CHAPTER 25

3.1K 223 21
                                    

An daura auren minal da yazeed akan sadaki naira dubu 50,Yan uwa da abokan arziki NATA taya murna makiya ma na hassada

Allah ka barmana makiyanmu kodan su zama dalilin da zamuyi nasara. Imagine life without munafukai 'Allah barmana Ku Yan wuta😂'

Mom ta aiko da kayan abinci da abubuwan da za'ayi walimah Dan babu wani event da za'ayi. saboda abin yazo a kurarren lokaci ko mai wa'azi ba'a sami daman kira Ba.

Bayan la'asar akayi da mom Cewa za'a daukan minal around 5 pm inji ango(mom anya wannan magana kuwa zan yarda da ita?).

Hakan yasa aka fara shirya Amarya around 3:50 bayan Anyi sallar la'asar.

Liffaya mai kyau tasa wadda aka siyo mata awajen reemah's collection. Wani sarkan gold akasa mata Wanda yake na inna ne family necklace dinsu. Babbar ya ake bawa in za'a kaita dakin miji. Kuma ba'ayarda ka siyar Ba amma zaka iya upgrading.

Kyansa yananan Dan haka ba'amayi upgrading din Ba.

Dayawa daga cikin Yan makarantansu sunyi attending, ciki kuwa harda heedaya Muhammad da ma'ani yerima Wanda suke mutunci sosai.

Yan matan ne adakin minal yayinda aketa tsokananta itako sai cika take tana batsewa wai ita batason adinga zancen batsa a gefenta.

Hidaya ce tace Nide sake fuskannaki in gama kwalliyan yayinda ma'ani ke Cewa nikam yau sai na cika camera ta da hotuna, inajin ma inna sami dama zanje in karanta photography😉

Heedaya ne tace oh mude zamuzo muji ya aka Kare a Daren farko.

Harara minal ta ballo mata,aka fashe mata da dariya Ashe ta shaka, minal tace ko ma dai menene ni kar a tura ma kowa hoto na cikin kayan nan tunda kunga dai gashi na da wasu bangaren jiki na a bude.

zaliha tace kai Ku rabu da ita bari ayi Daren farkon wannan Cuno bakin da take duk zata dena saide muga mutumiyar ka an zama miji dadi

Alamun zatayi kuka muryanta yayi tana Cewa wallahi zaliha karki bari na kamaki shegiya yar.....

Innace ta shigo tace inkika karasa sainaci ubanki.

Tunda ake hirar bansa baki Ba ina zaune a gefe ina typing a wattpad dina saboda kar ace na fiya rashin kunya sai alokacin na sako baki nace "assha!inna kin bata goma boyar bata gyaru ba in ita batayiba aike kinyi"

Dakuwa tayimin tace ingo naki yar jakan uban yarinya da baki cau cau Kamar babba kodan kinganki cikin Yan mata shiyasa kika falle ko?kinsa niqabi kamar da gaske ashe dai.......shegiya Da I damu Kamar na Yan chaina

Kafin ta karashe nayi Sauri nace wallahi Nide Ba yar China bace ina turo baki,aiko inna tayi kaina na fita a 360 har inacin karo da mutum Ashe ma sakina ce da habiba (from the nemesis of sakina)yi hakuri kawai nace kamin na buya a zaure ina haki sannan na sauke niqabi na,na saka gilashi na.

Ciki su sakina suka Shiga aka gaggaisa kamin suka wuce domin mazajensu na jiransu.

Kanwar dad din yazeed aunty nafeesa da Umma habiba wadda take step paternal grandma ga yazeed sai kuma aunty nina Kanwarka mom Wanda suka iso yau da safe sune sukazo daukan Amarya tare da motoci 3 kacal saboda basuso bidi'an tayi yawa

Aiko nan aka fara tashin hankali minal fa da taga da gaske tafiya za'ayi da ita kirjinta ya fara lugude duk dadin da takeji taji babu shi ya tafi kawai sai ta fara hawaye wiwi Ba magana nanfa wattpad fans dinta sukayi CAA anata bata hakuri amma ina kukan karuwa yake tunba sanda sukayi sallama dasu inna Ba dasu baba da ya abubakar.

Inna da baba hawaye suke hankali kwance yayinda idanun yaya abubakar suka ciko da kwalla deeje Kam an jika gaban riga ma da hawaye da majina sai alokacin na lura da kwalliyar da tayi kominta yayi matching da kayanta hatta Jan baki da eye-shadow, da brows din duka blue ne. Abin dai sai kun gani. Nikam share kwallan da zai zubo min Nayi domin tausayi. Rabuwansu was heart touching haka aka kwashemu mu 10 aka kaimu gidan amarya.

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now