Chapter 8

12.2K 1K 39
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SOORAJ !!!*

*Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*

_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*


*WATTPAD*
@fatymasardauna

*Chapter 8*

Tana buɗe ƙofan idanunsu ya sarƙe acikin na juna, wani irin tsorone taji ya kamata, take jikinta ya ɗauki rawa.

Kallo ɗaya yayi mata ya watsar agadarance yace.

"Wuce mukoma ciki"

Samun kanta tayi da kasa musa masa, tana gaba yana biye da ita abaya, suna shiga cikin falon ya murzawa ƙofar key, direct ya wuce ɗakinsa ko kallonta baiyiba, tana ganin wucewarsa cikin ɗaki ta saki wani irin marayan kuka. Yana shiga cikin ɗakin yasoma rage kayan jikinsa. Toilet yashiga yayi wanka, fitowa yayi dagashi sai towel dake ɗaure a ƙugunsa. Sama sama yashafa mai, farin riga da blue ɗin wando yasanya, ba abun dake tashi ajikinsa sai daddaɗan ƙamshi, buɗe ƙofar ɗakinnasa yayi yafita zuwa falo, ko kallon inda take durƙushe tana kuka baiyi ba, kitchine ya nufa, mintuna ƙalilan yadawo hanunsa ɗauke da wani faranti wanda samansa ke ɗauke da kayan fruit.

Zama yayi akan ɗaya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun falon, haɗe da ɗaura ƙafansa akan rug, apple ya ɗauka yana gutsura ahankali, jingina bayansa yayi da jikin kujera haɗe da lumshe idanunsa, ahankali yake tauna apple ɗin dake cikin bakinsa, a rayuwarsa idan yaji kukan mace sosai hankalinsa ke tashi, amma a yau ko ajikinsa, daɗima kukannata keyi masa, gani yake ita damuwarta ma mai sauƙice tunda hartana iyayin kuka, shi kuwa shi kaɗai yasan abun da ya keji, idan da zai samu daman yin kuka to tabbas da yayi, idan da za'ace dashi idan yayi kuka matsalarsa zata yaye to tabbas da shikam yayi kuka irin kukan da ya amsa sunanshi kuka, ba irin nata kukan na shagwaɓa da sakalci ba. Ahankali sautin kukanta ke tashi acikin falon, ware idanunsa da suka somayin ja yayi haɗe da watsa mata su. "Keee!!" yafaɗa murya akausashe.

Ɗago fuskarta da yayi caɓa caɓa da hawaye tayi ta kallesa. Yanayin yanda taga idanunsa sunyi jajur ne yasa taji gabanta ya faɗi, miƙewa tsaye yayi, haɗe da takowa harzuwa inda take, hanunsa yasanya ya finciko nata hanun, yana janta haka suka fita daga cikin falon, yana zuwa bakin motarsa ya buɗe murfin motar haɗe da cillata ciki da ƙarfi, har saida ta buge goshinta, shiga cikin motar yayi haɗe da kunnata, baijira mai gadi yagama wangale masa gate ɗin bama, ya figi motar da wani irin gudu haɗe da cillata kan titi. Gudu yaketa shararawa akan titi, bai tsayaba harsai da ya kusan fita daga cikin Kaduna, parking yayi agefen titi.

"Fita!"
yace da ita cikin wata irin murya.

Tsaida kukanta tayi cak, haɗe da ƙura masa ido.

"Kifitarmin amota nace!!" yanzu kam atsawace yayi maganar.

Jikinta na rawa tasoma kiciniyar buɗe murfin motar. Yanajin fitanta yayi reverse haɗe da cilla motarsa kan titi, bayan ya buleta da ƙura yabar wajen.

Tana ganin ɓacewar motarsa ta saki wani irin kuka haɗe da durƙushewa a wajen, kuka take mai cike da tsananin tausayin kanta, kuka take nakasancewarta marar gata, kuka take nakasancewarta ƴa mace marar galihu... Sama da mintuna 14 ta kwashe tana durƙushe a wajen, jifa jifa motoci ke wuceta.

Wata haɗaɗɗiyar motace ta tsaya adai dai gabanta, da sauri taɗago atunaninta shine yakuma dawowa, wani saurayi tagani ya sauƙe glass ɗin motar sa, haɗe da sakar mata murmushi.

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now