarsa? mecece damuwarsa? meyasa baya iya zama da mace?" yasan duk waƴannan abubuwan iyayensa suna da buƙatar sani,  "Amma mai yasa basa tambayarsa?" wannan tambayar shi ne abun da yake tambayar kanshi akullum, baikamata don ya kasance Namiji su sakar masa ragamar rayuwarsa ba, duk da cewa ya girma amma tabbas yana da buƙatar kulawan Iyaye atare dashi.
Wani numfashi yaja tare da fesarwa alokaci guda,    wani irin tausayin kanshi yakeji, sosai yake tausayawa al'amuranshi,  baisan taya zai dubi wata mace yace yana sonta ba, haka kuma baisan wace macece zata iya zama ta jure lalurar shi ba,  bazai taɓa yaudaran kanshi ba, saboda yasan babu wata mace da zata iya jure zama dashi ayanda yake, musamman ma idan tasan ƙatuwar matsalan dake tare dashi, yasani  shi me raunine ako da yaushe, safe, dare, rana, babu wani lokaci da zaizo masa yana cikin farinciki da walwala,  sau da dama yakanji kamar yayita kuka, ko da zai samu salaman rage ƙuncin dake cikin zuciyarshi, saidai hakan baya samuwa ayanzu, sakamakon zuciyarsa da tayi tauri,   haƙoransa yasa ya ɗan ciji laɓɓansa da ƙarfi, shi kaɗai yasan me yake ji, haka kuma shi kaɗai yasan kalan  ƙunci da yake ciki,  sama da shekara 10 kenan da haske ya gujewa rayuwarsa, azahiri acikin haske yake rayuwa, amma kuma idan aka duba bayansa duhune dulum mai wuyar kalluwa.    Cikin rashin kuzari haka yayi wanka, tare da ɗauro towel akan waist ɗinsa ya fito daga cikin toilet ɗin.
Zama yayi akan gado tare da ɗauko mayinsa ya soma shafawa, yana kammalawa ya feshe jikinsa da body spray mai daɗin ƙamshi.  3 guater jeans and white t-shirt ya sanya,  laptop ɗinsa mai ɗauke da tambarin apple asaman murfin ya ɗauka,  tare da ficewa daga cikin ɗakin.  Aje laptop ɗin yayi akan rug tare da buɗe fridge ya ɗauko goran pepsi mai matuƙar sanyi.  Zama yayi akan rug ɗin, tare da tanƙwashe ƙafafunsa, buɗe laptop ɗinshi yayi ya soma gudanar da aikinsa kamar yanda ya sabayi akowacce rana.
**
Ziyada kuwa komawa ɗaki tayi, tayi kwanciarta, harta fara bacci ta tuno cewa wulaƙanta abinci ba kyau,  hakan yasa ta fito saɗaf saɗaf  kan dinning ɗin ta nufa, abincin yana nan kamar yanda ta ajiye sa, ɗaukan kulan tayi ta fice daga cikin falon, direct wajen maigadi ta nufa nan ta sameshi zaune shida Kamalu driver suna hira,  kulan abincin ta basu, duk da basusan menene aciki ba saida sukayi mata godiya,  ita kuwa ta juya ta koma ciki.     Zama Kamalu driver da maigadi sukayi,  suka ci shinkafa da miyan, sam basuji wani abu na'alamar rashin daɗi acikin abincin ba, haka suka ci abincin sukayi nak.

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now