Chapter 27

12.2K 1K 83
                                    

*SOORAJ!!!*

*Written By*
phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*

*WATTPAD*
@fatymasardauna

#romance

(🌺I'm really proud of you my Wattpad fans, i felt happy with the way you are commenting and voting my work therefore I dedicate this page to you🌺)

*Chapter 27*

Kauda idanunsa gefe yayi tare da ɗauke duk wata annurin dake kan fuskarsa. Ziyada dake tsaye tsaye still akansa cikin wata sarƙaƙƙiyar murya tace.
"Kayi haƙuri....ban...kula bane!"

Bai juyo ya kalleta bama bare tasa ran zai tanka mata, saboda haka ta ɗanja da baya tare da nufar hanyar fita da ga garden ɗin, gaba ɗaya jikinta yayi sanyi wasu ruwan hawayene suka cika idanunta, itakam batasan me yasa tazama wawiya har haka ba, sam batasan meyasa dazaran abu yashiga tsakaninta dashi take saurin kuka ba, da wannan tunanin ta isa ga babban ƙofan da zai sadata da falon Ummu, hannayenta tasanya ta share hawayen dake kan fuskarta, sannan ta buɗe ƙofar tashiga.

Shikuwa Sooraj tunda yakawar da kansa gefe baisake koda ƙwaƙƙwaran motsi ba, lumshe beautiful eyes ɗinsa yayi tare da maida kansa jikin kujeran, daddaɗan iskan dake hurawa acikin garden dinne ke ratsa ko ina na jikinsa, hakan yasa yaji zuciyarsa ta ƙarayin sanyi.

Zieyada kuwa atare da Ummu suka haɗa Mango juice, babban jug ɗin da mango juice ɗin ke ciki Ummu ta bata tace tasanya a fridge, koda tasanya mango juice ɗin acikin fridge kaitsaye ɗakinta ta wuce, faɗawa kan gado tayi tare da lumshe manya manyan idanunta, da sauri ta ware idanunta tare da tashi zaune, hannayenta tasanya duka biyu ta murza eyes ɗinta, wani irin ƙaton ajiyar zuciya ta sauƙe alokacin da ta fuskanci cewa gizo ne idanunta ke mata, bawai shiɗin bane, wani irin yaar taji ajikinta sakamakon tunowa da cikin kyawawan idanuwansa da tayi, tabbas idanunsa kaɗai sun isa rikita duk wata ƴa mace, matuƙar zata kallesu, wani irin sirrin kyau ne ke ƙunshe acikin idanunnasa, aduk randa tsautsayi yasanyata kallon cikin idanunsa ji take kamar zata suma, wasu abubuwane ke yawo ajikinta yayinda takejin kanta kamar wata wawiya, eye balls ɗinsa tamkar magnet ne acikin nata idanun dake matuƙar zautar da ita, wani irin murmushine ya bayyana akan fuskarta wanda bata san ma tayi ba, sakamakon tunawa da kyakkyawar fuskarsa da tayi.

"Yana da kyau sosai!!"

Tafaɗa abayyane cikin wata irin murya me sanyi. "Ko abacci ma kyau yakeyi, shi komai nasa me kyau ne!!!" Tasake faɗa tana me murza ƴan yatsun hanunta, itakanta batasan maganganun da take faɗa suna fitowa fili ba, gaba ɗaya ashagalce take, fararen ƙafafunta ta zuro ƙasa tare da tashi tsaye, direct wajen window ta nufa, ɗan yaye labulen window'n tayi tare da soma bin ko ina dake cikin compound ɗin gidan da kallo, idanunta ta tsayar asetin ƙofar shiga garden ɗin, dai dai lokacin yafito daga cikin garden ɗin hanunsa riƙe da wani green apple, tafiya yake kansa tsaye yayinda skin ɗinsa keta walwali kallo ɗaya zaka masa kasan hutu da kudi sun zauna masa, tundaga wajen da take tana iya hango yanda tarin suman dake kansa ke sheƙi, gashi ya kwanta luf luf tamkar sajen dake kwance akan fuskarsa, bata taɓa ganin wani irinsa ba, shi na dabanne ko acikin maza, hannunta takai ta dafa glass din dake jikin window'n, fuskarsa kawai take kallo, akullum tana mamakin yanda yake rayuwarsa babu annuri akan fuskarsa, koda yaushe haka yake baka taɓa ganin dariyarsa, kafun kaji maganarsa ma wahala ne, shi komai nasa is difference, Maganan aurensa ne ya faɗo mata lokaci guda ta marerece fuska tare da ɗan taɓe soft lips ɗinta. "Wace zata aureshi?" tambayar da tayiwa kanta kenan azuci, amma sam batasani ba har sautin maganan yafito fili. Soft lip ɗinta na ƙasa taɗan tsotsa tare da soma karyar da yatsun hanunta, idanunta ne sukayi raurau kamar wacce zatayi kuka, ɗago kanta tasakeyi da niyan kallonsa, amma kuma saitaga kome kama dashi babu awajen, sake labulen tayi tare dakomawa kan gado ta zauna. "Mene nawa? Meyasa nake tambayar kaina abubuwan da basu shafeni ba? No wannan ba halina bane kawai sharrin zuciya ne!" Tafaɗi haka cike da tuhuman kanta, domin sam tasan tunanin rayuwarsa ba huruminta bane. Remote taɗauka tare da kunna ɗan madaidaicin tv plasman dake ɗakin, tashar MBC Bollywood takamo inda tasamu suna nuna film ɗin Sushant Singh da Kriti Sanon wato Raabta, yanayin film din sosai yaɗauki hankalinta musamman yanda taga suna wata kalan rayuwa a daji, sam saita manta da tunanin komai ta bada hankalinta ga kallo.

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now