CHAPTER 84

2K 162 44
                                    

OH WAI YANZU COMMENT DIN MA AN DENA.

RECAP

Ido cikin ido suka fara nufo juna gaba daya daliban da suka taru suna kallo baya baya suka fara yi Dan sunsan yau za'ayi world war na 3.....

CONTINUATION

Naushi ya kawo Mata ta kauce, caraf tayi ta riko shi tare da basa one blow seven die. Haka dai ta hadesu duka su goman ta basu kashi.

Principal ne yazo kanshi ya bata sammacinta lokacin da aka dawo daga wasa.
Cikin takunta na maza ta shigo dakin taron Dan malamai gaba daya sun taru, cikin harshen turanci tace malamai sannunku sannan ta dauke kai.

Ajiyan zuciya principal Solomon ya sauke tare dacewa zayyana meyasa? Meyasa bakyajin magana ko kadan? Ke wace irin matamaza(tomboy) ce? Mun baki hutun hukunci (suspension) yadi Akirga,hukuncin Karin lokacin tashi (detention) kuwa yana cikin jadawalinki. Kinsani a Bisa ka'idar makarantan nan ba'a duka tunda international school ne Dan haka mun yanke shawara zamu mayar dake dayan branch dinmu Wanda babu musulmai,babu hausawa, babu yan kasarnan saide yan wata kasa.

Tunda principal din ya fara magana ta saka earpiece a kunnenta dan haka koda ya gama godiya tayi ta karbi paper da ya bata sannan tayi ficewarta aji ta koma ta zauna a kujerarta Wanda ke karshen aji sannan ta fara shirgar baccinta. Girgiza kai malamin yayi kamin yaci gaba da bada darasi.

Koda aka tashi sanda sukayi fada da shameela akan ta bata musu lokaci zayya bata ce kala ba sanda shameela ta gama zayya tace bana taba Mata saboda ragwaye ne sannan ta wuce abinta.

Suna dawowa suka samu kowa da kowa a parlour barka da zuwa aka musu mama na zaune a gefen daddy wato Alhaji mansur mainasara, yayinda aunty jalila ke hararan kanwar shameela wato nana saboda tayi roko.

Bushra aka tisa a gaba akewa fada akan yadda ta rufe ido Sam wai ita sai mai kudi zata aura. Ga yadda take wulakanta talakawa kuma hakan matsala ke haifar musu ita da minal.

Ko ina idan minal taje neman aiki sai ace ba ita bace tayi wulakanci a waje kaza ? Sai a koreta komin rantsuwar da zatayi, yayinda ita kuma bushra ake cewa an ganta a waje kaza da shiga ta mutanen arziki. Shiyasa kullum sai sunyi fada.

Daidai lokacin minal ta sauko tana sauri tace bye bye everyone (kowa da kowa ) ni na fita inada interview Alhaji mansur ne yace haba minal ni zakibi ta tawa da kin bari na miki hanya kin samu aikinnnan cikin sauki. Girgiza kai tayi tace no daddy nafiso insha wahala in Nemo da kaina zanfi daraja aikin. Murmushi yayi yace kuma hakane kinci wannan yar uwar taki ita ba aikin za'a nema Mata ba ko yi Mata za'ayi bazata karba ba nide nayi asarar kudin karatu . Mikewa bushra tayi tana fadin haba dady tunda wannan imposter (me satan kamannin wani) tazo gidan nan ka dena sona komai akayi minal, minal, minal,minal.

Dariya yayi yace yaro man kaza ai sai ki yi aure ko kinga ba sai kinganta ba balle ta baki haushi. Kema.. ya fadi hakan yana kallon minal ya kamata ki samu miji ki sake aure tunda dai a asibiti ance babu abinda ya samu kwakwalwar ki malamai ma sun duba ki ance ba komai ko akwai abinda kikeji. Tace a ah kawai de idan suna duba ni sai in fara ji na tuna komai da sungama kuma sai na sake mantawa gashi kuma ko nayi kokarin fada kasawa nake.

Ajiyan zuciya yayi yace Allah dai ta kyauta. Fitowa tayi sabir na labe domin ya tabbatar ba bushra bace Dan batason ko ganinsa tayi acewarta.
Ganin ya tabbatar minal ne yasa yazo suka gaggaisa sannan ta fice bayan ya Mata addu'ar Allah ya bada sa'a.

Ba'a Dan Jima ba sai ga bushra ta fito itama buya yayi a bayan flower zuciyarsa na lugude.

Tuka motan ta take tanata sauri Dan tayi latti motan dake gabanta ne ya tsaya ba tare da bada alama ba aiko sukaci karo kau.
Iska ta furzar tare da saukowa ta cika tayi fam. Shima (yazeed) fitowa yayi kannensa dauke da bluetooth tare da fadin zan kiraka ta harshen larabci sannan ya kashe.

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now