CHAPTER 13

2.6K 225 0
                                    

Janta yake tana turjewa "Dan Allah oga sir kayi hakuri ka rabu dani wallahi bazan kara ba, na tuba,na tuba"

Abinda taketa fada kenan tana kokarin zare hannunta daga nasa domin tasan idan ya kaita Inda sai kaita bazataga da kyau Ba.

Store room yayi niyyan kaita.
Atish!aaaaatiiiish!!aatish!
Atishawan da take sirnanowa yasa ya fasa kaita domin yasan ta fada ruwa sanyi ya kamata ga kuran store kuma?
Maybe ma she is asthmatic. Hakan yasa juya ya canja hanya zuwa side dinshi.
Ihu take tana bashi hakuri amma Allah cikin ikonsa wannan Karen ma hawaye sun dauke kafa

(Nace kekam minal kinga ta kanki sanda ake bukatar hawaye sai su kafe sanda ba'a bukatarsu kuwa yanda kasan ruwan sama me saka ambaliya)

Bakin wata kofa wacce take barin dama da dakinshi kuma next to it ya bude. Wulla ta ciki yayi ta fada kasa sannan shima ya Shiga.
Bakin gado ya nema ya daba mazaunansa sannan ya kalleta yace knee down!babu bata lokaci tayi Kamar yadda ya umarta jiki na rawa

Sai alokacin yakalleta da kyau yarinyace sosai.
Sama da kasa yamata aranshi yace kwailace ma amma she has the guts to..........iska ya fesar a bayyane yanaci gaba da kallonta.

Itako ganin ya tsare da ido yana mata kallon tsana yasa jikinta yayi sanyi Ashe bazata kara ganin innarta da baba Ba? gashi ya Abubakar ma ya kusa dawowa nanda wata shida shima bazata gansa Ba?

Gashi dije ma takusa dawowa saga boarding Ashe bazasuga juna Ba?

Ashe ajalinta ne ya fito da ita?dama mafarkin mutuwa da taga tayi Ashe zai zamto Gaskiya?

Maganar da yazeed yayi yasa ta dawo daya tunanin da take.
Ke?kin iya up and down?
Harara ta banka mai yasin bazanyi Ba

Kallonta yayi da mamaki da kuma takaici Wai ita bakinta baya mutuwa ne?shi tunda yake banda zakiyya babu mai iya kallon idonta ma tamasa magana balle tsiwa ko zakiyya ma tasan lokacin da take haukanta. hmm zaiyi maganin yarinyarnan da alamu kanta yana rawa.

Hannu yasa ya dalle Bakin Wanda yayi sanadiyar fitar jini kamin yace
Mike ki fara up and down!
Jikinta na rawa ta fara kwanciya yayi ya rufe idonsa fuskarsa na kallon sama.

Sanda tayi kusan na Minti Biyar alokacin ta gama had a gumi sannan ta dubeshi tace oga sir kayi min rai
Wallahi bani kara maka rashin kunya jin shiru ba'a amsa mata Ba yasa ta tsaya da punishment din ta sansado ta leka fiskarsa ganin idonsa a rufe yasa tace
Kutma lallai ma mutuminnan Dan rainin hankali ne.
wato ga inji ko?inyita aiki shi yana bacci,wallahi Allah ya isa na.

Sanda takeyi harta iso Bakin kofa zata fita taji yace
Da izinin zaki aikata hakan?kuma Waye Dan rainin hankalin?

Juyowa tayi a zabure tana zare ido dama Ba bacci yake Ba?
Wayyo Allah bakinta yaja mata.
Zama yayi yace dawo ki zauna.
A hankali take takowa Kamar kazar da kawai ya fashewa a ciki harta tsuguna

Gabansa ya Muna mata ta matso tana zare idanu harta rame Kamar Ba ita ba.
Yazeed yace dago kanki dagowa tayi amma idonta a kasa.
Yace Nayi kama da sa'anki? Ta girgiza kai.
Yace kinada matsalar kwakwalwa ne?ta sake girgiza kai. Tsawo ya saka mata yace use your fucking mouth !

Itadai bata gane ba saboda accent dinsa ya mata tsauri amma sai tayi shahada wajen Cewa kayi hakuri.

Yace kintaba ziyartar gidan mahaukata ne?domin kinyi kama dasu

A ranta tace kutma wallahi ni banyi kama da mahaukata ba Saide kai ne mahaukacin.

Kaine mahaukacin shi ya bayyana azahiri wadda bata masan ya fito ba
A fusace ya mike ya yarfe ta da mari yace nine mahaukacin ?tana girgiza kai tace tace a ah dan Allah na rokeka kayi hakuri subutan baki ne bazan kara Ba. Ball yayi da ita ya fita tare da sawa kofar dakin lock yana ma fadin zan nuna miki hauka yar budurwa!

Koda ya fita waje idonshi yayi ja lukman ya gani yace ya kawo masa igiya

Cike da mamanki lukman din ya dauko igiyar yana nazarin me ogan nashi zaiyi da igiya? Dan shi baiga alamun saniya a gidan Ba lol.

Saniya minal za'a daure

Jin shiru bai dawo Ba yasa ya kwada masa kira domin ya tsani waste of time.

Da gudu yazo a kasa da da'ki'ka 2 domin Dan tazarar dake tsakanin side dinsu da kuma main one

Miko masa igiyar yayi yana Cewa oga yaushe za'a mayarda yarinyar?
Yazeed yace my friend, get out of my side!

Har lukman ya fara tafiya yazeed yace zonan.
Dawowa yayi yace masa ya batun Jamal din Ba nace a dauko shi Ba? Lukman yace su bala ne suka tafi Daukoshi.

Juyawa yazeed din yayi ya tafi Ba tare da ya tanka masa Ba.
Shiga dakinsa yayi ya samu minal Inda ya barta tayi jugum

Ba Komai ke damunta Ba illa wani bahagon yunwa domin tana fashin sallah,Kamar dai yadda kuka sani minal muguwar acici ce.

Mu hadu a next chapter domin jin yadda zata kaya tsakanin minal da yazeed.

Gaskiya you need to support me by voting, commenting, and most important sharing

Thank you!

18 June 2019

Mzz untichlobanty💕

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now