Chapter 40

12K 956 110
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SOORAJ !!!*

*Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*WATTPAD*
@fatymasardauna
#romance

*Chapter 40*

Hira Oummu da ƴan uwanta sukayi sosai inda suka cigaba da tsara yanda bikin zai kasance. Aunty Muhibbat wanda takasance itace ƙaramar cikinsu ta kalli Oummu tare da cewa "Ni aganina idan babu damuwa, zamanta ya dawo wajena saboda kinga ina tare da shuwa arab saboda haka ba ƙaramin gyara zata samu ba" murmushi Oummu tayi tare da cewa "Hakane amma aikinsan tana zuwa makaranta, duk da ma dai muntsara kan cewar awannan year din zata zana waec nd neco ɗinta"

Cike da jin daɗi Aunty Muhibbat tace "To Allah yasa ayi komai dai a sa'a" da "Ameen" suka amsa su dukansu, basu wani jima sosai ba suka kama hanyar tafiya bayan sun jibgewa Oummu tsarabobi masu yawa da suka kawowa surukarsu Zieyaderh.

Ɓangaren Zieyaderh kuwa jin kamar ta takura yasanya cikin nutsuwa ta shiga warware sari ɗin dake jikinta tare da aje sa gefe. Ajiyar zuciya ta sauƙe akaro na barkatai, tare da ɗan jingina kanta da saman gadon da take zaune akai, tunanine cike fal azuciyarta, turo ƙofar ɗakin da akayi ne yasanyata ɗago kanta ta kalli bakin ƙofan, Nabila ce tashigo cikin ɗakin cikin ɗan rusunawa tace "Hajiya tace ayi mata ƙiranki"
Murmushi Zieyaderh ta ɗanyi tare da ƙoƙarin miƙewa tsaye "Ganinan zuwa" tafaɗa tana me zura bedroom slippers aƙafanta. Kai tsaye ɗakin Oummu'n ta nufa, ɗan tsayawa tayi ajikin ƙofan tare dayin knocking. Sanin cewa itace yasa Oummu dake zaune akan gado ta bada izinin shigowa, da sallama ɗauke abakinta ta shigo tare da neman waje taɗan rusuna daga gefe.

Oummu da yawancin lokuta fuskarta baya rabo da murmushi yanzun ma murmushine ɗauke akan fuskarta, miƙowa Zieyaderh wata haɗaɗɗiyar ƴar jaka me kyau tayi, amsan jakan Zieyaderh tayi tana me kallon Oummu cike dason ƙarin bayani, "Kyautane daga surakanki, inafata zakiyi murna zakuma ki yaba da kyautar!" Oummu tafaɗa tana me ƙoƙarin manna farin glass akan idanunta.

Jitayi gaba ɗaya jikinta yayi sanyi sunkuyar dakanta ƙasa tayi asanyaye tace "Nagode sosai Oummu amma sai nake ga kamar kyautan sunyi yawa, duk dama banga menene aciki ba!"

Murmushi Oummu tayi tare da cewa "Bana tunanin kyautar tayi yawa kedai ki amsa kawai, gaba kuma idan kunsake haɗuwa sai ki musu godiya"

Cike da jin nauyin Oummu'n tasake yi mata godiya sannan tatashi ta wuce ɗakinta. Koda taje zama tayi akan gado tare da buɗe jakar, wani ɗan box me kyau da burgewa taciro daga cikin jakan, tare da buɗewa, wani danƙareren agogon hannu na gwal ne ya bayyana acikin kyakkyawan box ɗin. agogone na mata me matuƙar ɗaukar hankali, kyawawan duwatsunsa sai ɗauke ido suke, sake fito da wani box ɗin tayi wanda har yamafi wancan ɗin girma, shi kuwa wani irin danƙareren sarƙa da ɗankunnen gwal ne acikinsa me kyaun gaske, sosai design ɗin sarƙan ya mata kyau, har batasan sanda ta saki lallausan murmushi akan fuskarta ba, ganin kyaututtukan nada yawane yasanyata zazzage jakan gaba ɗaya akan gado, nan tayi arba da wasu arebian gown masu kyaun gaske, tare da wasu kwalaben humra masu ƙamshi irin masu kama jiki ɗinnan, cike da jin daɗi ta tattara kayan ta maida cikin jaka, sosai kayan suka mata kyau saidai kuma tasan matsayinta baikai nanba, bai kamata ace amatsayinta na ƴar wanda ba kowa ba ayi mata irin wannan hidiman, shigowar Nabila cikin ɗakinne yasanya ta tsaida duk wani abu da take tana kallonta.

"Hajiya tace ashaida miki kina da baƙo awaje"

Ƙirjinta ne ya buga da ƙarfi yayinda taji gabanta ya ɗan faɗi cikin yanayi naɗan mamaki tace "Baƙo?"
Kai kawai Nabila ta iya kaɗa mata alamar "Eh" kasa cewa komae tayi har Nabila ta juya ta fice daga cikin ɗakin, Vail ɗinta me kyau da walwali ta sanya tarufe jikinta, cikin fargaban sanin ko waye haka ta buɗe ƙofar ɗakin ta fita, bata samu kowa afalon ba hakan yasa kaitsaye tanufi ƙofar da zai sadata da compound ɗin gidan.

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now