CHAPTER 83

1.9K 154 55
                                    

RECAP

Zayya tana isa taga wasu yan Mata suna fadin baiwar Allah ya haka zaki zauna da yarinya me bacci a titi kina kuka dauke kai tayi ganin sun takura yasata cewa ta mutu.... zayya tace me?! Ummu me kike cewa sahla ta mutu? Har idonta ya ciko da kwalla ya fara zuba faduwa tayi a guiwanta ta matso kusa da ita tace kanwata karki barni Dan Allah.  Daya daga cikin yan matan ne tace karkice ta mutu muje gida a kawo likita ya duba ta dai tana da rai.
Mikewa minal tayi cikin fitar hayyaci tace kin tabbata tana raye baiwar Allah karki sakamin rai fa.
Sai a lokacin suka kalli fuskarta take suka ja da baya baya sunan fadin wayo Allah mun shigesu. Nafeesa tace aunty me nake gani haka?

CONTINUATION

Nafeesa wacce bazata wuce shekaru 18 ba tace aunty me nake gani haka? Me aunty bushra keyi anan ba yanzu muka barota a gida ba? Dakata, y
anzu na gane abinda sabir ke fada dazu Allah sarki ashe da gaskiyarsa

Mintuna kadan da suka wuce

Sabir na komawa gida ya iske wannan labari haka yadan bi sawu amma bai gansuba cikin tashin hankali ya nufo gidan da yake gadi domin su taimaka a sanar a gidan rediyo, talabijin da sauran su.

Acan kuwa......
"Oyoyo aunty Bushra sannu da dawowa" nafeesa wato feena ke fadin haka yayinda ta rugo a guje saura kiris ta fadi a beni sanadiyyar karar motan da taji. Wata budurwace ta fito daga ciki tana yarfe gashinta dake kan farin fuskarta tare da gyara tabarau din dake manne a idonta murmushi ta saki lokacin da ta sanya kanwarta nafisa a idanunta. Rungume juna sukayi feena na turo baki cikin shagwaba tahau magana...

Amma wani hanzari ba gudu ba na kasa saurara balle har na rubuta abinda take fadi domin nifa ba kowa nake gani a tsaye ba sai minal cikin kananun  kaya saide wannan tafi minal kiba da kirji sannan minal ta fita gashi  da tsayi.

Sauran yan gidan ne suka fito suna Mata marhaban. Ana cikin haka sabir ya shigo duk ya hada gumi yana fadin hajiya wannan baiwar Allahn ta gudu daga gida sabod........
Maganarce ta makale masa a makokoro cikin rawar yatsa yake nuna bushra yace yar uwa me kukeyi anan sannan ina yaran. Wani kallon ka renamin wayo ta mai tace (Dan Iska me ka kirani yanzunnan?) what the fuck did you just called me? Baki ya bude zai bada amsa amma bai samu dama ba sanadin Marin data yanka masa. Mahaifiyarsu ce ta riko ta tare da cewa ke bushra bakida hankali ne zaki daki namiji? Kuma ya girmeki? Banason rashin tarbiyya, au abinda kika koyo a turan kenan? Toh bari mahaifinki ya dawo zakiga ikon Allah.

Hakuri suka bawa sabir Wanda ya kasa yin komai yayinda tayi tsaki tayi wucewar ta. Fadawa tayi a kujera, tayi ciro da takalman kafunta tare da cewa (ji wani mafari mara kyau)what a bad start! Aunty jalila kanwar wacce takeda shekaru 32 maman su tace gaskiya bushra kin bani mamaki menene haka? Ya zaki Mari sabir? Mutumin kirki ga gaskiya kuma.... datseta bushran tayi ta hanyar cewa aunty kuyi min uziri ku siyomin icecream keda feena, kaina ciwo yake zamuyi magana anjima. And please ku zaku siyo kar a bada sako ma driver ko wani kazamin.

Tabe baki aunty jalila tayi kamin ta shiga daki tana fadin aiki ya sameki sannan ta shirya suka fice tare da cewa yarta shameela wacce take sa'ar su zayya ta zauna ta sakawa bushra ido idan tayi wani Abu ta sanar Mata. Ita kuwa abin nema ya samu saboda rawar kai gareta.

Hakuri suka sake bawa sabir sanda ya bude musu gate yace ba komai sannan suka fita suna cikin tattauna halin da ta dawo musu dashi feena tace la aunty kinga wata baiwar Allah zaune da yarinya a hannu ga za'ayi ruwa kuma dai nan ba wajen bara bane. Haka kawai aunty jalila taji tanason ta tsaya dukda yadda zamaninnan ya baci.

Magana sula fara Mata amma taki ta dage kanta balle ta kulasu sai kuka take ana cikin hakane zayya ta dawo......

CIGABAN LABARI

Ajiyan zuciya minal ta sauke tana mamaki da akace akwai me kama da ita. Feena tace aunty zo kiji, cikin kunne ta fada Mata wani Abu sukayi yar shawara.

Tsugunawa tayi a gaban minal tace kinga yanzu ruwa za'ayi kuma da alamu bakida wajen zuwa me zai hana ki biyo mu. Girgiza kai tayi tare da cewa ni yanzu bazan yarda da kowa ba ku barmu ni da yara na kawai mu mutu.

Aunty jalila tace wannan wacce irin... kasa karashe wa tayi sanadiyyar ruwan daya tsinke zayya ne fara rokanta akan su bisu kawai kar ruwa ya halaka yar uwata. Badon ran minal yaso ba tabisu.

Yazeed kuwa suna cikin tafiya ruwa ya balle Abu na farko da ya fado a ransa shine boss ladynsa. Ganin hankalinsa bai kwanta yasa yace su juya koda ya koma yaga wayam haka yanaji yana gani ya hakura.

...........

Suna shigowa gida suka sassauko a motar da sauri suka shiga ciki saboda ruwa yayinda akabar  feena da zayya suna dauko ledan icecream. Shameela na ganinsu tace mummy wallahi kina fita aunty bushra ta sa ya sabir aiki wai ya goge Mata takalma..... aunty jalila tace yanzu tana ina? Tace tana dakin mama.

A waje kuwa daidai zayya ta juya ta hango wani kamar ta sanshi amma ta share batayi magana ba taci gaba da yiwa feena hira suna dariya suka shiga ciki.

Surutun da shameela keyi na ya tsaya lokacin da ta lura da minal dake bayan jalila. Kallon saman beni tayi ta kuma kallo minal sai ta bazama a guje tayi sama cikin haki ta bude dakin mama taga bushra a cikin dakin sai ta kallo minal, ta sake kallo Bushra ta kalli minal kawai sai ta fashe da kuka.

Waiyo umma(abinda take kiran mama dashi) na shiga uku na haukace. A tsorace mama da bushra sukayo kanta suna fadin lafiya ? Nuno minal tayi da yatsa aiko minal da bushra suka hada ido.

Kallo kurilla sukewa juna yayinda mama ke fadin ke jalila me nake gani haka? Murmushi tayi kamin ta fara fadawa mama yadda akayi. Mama tace no wonder sabir ya Kira bushra da yar uwa ya dauka itace ashe.... wani tunani ne ya fado Mata bata karasa zancen ba tace ke dakata hakan na nufin itace Wanda ta gudu yake neman ta. Ke shameela je ki Kira mana sabir, da gudu ta fita a bakin kofa sukayi karo ita da zayya. Tsaki taja kamin ta fice zayya ta bita da kallo. A lalle za'ayi cakwakiya bata sanni bane kar taga nan gidansu ne babu abinda ya dameni wallahi wulakanci zan Mata kar taga gidansune.

Ganin kallo yayi yawa yasa feena tambayarta ko ta Santa ne? Tace a ah.
Haka dai sabir ya shigo ya roki afuwar su sannan aka duba sahla inda aka tabbatar tanada rai saide a halittarta bata juran wahala.

Minal da bushra dai basu cewa wa juna komai ba har dare yayi sukaci abinci. Ba ciki na ciki, minal ta kasa gaskata akwai me kama da ita yayinda bushra kejin haushi ya za'ayi ita da take ganin tanada kyau ace wata banziya gayyar talauci tana kama da ita har ma ta fita kyau.

Wasa wasa lokacin na tafiya safina hargutsa gidan yazeed baki daya. Yayinda sahir ya tafi cambridge university karatu safwan kuwa yace a kasarsa zai makale babu inda zashi danshi Dan baba ne.

Bayan shekaru 6

Da baya baya yake ja idonsa cike fal da tsoro kamar kulya a lungu kafarsa na mazari Dan yasan kashinsa ya bushe tunda ya sake ya jefi zayya da ball.

Gefe kuwa yan team dinsu ne tsaya suna cika suna batsewa. Kirbashi ko ta soma tun yana ihu har ya daina da alamu ya suma yarda shi tayi ta juya zata tafi ogan team din cikin harshen turanci yace ke kina tunanin kin daki banza ne ? juyowa tayi suka hada ido.

Ido cikin ido suka fara nufo juna gaba daya daliban da suka taru suna kallo baya baya suka fara yi Dan sunsan yau za'ayi world war na 3.....

Don't forget to vote, comment and follow me. I repeat vote and comment ooo.

DEDICATED TO: aysherahmaddanlami

Love you all💋❤

Miss Untichlobanty 💕

14th April, 2020.

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now