Chapter 18

11.2K 1K 68
                                    


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

              *SOORAJ !!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*
_{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://facebook.com/kainuwawritersassociation*

           *WATTPAD*
     @fatymasardauna

#romance

         *Chapter 18*

Ƙirjinsa ne ke ta dokawa kamar zai fito waje. Yana ƙarasawa gaban gadon yaja ya tsaya tare da kafeta da idanunsa, jin kukanta yake har acikin ransa,  hannayen rigansa ya ɗan naɗe tare da nufar  toilet ɗin ɗake cikin ɗakin,     heater ya kunna ya tari ruwan zafi acikin wani ɗan madaidaicin bucket,  towel ya ɗauko sannan ya fito daga cikin toilet ɗin.   Ƙafansa ɗaya yasanya ya taka kan gadon, baisan tayaya kuma ta ina zai fara ba, hakan baikamacesa ba, sannan kuma sam hakan ba aikinsa bane, saidai kuma sosai yake tausayin halin da take ciki.  Aƙalla yaɗau kusan mintuna 10 a haka ya kasa aikata komai, yayinda ita kuwa har yanzu take aikin kuka gaba ɗaya tasake fita  hayyacinta,    zama yayi akan gadon tare da sanya towel ɗin acikin ruwan zafi,  hannayensa ne suka ɗauki rawa, ya kasa  koda kai hanunsa jikinta, zuciyarsa bugawa take,  hanunsa yakai kan wuyanta ya ɗan taɓa, ji yayi babu wani zazzaɓi sosai ajikinnata,   rumtse idanunshi yayi tare da kai hanunsa kan lafeffen cikinta,  tamkar wanda aka jonawa shocking haka hannayensa ke rawa, da ƙyar ya iya ɗan ɗage rigan dake jikinta yayi sama dashi,   still hannayensa na rawa yasanya hanu ya ɗanyi ƙasa da sket ɗinta, towel ɗin yaciro daga cikin ruwan zafin tare da ɗan matsawa ya rage ruwan dake jiki,   sake rumtse idanunshi yayi tare da ɗaura towel ɗin adai dai kan cikinta, wani ƙara tasanya tare da ɗan soma yunƙurin tashi zaune, baisan sanda yasanya ɗayan hanunsa ya maida ita ta kwanta ba,  sai alokacin ya samu damar buɗe idanunshi ya sauƙesu akan fuskarta, hawaye ne kawai ke gangarowa ta gefen idanun ta, gaba ɗaya ta galabaita. Sake danna towel ɗin yayi akan cikinta, gani yayi ta sake rumtse  idanunta, ahankali  yake ɗan matsa towel ɗin akan cikinta, ƙasa ya somayi da towel ɗin daidai kan mararta ya tsaya,  Yanayin yanda yake matsa towel ɗin akan maranta ne, yasanya ta jin wani ɗumi na ratsa gaba ɗaya ilahirin jikinta, sake maida towel ɗin cikin ruwa yayi tare da ɗan matsewa, sake manna mata yayi akan maranta, haka yadinga yi mata har tsawon wasu lokuta,  ahankali kukanta ya tsaya cak, wani irin ajiyar zuciya take sauƙewa akai akai, fitar numfashinta ne ya soma sanja sauti, ya  zama na yana fita slowly,   duk wannan abun da yake mata, bai bari idanunshi sun kaishi ga kallon jikinta ba. Cikin wani irin yanayi na wahala ta kamo hanunsa na hagu ta riƙe acikin nata hanun,   ganin haka yasa ya aje towel ɗin agefe, ɗan ranƙwafowa yayi tare da kawo bakinshi dai dai saitin kunnenta, ahankali ya soma hura mata iskan dake bakinsa acikin kunnenta.  Daddaɗan ƙamshin  turarensa ne ke ziyartan hancinta, yayinda iskan bakinsa dake hura mata ya kasance garkuwa wajen  samun nutsuwarta, ahankali taji wani irin salama na sauƙar mata, cikin wani irin yanayi hucin numfashinsu ke gauraya waje guda,  jin yanda sautin numfashinta ya sauya ne, yasanyashi ɗan ɗago da kansa ya dube ta,   gani yayi tana fitar da numfashi ahankali da alama bacci ne ya ɗauketa, wata ƙatuwar ajiyar zuciya ya sauƙe, tare da ɗago kansa daga ranƙwafon da yayi, hanunsa dake cikin nata ya kalla wanda ta damƙeshi gam. Ƙoƙarin cire hanunsa daga cikin nata yayi,  amma yaji ta sake riƙe shi gam, cikin ɗan dabara ya samu ya zare hanunshi,  hannayensa ya ɗaura akan kafaɗunta tare da gyara mata kwanciya, blanket ya rufa mata, sannan ya rage mata hasken ƙwan wutan dake cikin  ɗakin,  tashi yayi ya fita tare da jawo mata ƙofar.     Ɗakinshi ya koma yayi kwanciyarsa, ya jima kafun bacci ɓarawo ya samu damar ɗaukarsa.

Tunda ta kwanta ba itace ta farka ba sai ƙarfe 8:00 daidai na safiya, ahankali take buɗe gajiyayyun idanunta da suka kumbura sukayi luhu luhu dasu, kasancewar daren jiya tasha kuka sosai, tashi tayi ta zauna akan gadon tare da sanya hanu ta shafi saman mararta, ko ɗigon ciwo bataji ajikinta saidai kasala kawai dake damunta, lumshe idanunta tayi tana mai ƙoƙarin son tunano abun da ya faru da'ita a daren jiya, ita dai bazata iya cewa ga abun daya wakana ba, amma tabbas tasan ta ganshi acikin idanunta, sannan kuma taji daddaɗan ƙamshinsa acikin hancinta,  amma wata zuciyar ta na faɗa mata cewa ba shi bane.  Zuro ƙafafunta ƙasa tayi daga kan gadon tare da tashi tsaye, banɗaki ta wuce ta haɗawa kanta ruwan wanka mai ɗan ɗumi,  sosai taji daɗin wankan da tayi domin ya ƙara taimakawa wajen warware mata gajiyan dake jikinta. 

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now