CHAPTER 3

4.2K 261 18
                                    


Sanda ta kara kusan 5min sannan ta leko da kanta duk ta hada gumi saboda rashin gaskiya

Saukan rankwashin da tajine yasa ta sankare a wurin na wani sakanni

durkushewa tayi a wurin tana tutturo baki kamar zai taba kofa

baba ne yace rufi min baki kamin in kara miki,
Maza tashi

Mikewa yayi tana zuzzunburewa tace haba baba ko Dan wannan rankwashin da kake samani kamar abinci Ba dole na KASA kokari Ba kana taba min CPU na bakasan Cewa itace masarrafin Dan Adam ba?

yace yimin shiru kamin in da'da maki wani yar kaniya kawai,me kwakwalwar kifi Allah dai ya bude maki wannan toshesshiyar kwakwalwar taki.

kuka ta fara yi tana buga kafa ni Gaskiya baba kwakwalwata ba a toshetake baaa😭 inna tace ni yimin shiru karki taramin makwabta ehe

murya ta kara baba yace bari kiga ikon Allah mikewa yayi ya dauko sanda.
yanda Kasan Anyi ruwan sama an dauke tsit ta shanye kukan da takeyi tana tsitstsilla idanu tare da sheshsheka baba yace banson jin sheshekar nan. Ki natsu bari inga tsiyar da kika shukowa mutane wannan karan.

Mutum bashida aiki sai fada ni Nayi mamaki ma yau kusan sati 2 ba'a kawo kararki Ba.
Turo baki tayi duk yasha mai sai yalki take tace yo ai dannayi mafarkin na mutu ne kuma ko yanxu ma Ba fasawa nayi Ba.

Kallonta baba yake har ta ida maganan ta already ya Ciro takalmi Dan haka ya lafta mata.

papers din ya fara dubawa yaga subjects 2 ne takeda A amma saura Wai sai a slow saide rubutun nan war inka gani zaka dauka wata Dr ce tayishi sai ka karanta ne kaji Kamar kayi kuka.

takaicin rashin kokari na diyartasa abar kaunarsa ne ya taso mai.

Kansa kawai yake girgizawa saboda takaici bazai musaba Idan akace masa Dan primary five ma yafi yar tasa kokari.

Tsawa ya daka mata ke zonan !
Simi simi taje ya kalleta sannan yace yanxu ke ahakan zaki tafi makarantar gaba?ki Duba fa gododuwar banza da wofi. Murmushi tayi
inna tace Allah zanci mutuncinki ana miki fada kina dariya saboda kin daina mutane ko? Tace Toh Toh Toh ni inna me Nayi ? Dakuwa inna ta mata tace kaniyarki kikayi

tace to yi hakuri bazan kara Ba shikenan aiko?yauwa inata Dan Allah ki siyan awara?harara inna ta banks mata tace ba'a siya dinba
Baba dake jinsu ya tattare takardun yana cewa ace mutum anmai repeat har sau biyu amma bai gyara ba nasan duk ajin keda zaliha kun fisu girma amma kanku Kamar kifi har gara ita akanke.
antara dakikai biyu a aji daya bakuda aiki sai ciye ciye kuma da kunada kokarinku tunda kuka fara Hulda da wannan fatiman shikenan lamuranku ya tabarbare.

tace toh Ba kai kake Bani kuddin Ba? Kuma ai fatimamma sun Koma kano.

Yace au haka zakice?

Inna tace kaga malam rabu da ita kar hawan jininka ya tashi
Mika ma innatakardun yayi yace jeki ajiye min adakin ki Dan in ina ganinsu takaici ne zai kasheni

ni inanan ina fafitikar biya miki WAEC kan arufe amma naga alama asara zanyi

Zama kusa dashi tayi ta Washe baki tace baba kawai ka barni in fara aiki a gidan abinci Dan Gaskiya ni karatun bokonnan sai a hakali bazan maka karya in batama lokaci da dukiya ba yasin dakyar in zan hada ko credit 4 me kyau a wannan WAYES din
Yasin Gaskiya kake fadi kwakwalwartawa a to she take nakifinne maganarka Ba karya.

Abin yaso bashi dariya amma sai ya Girgiza kai

yace ai ga irintanan ana WAEC kina WAYES dubaki ko ajikinki Yan ajinku zasu makarantar gaba amma ke oho ko ?kinacewa inbarki Kiyi aiki a gidan abinci

Bakiji abinda ya faru da salma Ba ko 'yar gidan malam ado ?tana gidan ubanta ma ba'abarta Ba balleke budurwa kin tallata kanki a gidan abinci
Nan ya labarta musu abinda ya samu salma sannan yace Suma suje suyi ta'aziya.
Inna kam salati take harda kwalla tace kai duniyar nan Ba imani.

Minal ko mikewa tayi tana bubbuga kafa tace Toni baba idan ma bazaka iya barina inyo aikin Ba kawai kamin aure ka huta
Ai da gudu sukayo kanta ba shiri tayi waje tare da Jan mayafi akan igiya.
Baba yace da shegiyar kazanta ma wa zai soki?ja'ira yar kwal uba
Inna tace abita da addu'a da fata na gari kawai.

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Wakarta takeyi tana tafiya ta hango murtala da wani abokinsa mai kawo masa ziyara babba yake kowa?waishi a dole Santa yaje. Zukar sigari suke Suna busa abarsu.

Tsayuwa tayi a wajensu tace anya murtala kanada hankali kuwa kullum kayita busawa 'ya'yan hanjin ka hayaki Kana biyewa wannan sha katafin?

Dariya ya bushe dashi kamin yace minal kenan ai na Fiki hankali ma. Babba yace ke yar shila karki kawao mana raini Anan fa ko kinga sa'anki ananne?

Bata kulashiba taci gaba da yiwa murtala magana da tayi:
Dalla tafi can wallahi baka isa ba kayi kadan.

Kaikuma ta nuna babba da yarda kama daina nuna ka sanniwata kila ma sanadinka ne samari basa kulani to ka kiyaye ni.

Babba ne ya bushe da dariya Hahaha sannan yace kinfaiyi kwantai babu mai sonki sai yawo a unguwa

Dariyar takaici ta kyalkyale dashi kamin tace kaji banza botorami, yo da na Sauri miji irinka a gara na zauna Ba aure sha katafi kawai. Kuma in mijin agidan uban mutum ake rabawa sai ya hanani.
Murtala yace Ke yarinyannan zanyi maganinki fa, abokin bawa kuke fadawa maganar banza?

Minal tace da wacce itaciyar zakayi magani na? Kasan ni annobace da banida magani. Nan gani nan bari dumamen mayya in fada ma.

Murtala yace kinci darajar babanki mutumin kirki ne kuma banason rigima yau da kinga yadda ake balla kafar yarinya. Tace yo inba tsoro Ba kamaso mana wallahi kaga yadda na fito dinnan babu mutunci.... Mtsw ni banma da lokacin Dan shaye.

Tafiya tayi abunta,babba Wanda ya tsaya yana kallonta sai alokacin yace kai murtala babe dinnan tayi aradu. Kaga jiki me kyau kuwa........

Tsaki murtala yaja kamin ya tashi yabar wajen yana gunaguni akan irin yadda babban ya nuna halin ko in kula gameda abinda minal din tamai.

27th April 2019
Show some by
voting,
Liking,
Sharing
And
Commenting

Mzz untichlobanty💕

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now