CHAPTER 81

2.1K 163 71
                                    


RECAP

Ayush ne tace brother akwai abin da nakeson in fada maka. Gyara zama yayi yace kaga dai yanzu 7 years kenan da rasuwar mummy sufwan ya kamata ka kara aure ko Dan su. Jin Jina kai yayi yace wannan gaskiya bari zan Nemo musu mummy, kunaso ko? Suka daga kai da sauri tare da fadada murmushin su amma dai sahir abun bai kwanta masa ba.

Ayush tace AI na samo maka kanason ka hadu da ita? Shiru yayi kamin yace
KO BAN GANTA BA NASAN ZABINKI YAYI DON HAKA ZAN AURETA!

CONTINUATION

Akwana a tashi kamar wasa auren yazeed da safina saura sati daya cir. Lokacin da iyayen safina sukaji sunyi mugun mamaki da lokaci daya ta fitar da miji amma basu kawo komi a kansu ba ganin Wanda zata auran mutumin arziki ne ba sha ka tafi ba. Ayush sai rawar kai ake yayinda yazeed ko zaiyi auren ne saboda yaransa Dan shi yanzu ba mace bace a gabansa.

Minal zaune a parlourn ummu suna shan rake taji kamar mararta yadan murda. Dakewa de tayi taci gaba da hira can sai ta fara jin fitsari amma abinda ke damunta shine ta kasa yi Dan ta kewaye yakai sau 10. Ummu run bata lura da zirya hardai abin yayi yawa hankalinta ya dawo kan minal. Koda minal ta zauna ummu tace yar nan ince lafiya dai ko naga sai zirya kike murmushi minal tayi tace ba komai. Abinci ummu ta zubo musu sukaci minal ta dau kwanon zata wanke ummu tace ta barshi itako ta dage tsugunawa tayi ta fara zuba detergent babu shiri ummu ta Mike ta karba tare da fara wankewa daidai lokacin sabi ya shigo yana fito. Wani ashar ya danna tare da dauke minal da Mari har sanda ta fadi kasa Wanda ya janyo tsananta Mata nakuda. Yace bansan cewa ke yar dakikiya bace sai yau idan ba hauka ba ya zakiyi ki saka uwata aiki. Tau! Tau! Kakeji, ummu ta daukesa da maruka har biyu tare da mangaresa.

Hankalinta ne ya iyo kan minal saboda ihun data tsala nan fa ummu tasa ya Kira Mata uwani sukasa minal a daki. Yanda sukaga yini haka suka ga dare, daidai an fara kiran sallan asuba Allah ya albarkace su da........





























































Yan biyu Mata yan cukul cukul gwanin sha'awa,dadi ummu ta dinga ji kamar jikokinta na gaske kankace me makota da munafukai da yan tsurku anata shigowa domin ganin yara. Kowa na tofa albarkacin bakinshi. Saide an fara tuka tsiya da minal ne lokacin da akazo wankan jego tace ai Sam batasan da zance ba saide tayi da kanta haka aka hakura aka barta tunda ba halin ayi Mata karfa karfa.

Sati na kewayo wa aka sha suna daidai gwargwado, inda aka samu sahla da zayyana.
Kuma a wan an rana ne aka daura auren ango yazeed da amaryarsa safina. Har yan kawo amarya suka gaji suka watse ango shiru. Su sahir ne suka shigo suna murna suja rungumeta suna fadin mommyn mu, sannu da zuwa. Yake tayi musu tana Dan tutturesu a dabarance yayinda a ranta take cewa kai indai yarannan kamannin uban su suja dauko toh lalle na jefi tsuntsu biyu da dutse daya.

Dalewa tsakiyar gadon sukayi suna tsalle ta daka musu tsawa tsirata sukayi ta nuna musu kofa sidif sidif suka fice suna kallon juna. Bayan sun fita Safwan yace mommyn nan batada kirki. Sahir yace maybe kawayenta ne suka bata Mata rai. Rugawa sukayi da gudu abinsu ko a jikinsu.

Shiru shiru yazeed bai shigo ba har bacci ya dauki amarya a wajen. Mutuminku ko tun da aka daura aure ya shige dakinsa ya kwanta Baku kara jin duriyar sa ba yanaji aka kawo amarya aka gama bidiri aka wuce tsaki yaja tare da kwanciya haka kawai yakejin haushin kowa dake tare dashi a lokacin ji yake kamar ba shi ba.

Minal kuwa tsakar dare zayyana ta tashi ta fara musu kuka aka bata mama anyi yin duniya amma sai kuka basu suka rintsa ba sai bayan asuba yayinda sahla ta dinga bacci kamar gawa.

BAYAN SHEKARU 8

Dauke shi da Mari safina tayi tare da cewa wallahi sahir idan baka fice mun a daki ba zaka Rena kanka idan ba rainin hankali ba da ban yini ba zaka ganni ne? Tsabar munafurci zaka wani zo wai gaisheni? Kuma saura inji ka fadawa wa ubanku ni da kai ne mangajesa tayi tare da fita ta kunna TV a parlourn sama tare da kure murya kamar cinema.

Mummy ne ta fito tare da cewa haba safina irin wannan murya sukace cinema? Ki rage muryar tv din mana. Tafiya mummy taci gaba dayi amma me ? Sai safina taja tsaki juyowa mummy tayi tace je safina karkiga ina daga miki kafa ko nemi ki kawomin hauka a gida kinaji na ko toh wallahi idan baki kiyayeni ba zaki sani aikin banza da wofi. Mikewa tayi tare da cewa ke tsohuwa dakata kiji..... mummy ne ta datse ta ta hanyar cewa uwarki ne tsohuwa.

Daga hannu tayi zata wanke mummy da Mari ayush tayi caraf ta rike hannunta sannan ta yanka Mata Marin. Dariya ta sheke dashi kamin ta tattare zanyi nanfa suka zage dantse suka casu suns zagin juna ayush na fadin dama a karuwancinki na barki kikayi yayinda safina ke fadin ai yafimin zama da wannan Dan wahalar Wanda tunda mukayi aure sau daya ya rike hannuna.

Mummy ne tayi kokarin rabasu aka mangaje ta, ta doke kai da gini ashar ta danna tare da cewa yasin babu abinda zai hana Dana sakinki. Dariya safina tayi tace wai danki, ke bakiji kunya ba ? AI shekarata 2 a gidannan na gano ba danki bane. Kuma da kike zancen saki AI gara zawarci da aurennan saide babu inda zani yadda na wahala na shekaru 8 wallahi kuma bazakuji dadi ba. Kuma wata shegiya tace zata fada masa taga ikon Allah komawa tayi ta zauna akan kujera sai haki take sanadin fadar da sukayi tare da turo Dankwali gaban kai.

Cikin tsoro mummy da ayush ke kallo juna jamin sukayi wuf sula shige daki tare da yin kuskus.

🌹🍀

Abangaren su minal kuwa ta auri sabi saide dukan yau daban na gobe daban ga ummu amina bata da lafiya wannan dalilin kadai yasa minal bata gudu da daga gidan ba.

Zayyana da sahla ne a kofar gida, sahla na yar carafke yayinda zayyana ke yar gala gala akan hanya. Yaran anguwa babu Wanda ya isa ya taka idan zaka taka kuma ka wuce toh dole ta mareka haka yara ke kin zuwa aike saboda ta kasa ta tsare tijararta yafi na mahaifiyar ta.

Da daddare minal da sabi sukayi wani fadan hakan yasa ya zaro wuka zai kokuwa suka fara yi har suka bige lantarkin su. Hankadesa tayi ya fada aiko akayi rashin sa'a ya fada akan wukar ihu ya saki hankan ya tsoratar da minal sosai babu shiri ta dauki sahla wacce take shiru shiru kuma batada kuzari tare da tashin zayyana cijewa ta fara yi minal tace idan baki Mike mun tafi ba gobe zaki mutu babu shiri tarigasu isa bakin kofa tafiya sukayi sosai cikin daren wajajen karfe 3 jiri ya dauke minal ta suma tsabar tashin hankali ga tsoron kisa, ga daukar yarinya gashi yanayin da tabar jikin ummu Anya kuwa ta Mata adalci, iya ta dauketa lokacin da batada kowa kamar nata tayi Mata komai amma da abinda zata saka mata dashi kenan? Kai amma yaranta fa tunda dukda ba ita ta kashe sabi ba ita za'a daurawa balle ansan basa jituwa. Ga ummu kuma rai a hannun Allah hawan jini ya addabe ta.

Jijjigata suka fara yi suna kuka suna kiran sunanta wani ya haskosu da tocila tare da cewa kai! Su waye a wajen ne? Matsowa kusa yayi ganin kamar yara ne. Haska Fuskar minal yayi cikin rawar baki yace YAR UWA? KECE?

KO SHIN WANENE WANNAN MUTUMIN? TAMBAYAR MAI SAUKI CE AMMA DUK WANDA YA ANSA TA TO CHAPTER BIYU NA GABA DUK NASHI NE SHI DAYA.

TEASER/CIKIN CHAPTER NA GABA: minal zata hadu da yazeed.........

MASHA ALLAH, AYI MIN AFUWA JIYA KUN JINI SHIRU,  SAFGOGI NE SUKA SHIGEMIN GABA.

DEDICATED TO @MYNEWFANS.

GOODNEWS: their will be another update today by 5pm insha Allah stay tune.

DON'T FORGET TO VOTE AND COMMENT.

ONE LOVE FROM

Miss untichlobanty 💕

10 April, 2020.

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now