Chapter 55

14K 1.1K 132
                                    

  🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

          *SOORAJ!!!*

     *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

                 *Wattpad*
         @fatymasardauna
#romance

                  *Chapter 55*

Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da duban ƴar tasa,  tabbas ko kaɗan bayason tuna irin tsananin wulaƙancin da dangin Maryama sukayi masa, wato dangin mahaifiyarta kenan, sun tozartashi, sun kuma wulaƙantashi duk dan kawai saboda  bashi da kuɗi.
Cikin sanyin murya yace.
"Dangin mahaifiyarki ba suƙita don komai ba saidan aurena da tayi,  mahaifiyarki tasoni duk da kasancewata talaka,  takasance itaɗin kyakkyawar mace ce, don kuwa ko acikin sauran ƴan uwanta na shuwa arab, samun mai kyau kamarta sai an tona, asali mahaifiyarki ƴar garin Maiduguri ce, sannan takasance cikakkiyar shuwa arab,  awannan lokacin shuwa arab basa yarda su auri kowani namiji sai inyakasance daga cikin danginsu ya fito, idan kuwa har takai ga wani bare zasu aura tofa sai ya tabbata cewa shi ɗin mai kuɗine na gaske,    kamar yanda kika sani talaka baya zama akoda yaushe yana cikin fafutukan neman na kansa, sannan yakan iya tsallakawa yabar garinsa ya tafi wata duniya ta daban domin samun abun da zai rufawa kansa asiri, hakanne takasance agareni, inda nayi ƙaura daga garina na tsallaka zuwa garin Maiduguri dan nanemo kuɗi, zuwana Maiduguri shi ya haɗani da mahaifiyarki, inda soyayya mai ƙarfi tashiga tsakaninmu, ko kaɗan bata ƙyamaceni wai dan ina matsayin talaka ba, tana sona fiye da yanda nakesonta, hakan yasa bata sauraran kowa idan bani ba, koda gidansu suka nemi aurar da ita saita bayyana musu kan cewar tana da wanda takeso, sunyi baƙinciki sosai saboda sun so ta auri tsatsonsu, koda sukace takowani su ganni, sai batayi ƙasa a guiwa ba wajen sanar dani, zuciyata cike da fargaba haka na shirya don zuwa gidansu,  sam iyayenta da ƴan uwanta basu taɓa kawowa cewa da talaka take soyayya ba, saboda su atunaninsu wani hamshaƙin mai arziki zata kawo musu, ko kusa basu kawo cewa kamar yanda take da kyau zata iya tsayawa sauraran talaka kamarni ba, haka naje gidansu zuciyata cike da fargaba, koda suka ganni sun cika da baƙinciki haɗi da takaici, nanfa sukayi rantsuwa akan cewa ko mutuwa zatayi bazasu taɓa yarda ta aureni ba,  sunƙirani da maƙasƙanci, mafataucin talaka, sunƙirani da baƙauye, kuma marar ilimi, saboda kwata kwata ni banyi karatun boko ba, saidai kuma bankasance jahili ba saboda nayi karatun islama, dayawan mutane sukan ɗaukan mutum jahili don kawai baiyi karatun boko ba, bayan azahirance kuwa babu jahili sama da wanda baiyi karatun addininsa ba, ko kuma wanda yayi sani ya kuma take sanin,  haka suka ƙaremin cin mutumci da cin fuska, suka kuma gargaɗeni dana fita daga cikin rayuwar ƴarsu,
soyayyar da Maryama mahaifiyarki kemin tana da matuƙar yawa Zieyaderh, haka take wuni take kwana tana kuka, sannan takan hana cikinta abinci, ta kuma hana kanta sukuni duk dan saboda soyayyata, burinta shine iyayenta da ƴan uwanta su aminta ta aureni, sam sukuma idanunsu ya rufe, basaji aransu cewa zasu bari ta aureni, abu kamar wasa haka ta dinga rashin lafiya,  damuwa sukayi mata yawa, sosai tashiga halin tashin hankali,  ganin abun nata yayi tsamari ne yasanya suka ɗauki mummunan fushi da ita, mahaifinta da kansa ya zauna yace mata, tunda ta dage dole saini zata aura shikenan taje ta aureni amma tasani bada sa yawun bakinsa ba, saidai taje can wata uwa duniya aɗaura mana aure, sannan kuma daga ranan da aka ɗaura mata aure dani tasani babushi babu ita, komai yafaru da ita kada tazo masa gida, haka ma ƴan uwanta kowa yace babushi babu ita,  giyar soyayya dake ruɗan zuciyarta yasa tace ta amince, saboda ita dai burinta aduniya bai wuce zama dani ba,  haka tana kuka ta baro ƴan uwanta,  anan cikin garin na Maiduguri mukaje wani masallaci inda nasanarwa da limamin masallacin kaf abun da ke faruwa,  sam limamin baiyi ƙasa aguiwa ba yatara jama'arsa inda yace nabiya sadaki, nan nabada sadakin aurenta naira dubu goma shabiyar aka ɗaura mana aure, tabbas limamin yayi hakane saboda yana gudun mu faɗa halaka, saboda mafi akasarin masoyan da suka tsinci kawunansu a irin wannan yanayi,  sukan faɗawa cikin halaka aduk sanda akace an hanasu auren juna, baya ga kuma suna matuƙar son juna.
Haka aka ɗaura mana aure nida mahaifiyarki inda kaitsaye na wuce da ita ɗan ɗakin dana kama wanda ciki nake kwana, kwananmu biyar a Maiduguri naji gaba ɗaya bazan iya zaman garin ba, hakan yasa natattara ƴan abubuwana, muka taho garinmu Saminaka kenan,  tundaga kan neman auren mahaifiyarki har kama daga kan auren mu babu wani mutum ɗaya a dangina dana faɗawa, koda muka dawo Saminaka iyaye da ƴan uwana suka ganta nakuma gabatar da ita amatsayin mata, shikenan kuma tashin hankali yasoma, tsantsar tsana dangina ke nuna mata, babu ma kamar ya mahaifiyata,  sam basa sonta, acewarsu wai ita kaɗo ce baikamata ina cikakken fulani naje na auro musu ita ba,  auren ma kuma wai ni nayi gaban kaina, haka muke rayuwa watarana daɗi watarana akasin haka, awajena kaɗai Maryama kesamun soyayya, kowa bayasonta, ƴan uwana kyararta suke, har takai ga tsoron shiga cikinsu take, ahaka muka shafe shekaru huɗu da ita, acikin waƴannan shekarun babu wani ɗan uwanta guda ɗaya daya nemi sanin inda muke, sau dayawa nakan isketa tana kuka wanda na tabbata kukan nan na kewar ƴan uwanta ne takeyi, saboda akwai shaƙuwa mai kyau atsakanin su, wanda kuma ƙaddararren aurena da tayi ne ya raba hakan,  tsana da tsangwaman da ƴan uwana keyi mata ya ƙarune alokacin da muka shafe shekaru huɗu   sukaga babu alaman ciki atattare da'ita, nanfa bakin kowa akanta yake kowa sai yana ce mata juya,  sam mutane sukan manta cewa haihuwa da rashinta duk na Allah Ne, sannan Allah Yakan iya tawayan bawa ta kowani fanni, dayawan mutane ƙarancin ilimi da tunani kesa suyin gorin haihuwa, sun manta  ita haihuwa Allah Kan bawa wanda yasone ya kuma hana wanda yaso, hakan kuma bawai yana nuni da cewa Allah Ya hanaka don baya sonka bane, wataƙila hanakan dayayi shine mafi alkhairi agareka, kuma dama shi Allah Baya hana bawa abu dan haka kawai, saidai idan abun ya kasance ba alkhairi bane agareka, kuma komai na duniya yana da lokaci, sannan ƙaddara tana yawo akan kowa,  bayan munshafe shekara huɗu da ƴan watanni Allah Ya azurtamu da samun ƙaruwa, tahanyar bawa Maryama ciki, nayi farinciki sosai, duk da kasancewar awannan lokacin inacikin wani hali na takurar rayuwa, ma'ana talauci yayimin  tsanani, munzauna da mahaifiyarki lafiya koda sau ɗaya bata taɓa ɗaga muryarta akan tawa ba, munyi zaman daɗi da ita, takasance mace me tsananin biyayya da haƙuri, kana takasance me kyakkyawar zuciya, da kuma kyawawan halayya, takanci duk wani abun dana kawo mata komai rashin daɗinsa, aduk sanda bansamo ba kuwa takanyi haƙuri taɗanyi ƴan dabarbarunta wajen ganin tasama mana abun da zamuci,  sosai tasha wahala wajen rainon cikin da ke jikinta, kusan kullum bata da lafiya, amma haka take jurewa."
Ɗan numfasawa yayi tare da sanya hannu ya dafe kansa, zuciyarsa cike take da tsananin danasanin da yayi, haƙiƙa yabiyewa son zuciya, da ruɗin shaiɗan wanda yakaisa ya baro, ci gaba yayi da cewa.
"Cikin Maryama nada wata 5  nawayi gari da wani irin hali, wanda har kawo yau bansan meyasa halina ya canza ba, saidai nasan cewa hakan ma yana ɗaya daga cikin Ƙaddarata, hakanan nakejin wani irin masifaffen son ƙara aure ya shigeni, har takai ga inaji ajikina cewa idan banƙara aure ba hankalina bazai taɓa kwanciya ba,  wallahi nayi rantsuwa Maryama bata taɓa ƙuntatamin ba, hasali tanayimini biyayyya, sam kuma batacancanci zama da kishiya ba, amma saboda hali irin namu na maza hakanan naji ina sha'awar zama da mata biyu, duk da kasancewar bani da kuɗi, saidai dama ance ƙarin aure ajininmu yake mu maza, koda ana zaune lafiya, ko ana tashin hankali idan mukaso sai munyi,  haka naje na jajiɓowa kaina auren Ma'u,  babu wani fargaba bare ɗar haka nazo na tunkari Maryama da batun ƙarin aurena, ko da sau ɗaya banji tausayin halin da zata shiga ba, gashi lokacin da ciki ajikinta, sannan bata da kowa wanda ya wuce ni, akaina tabaro iyaye da danginta, ta zaɓeni sama da kowa, halacci take buƙata agareni akullum bawai butulci ba, amma kuma saidai me zuciyar ɗan adam bata da ƙashi, idanuna sun rufe ƙarin aure kawai nasa agaba, hakan yasa nadaina bata wani ingantacciyar kulawa,  ƴan uwana kuwa dama basonta sukeba, jin batun ƙarin aurena kuwa yasa suka cika da murna, nan fa suke ta yada mata haibaici, ita dai haka take rayuwarta sam bata tanka musu,  koda damuwa yayi mata yawa, saidai ta roƙi Allah Sassauci ko kuwa tashiga ɗaki ta ɓoye kanta tayi kuka, daga bisani kuwa tayi murmushi ta share hawayenta, saboda tasan ƙunci baya taɓa dauwama acikin rayuwar ɗan adam, dole watarana sauƙi zaizo.
Anyi bikina da Ma'u lafiya lafiya, inda na gina mata ɗakinta na laka agefen na Maryama,  satin Ma'u ɗaya agidana ta fara bayyana wasu halaye, sannan lokaci ɗaya yazamana inajin mugun shakkanta, idan tace eh bana iya cewa a'a, haka take juyani son ranta, saikuma taga dama nake kula Maryama.
Akwana atashi cikin Maryama ya cika wata tara da sati biyu cif, awata rana ta jumma'a ne nakuda ya tashi mata, rashin kuɗi yasa ta haihu agida, cikin iko da jin ƙai irin na Ubangiji kuwa ta haihu lafiya, inda ta haifo ƴarta mace,  wannan ƴar bakowa bace face ke Zieyaderh, haka Maryam tayi jegonta cikin rashin jin daɗi, don kwata kwata nadaina kulawa da ita, saudayawa takan sa kanta aɗaki tayi kuka sosai,    sanja halina danayi yasa gaba ɗaya ta rame ta fita hayyacinta, nikuwa ko ajikina, haka nake rayuwa ta da Ma'u, inda komai take buƙata inayi mata, tsananin son zuciya irin tawa yasa na manta da halaccin Maryama agareni.
Haka rayuwa take tafiya babu dadi, aɓangaren Maryama don ma saina ga dama nake shiga ɗakinta, haka take rainonki cikin so da ƙauna, sannu ahankali kike ƙara girma, yayinda kammanninki da Maryama ke ƙara bayyana, harma takai ga kinaso ki ɗarata fari da kyau,   sam namanta da wani haƙƙinku ko nauyinku dake kaina, rayuwata kawai nake gaba gaɗi, ɓangaren Ma'u kuwa kullum ƙara ganin ƙimarta nake, yayinda ita kuma takemin duk wani abun da taga dama,  tun kina ƙanƙanuwa ban baku kulawa keda mahaifiyarki ba, bansan meyasa zuciyata tazama butulu akan halaccin da mahaifiyarki tayimin ba."
Hawayen da suka cika idanunsa yayi ƙoƙarin shanyewa tare da cewa.
"Har mahaifiyata  ta rasu batazama mai ƙaunar Maryama ba, haka ƴan uwana suka dinga rasuwa da ɗai ɗaya,   akwana atashi asaran me rai, haka Maryama ta rasu ban zama mai kyautatawa agareta ba, sannan ko bayan rasuwarta da ƴan uwanta suka zo, sun nuna tsantsar tsana akaina saboda acewarsu talauci da zaman ƙuncine yayi ajalinta, inda suka barmini ke don sunce ke jininace sukuma bazasu karɓi jinina ba, har kawo yau kuwa basu sake nemanki ba, bankuma ƙara jin labarinsu ba, saidai akwai yayan mahaifiyarki Alhaji Ahmad Rufa'e wanda yake cikakken ɗan kasuwa, kana kuma babban  ɗan siyasa, shine ma wani lokaci nake ganin fostan sa, amma bayan haka har kawo yau babu wata alaƙa dake tsakanina dasu."

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now