CHAPTER 91

1.9K 131 54
                                    

RECAP

Tace wa ? ni shegiya inji Dan daudu kawai ku cireni. Zayya da sahla ne suka rike hannu yayinda mummy da minal suka rike kafa akayi sama da ita a lokaci daya.

Tace la ha'ila ha illallahu shikenan! Kun kun kasheni. Waiyo Allah sun kwaye min mazaunai.

CONTINUATION

Mummy ne ta fado dakin su umma hani duk a rikice tana fadin umma hani zo ki taimaka kar yata ta tagaiyara,umma hani tace ni kuma ranki shi Dade? nida bani da kwakwalwa bansan me nake ba ta ina zan temaka wa wayaiyu yan boko abin tausayi mummy tayi tace haba ke kuwa AI an zama daya ko ba haka ba? Ki mance da baya ai duk rashin sani ne kinsan ance yafi dare duhu. Zo muje kinji.

Haka aka dauki ayush aka kaita daki aka kwantar da ita ruf da ciki. Mummy ta nemi ointment (man da za'a shafa ma ciwon) ta rasa shi sama ko kasa batasan su yazeed bane suka boye.

Umma hani dukda batasan nake wakana ba tasan aikin su yazeed ne tace bari na hado wani abin na gargajiya a shafa Mata kamin gobe a siyo na malam bature. Ayush cikin kuka tace yi sauri Dan Allah kamin ta share majina.

Minal ne tace bara inje in taimaka Mata, mummy tace toh yi maza yar albarka. Umma hani tana shiga kitchen ta hau dariya tace kai wannan Anya kuwa ba hadashi akayi ba ? Dan baiyi kama da tsautsayi ba. A bayan ta taji minal tace aikin mu ne. Juyowa tayi adan tsorace tace hajiya barka dai minal kam zuwa tayi ta rungume ta tace umma hani nice fa me zaki wani ce mini hajiya. Gaggaisawa sukayi sama sama umma hani har da kwallar ta. Minal tace idan kin hada maganin ki saka wannan a ciki. Umma hani tace menene shi? Minal tace kallesu da kyau mana barkwano ne da gishiri sai kuma aboniki. Wannan kuma kiyi a hankali dashi domin karara ne wato garin a Sosa. Kawai kwabasu zakiyi da manja

Toshe baki umma hani tayi Dan kar tayi dariya tace Allah ya biyaku. Wannan aiki naku yayi daidai idan kuma numan taimako ko na menene indai zan iya zan muku. Minal tace mun gode! Umma hani tace yi wa kai ne.

Kawowa sukayi suka bawa mummy umma hani tace idan ya fara zafi kadan yana aiki kenan sannan yakan yi ma wasu kaikayi toh kar ki sake ki Sosa.  sannan kowa ya fice kafa kunne sukayi a bakin kofa.

Ayush ta Dan hakura ta dena kuka har bacci ya fara daukarta taji an saka Mata wani Abu kamar acid babu shiri ta Mike tsaye kewaye dakin ta fara a haukace ta ma kasa komai saboda azaba. Sanda tayi kusan minti biyu sannan ta daka tsalle ta saki ihu. Kaikayi take Mata ba halin Sosa wa. Kai ganin abin ba sha yasa ta fara sosawa sai jini. Mummy tana karki Sosa aiki yake itako fadi take bazaki gane bane. Ya ge rigarta tayi ta shiga toilet kamar mahaukaciya tana Sose sose ta shiga ban daki. Kunna ruwa tayi taji ba sauki lamarin gaba yake kawai ta fito zata fice tsirara mummy ta rikota ta saka Mata hijabi.

Da gudu su yazeed suka buya itako ta Fito sai kitchen ta dauko cokali tana sosawa yana jini umma hani tace kai har ta ban tausayi wallahi. Minal ne tace baki San me tayi ba shiyasa kike fadin ta baki tausayi.

Daki suka tafi sukayi kwanciyar su sunajin daidai a ransu. Ayush ko yanda taga Rana haka taga dare. Gashi bazai yuwu ta zauna ba in ta kwanta kuma azaba. Gaba daya ta koma mahaukaciya a kasa da awa 24.

Washe gari ambulance yazo ya dauke ta yayi asibiti da ita anan su yazeed suka sami damage kwashe allauran da take ma zakiyya sannan suka canja da na magani.

Zayya da sahir ne suka fita shopping tunda gobe zata koma makaranta dama auren minal tazo da weekend kuma sai itama aka daure ta.
Yawanci kayan sawa ne suka sissiyo nata da nasu halsey. Chanji aka basu amma babu naira 50 sahir yace a barsa sai cashier tace ba matsala tunda tafe yake da kanwarsa kuma ansan Mata da cin chewing gum su dauki daya. Zayya ne ta harari matar tace nayi kama da kanwar sa? Sahir ya janyota tare da yiwa matar yake yace matata ce sannan ya janyota suka wuce. Daukan strawberry flavor sukayi sannan suka tafi gida.

Direct dakin sahla ta shiga babu ko kwankwasawa ta samu safwan yananan gashi yanayin su da matsala hakan yasa ta fice da sauri kamar wata shashasha tana basu hakuri. Sosa kai take Dan kanta ya daure har ta shiga part din ta. Ganin idan taci gaba da tunani wahalar banza zata sha yasa ta fada kan gadonta tana mai sauke ajiyan zuciya bayan ta ajiye ledojin a kasa.

Yazeed ne ya tare sahir kamin ya haura sama yace sahir zo zauna mana. Zama yayi yace daddy ina wuni? Yace lafiya ya kuka kwana jiya? Yace lafiya Alhmdllh yazeed yace toh yayi kyau daga ina kuke ne? Yace wallahi mun Dan je siyo abubuwa ne gobe zata koma makaranta. Yazeed yace yayi kyau da fatan ka shirya ma next plan ? Sahir yace na shirya yazeed yace naga kana kallon sama bi matar ka bazan rike ka ba dariya yake ya tashi ya haura.

A daki ya sameta kwance akan gado yace wifey ya naga kinyi jungum jungum? Juyawa tayi tace karma kayi tunanin ni zan yarda. Yace me fa? Tace barshi kawai a wuce page din.
Yace oya dauko mana kayan muyi arranging a akwatin ki.
Dauko wa sukayi suna jerawa ta dauko chewing gum din boyewa tayi a bayan ta ta masa gwaliyo tace bazan baka ba.

Yace yarinya kinyi kadan kokarin kamawa yayi ta kautar cuku cuku suka fara yi kamar wasa Abu ya koma dambe sai dariya take.  Gudu suka fara yi a tsakiyar dakin wayarta yayi ringing tace ka tsaya a inda kake idan ka matso ka kwace kayi cuce kuma ka zama ragon namiji.
Tsayawa yayi ta dauki wayar sahla ce ke kira tana dauka, ihu ya daki kunnenta. Cikin masifa amma a wasa sahla tace sis kede anyi yar wulakanci shine kika fado min daki babu sallama babu knocking ko? Yanzu gashi kinsa ya fita ma. Zayya tace iye sannu Sara me farar takashi gashi blue gashi jaja jaja.
Wai ke me miji dadin abun nima inada shi dallah in bakida Abin fada zan kashe waya ta. Sahla tace AI ko baki fada ba ansan kinada miji ji yadda kikewa mutane haki aci dadi lafiya. Zayya tace ba haka bane ba fa kawai..... sahla tana dariya ta datseta ta hanyar cewa kawai me? Sis babu boye boye sai anjima.

Zayya tace kash anyi banziya wallahi. Sahir ne yace gwamma kin shanyani anan fa. Kamin ta ankare caraf ya kwace yana shirin budewa idonsa ya fada kan wani rubutu....
Mika Mata yayi yace kinsan ni mijin kirki ne gashi na baki amma kar kici sai tare da kawayenki gobe. Tace me yasa yace saboda ki zama kawar kirki. Karba tayi ta sumbaci kumatunsa tare da shafa kansa tace good boy sanda bata ma lura da tayi hakan ba taci gaba da jera kayan ta.

Yana fita yayi dariya yace yan Matana aci chewing gum lafiya yana Mata dariyar mugunta. Itama a bangaren ta yana ficewa tace sai kace ban sanka ba kawai zan yarda cewa ka hakura. Hmm nasan so kake kabi dare ka cinye dan haka gadi zanyi sannan tayi ma kofar gwaliyo.

A asibiti kuwa........

Shin ok me yasa sahir ya fasa cin cingam din?

ANAN ZAMU DASA AYA FAH. A BAYA NACE ZAMU TSAYA DA UPDATE HAR SAI BAYAN RAMADAN AMMA SAI WASU SUKA NUNA CEWA PAGE DAYA BAZAI HANASU IBADA BA KUMA SUN KASANCE SUNFI YAWA FIYE DA WANDA SUKE GANIN YA DACE A TSAYA HAKAN YASA NACI GABA AMMA UPDATE SAI BAYAN KWANA UKU UKU.

DON'T FORGET TO VOTE, SHARE, COMMENT AND FOLLOW ME.

miss untichlobanty 💕

26th April, 2020.

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now