Chapter 21

11.2K 970 65
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

                *SOORAJ*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain and motivate he mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

             *WATTPAD*
       @fatymasardauna

#romance

           *Chapter 21*

Jini ne ke fitowa daga jikinsa yana malala akan white tiles ɗin da ya mamaye gaba ɗaya falon.   Wasu ƙattin maza guda biyune suka fito daga maboyarsu, wato bayan labule kenan inda suka ɓoye, ko wannensu fuskarsa sanye take da mask, dukansu suna sanye da baƙaƙen kaya, sannan kuma kowannensu ahanunsa ɗauke take da bindiga, ɗan ranƙwafowa  ɗayan yayi tare da ɗaura hannunsa adai dai saitin hancin Sooraj, jin baya numfashine yasa ya kalli ɗayan ɗan uwannasa.  Alama yayi masa da ido akan su tafi aiki ya kammala,  babu wani ɓata lokaci, aƙagauce suka fice daga gidan..   10 minute da tafiyarsu saiga ƴan sanda har mota biyu.  Alhaji Ilyass (maƙocin Sooraj)  dake laɓe jikin gate ɗin gidansa, yana ganin ƴan sanda ya ƙaraso garesu haryana jin tuntuɓe, aruɗe yace.   "Yauwa ranka ya daɗe kun ƙaraso? Ni ne nan naƙiraku, tabbas naji ƙaran harbin bindiga awannan gidan har sau biyu, saboda haka duk yanda akayi babu lafiya!" yafaɗi haka yana me sharce gumin dake yankowa ta gaban goshinsa, gaba ɗaya atsorace yake, ƙiran ƴan sandan ma da yayi baƙaramin Jahadi yake ganin yayi ba, saboda tsorone cike fal aransa. 

Cike da rashin tsoro haka ƴan sandannan suka rarrabu, kowanne daga cikinsu ya saita kunamar bindigarsa, ƙiris sukejira su saki harsasai,  haka sukayi cikin gidan Sooraj,  ahankali suka tura ƙofar falon suka shiga, ganin bakowa acikin falon yasa suka shiga ƴan dube dube, yayinda wasu daga cikinsu suka nufi bedrooms ɗin dake cikin falon, ɗaya bayan ɗaya haka suka shiga suna dubawa, ɗaya daga cikin ƴan sandan ne idanunsa suka sauƙa akan jinin dake kwance ya daskare akan tiles, jawo ogansu yayi ya nuna masa jinin,  aikuwa suna leƙa bayan kujera sukaga mutum yashe aƙasa, gaba ɗaya jini ya ɓata jikinsa, aɗan razane sukayi kanshi, daidai lokacin sauran ƴan sandan suka dawo cikin falon.   "Sir gaba ɗaya fa mungama duba gidannan bakowa acikinsa" suka faɗa suna mai kallon Sooraj dake yashe aƙasa.   Shiru ogannasu yayi tare da ciro wayarshi acikin aljihunsa ya danna ƙiran asibiti.  Kallon sauran ƴan sandan yayi yace subi hanya duk wanda suka gani sukamashi.  hakan kuwa akayi duk suka watse yazama saura mutane ƴan ƙalilan.  Ƙarar jiniyan ambulance ne yacika gidan.    Ɗaukan Sooraj akayi aka sanyashi acikin ambulance ɗin, suka wuce asibiti.
Babban asibitin dake cikin garin Lagos suka wuce dashi, direct ɗakin bada taimakon gaggawa aka nufa dashi, duk da cewa basu da tabbacin cewa yana da rai ko bayidashi.   Dr. Femus shine mutumin daya fara cire handglobes ɗin dake hanunshi, kallon sauran abokan aikinnasa yayi yace.  "He is dead!"   Jikinsune gaba ɗaya yayi sanyi, saboda haka suma suka soma ƙoƙarin cire handglobes ɗin dake hanunsu.

Dr. Fawwaz da bai yarda da abunda Dr.Femus yace ba, yaɗan matso gaf da Sooraj ɗin tare da kama hanunsa ya riƙe, sannan ya ɗaura kansa adai dai saitin ƙirjinsa inda zuciarsa ta ke.  Da sauri ya ɗago da kansa tare da cewa "Bai mutu ba, zuciyarsa na bugawa, muyi sauri mucire masa bullet ɗin dake jikinsa!"   nan suka duƙufa aikin cire bullet ɗin dake jikinsa.    Sunyi masa gwaje gwaje sosai,  inda suka tabbatar da cewa bai mutu ba, amma kuma su kansu basu san awani condition yake ba, abu ɗaya suka sani shine, zai iya wucewa tacan zai kuma iya tashi, duk wannan na Allah Ne.  Duk abun daya kamata suyi mishi sun masa, sannan suka killaceshi awani ɗaki na musamman. 
***
Gaba ɗaya ta hargitsa gadon, sai juye juye take, ta ya mutsa ko ina, gashin kanta gaba ɗaya ya watse akan gadon, yayinda ta sanya hanunta ta damƙi zanin gadon da iya ka ƙarfinta,   duk da cewa sanyin ac na tashi acikin ɗakin, amma ita wani irin gumine ke fitowa daga jikinta.  Arazane ta ware manya manyan idanunta da sukayi jajur dasu, tashi tayi ta zauna tare da dafe ƙirjinta dake bugawa da sauri.   "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!!" tafaɗa cikin wata murya me rauni, kawai saita  samu kanta da fashewa da kuka, kuka tayi sosai wanda itakanta batasan na menene ba, aƙalla taɗauki kusan 40 minute tana kuka harsaida muryarta ta dashe, idanunta ne suka sakeyin jajur dasu,  jin ana ƙiran sallan asuba ne yasata miƙewa ta nufi toilet,  doguwar rigan dake jikinta ta cire tare da tsayawa agaban shower ruwa yashiga dukan ta,   bazata iya tuna mafarkin me tayi ba, amma tabbas tasan taga wani abu wanda yake shirin taɓa rayuwarta,  wani irin bacci tayi wanda adunia bata taɓa bacci marar ɗaɗinsa ba,  MR. HANDSOME shine wanda tunaninsa ya kutso cikin rai da zuciarta,  aƙalla ta ɗauki kusan sama da 15 minute tana tsaye ruwa na dukanta,  da ƙyar ta iya ɗauro alwala tafito, domin gaba ɗaya bata jin ƙarfin jikinta.

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now