CHAPTER 41

2.8K 188 17
                                    

A haka har suka iso sabon gidan iyayen minal, itakam ta rufe idonta kyam sai laftawa lukman da yazeed din kwandon Allah ya isa take a zuciyarta Dan gani take hada baki sukayi domin suyi mata mugunta.

Yatsa yazeed yasa ya dungure mata kai yace ai saiki sakemin Riga ko? Duk kin yamutsa Min Riga sai kace na fito Daga filin kokuwa, ko jikin nawa ne bai isheki Ba?

Bude ido tayi da sauri tare da hade fiska ta zabga masa harara kasa kasa tace sai kace wani abin arzikin ne ajikinnasa.
Yazeed yace me kikace zaro ido tayi tace babu aranta ko Cewa tayi Wai wannan mutumin aljanine ?taya akayi yaji me nace?
Wani smiling yazeed yayi yace matar aljani muje ko?
Wani numfashi me karfi taja ta zaro ido tana kallonshi tama kasa motsi.

Tabe baki kawai yayi ya fice sannan ya miko mata hannu ganin kawai kallonsa take Kamar taga fatalwa yasa ya fincikota suka fara nufar cikin gidan hannu cikin hannu.

Kallonsan kawai ta cigaba dayi shikam gabansa yake kallo yana murmushi Wanda ya rasa dalili, Ashe luku ya Ciro wayarsa yana watsa musu photo dan Ba karamin kyau sukayi Ba Kamar sune Amarya da angon.

Juyowa yazeed din yayi Dan ganin kallon yaki ya kare aiko tayi saurin kauda kai tana kyafta idanu cikin jin kunya. Aiko lukman ya kara hasko su Wanda su duk abinda ke faruwa basusan anayi Ba.

Koda suka Shiga gidan dauke da sallamar su suka zauna. A lokacin minal ta lura gidan mai mugun kyau ne. Yaba kyawun gidan take taji wata murya wadda yayi mugun tsoratar da ita dan batayi tsammanin wannan muryar anan ba. Saurin kallon wajen data jiyo murya tayi aiko Ba karya kunnanta sukayi mata Ba tabbas innarta ce sanye da super mai kyau ta kashe daurin dankwali tayi haske sai murmushi take kamin tace wanake gani haka? babban bako dan albarka zuwa Ba sanarwa ? Allah ya taimaka akwai abin naka ba bari inkawo ma.
Ah ah kace min tare kake da malam lukumanu. Murmushi yayi yace wallahi inna tare Mike ina wuni?...... Nan suka gaggaisa inna tace malan lukumanu irin wannan babban Riga haka sai kace ango Sosa kai yayi yace wallahi daurin auren classmate dinmu zamu.
Inna tace ayya Allah ya Sanya alkhairi.

Ganin Kamar inna bata lura da minal dake sankare scan kuryan parlourn Ba yasa yazeed Cewa inna bakiga bakuwar ki bane sai lokacin inna ta juya aiko minal ta gani tayi kuri tana kallon ta.

Inna tace ja'irar 'yarnan kina kallona bako gaisuwa?minal kam mikewa tayi ta fara takowa wajen innar ga mamakinsu sai ta rungumeta ta fashe da kuka haka aka lallasheta tace inna banganeba innan tace kwantar da hankalinki wato.................

Nan tayi mata bayani duk yadda akayi sannan ta kallo yazeed din tace baka fada mata bane? Murmushi yazeed din yayi yana kallon kasa yadan gyara hularsa sannan yace wallahi dama surprising dinta nakeson yi.

Inna tace dakyau aiko ta sufarasu dayawa harda kuka.
Turo baki minal tace bafa safarsu bane suprise ne. Hararar ta inna tayi tace o ni 'yasu mai hali bata chanja halinsa, kice min bata chanza zani. To mike ki shige nan kofar ta bangaren hannun daman ki akwai firji cikin akwai sobo ki dauko. Acikin drawer akwai tray saman canter kuma akwai cup ki dauko musu Toh tace sannan ta mike ta nufi kitchen din.
Koda ta kawo so'bon suna sha inna sai hira suke da yazeed da alama sun shaku, minal kam abubuwan da suka faru da ita ayau Nada wuyan shanyewa lokaci guda.

Mikewa su yazeed sukayi Suna Cewa zasu wuce lokaci na kurewa,minal din kuma sai su tafi gidan bikin tare da inna tunda itama innar zata Kamar yadda tace.

Wajen suka fita inna tace bazaki raka mijin naki bane? Tashi tayi akunyace tabi bayan su koda lukman yaga ta fito mota ya Shiga yana Cewa bari in bada guri kar adaga mini hankali da rana tsaka.

Yazeed ne ya kalleta yana mai Daga gira alamun yadai?tace uhm dama so nake nace nago....

Yazeed ya datseta ta hangar Cewa in godiya zakiyimun ki barshi dan Ba irinta nakeso Ba tace to irin wanne kakeso yace zan fada miki Ba yanxu Ba. Dan tabe baki tayi sannan tace to Allah ya kiyaye sai kun dawo. Murmushin gefen baki yayi sannan ya gyada kai ya shigewarsa mota sannan suka wuce lukman na fadin wallahi sobon nan yayi yana hajiya dashansa yazeed yace dam inajin haushinka dan wulakanci shine bayan ka shanye naka ka dauki nawa ko?lukman yace afuwan mutumina santi ke dawainiya da ni,tsaki yazeed yaja yana mai kauda Kansa izu.

🌹 🌹 🌹 🌹 🌹 🌹 🌹 🌹 🌹 🌹 🌹 🌹

Abangaren ango Sulaiman Kam Sai murmushi take har yashiga dakin mahaifiyarsa cikin shirinsa na daurin aure nasiha tayi masa sannan tasa masa albarka domin kuwa Ba karamin so takeyiwa dan nata Ba cikin yara uku da Allah ya azurtata dashi wato;
Na farko Sulaiman mai shekaru 29, sai abdussalam mai shekaru 25,sai kuma fadeelah wacce take yar auta mai shekaru 17-18 kuma anfi saninta da deela ta zana jarabawarta this year.

Fita yayi ya nufi mota Inda abokansa ke jiransa domin tafiya wajen daurin aure.

Suna cikin tafiya sukayi realising ai birki bayaci nan hankali ya tashi salati suka somayi yayinda motar ke wujiga wujiga dasu akan titi kamin ta karasu da wani gini.

Allah sarki!cikin su Biyar da suka fito 2 ne suka rayu wato Muhammad da Ismail wadda akayi hospital dasu rai ahannun Allah amma ango da mutane biyu take suka cika. INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!
Allah taji kan musulmi.

Abangaren wurin daurin aure kam su ango shiru har 2:16pm.

Cikin gida kuwa mata sun cikashi dam Kamar lokacin bikin minal. Ana cikin shagali Amarya tasha kyau sai murmushi take black beauty akaji mai shela na magana Kamar haka: jama'a salamu alaikum, andaura auren malama zaliha usman da malam lukman shu'aibu akan sadaki naira dubu 80 bisa malam yazeed abdulmajeed umar amatsayin waliyin ango,kuma malam abubakar Yusuf amatsayin waliyin Amarya.

Cak kowa ya tsaya gidan yayi shiru bakajin Komai sai numfashi kamin kuma ya sake kacamewa da surutu masu tambayar Dama Ba Sulaiman zata aura bane ?nayi,Masu zagi da habaici Nayi,masu al'ajabi Nayi mai suma ma tayi nata wato Amarya.

Nan Yan daurin aure suka watse akayi gidansu Sulaiman domin jana'iza.

🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹

Abinda ya faru kuwa shine ana cikin jiran ango sai..........

Kubiyoni acikin babi na gaba domin jin abinda ya wakana

Shin kuna ganin lukman da zaliha sun dace ? Yaya zaman nasu zai kasance?

Don't forget to vote,comment and share with your friends.

Thank you.

Miss untichlobanty💕

12 November,2019.

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now