QUESTIONS AND ANSWERS

2.7K 202 44
                                    

CHAPTER 59 IS LOADING..........

A Gaskiya bazan boye muku ba inajin dadin comments  da goyon bayan da kuke bani alla h ya barmu tare.

Saide wani hanzari ba gudu ba na lura da Cewa bakuyin sharing kuma a Gaskiya Allah ya gaji ban fara rubutu Dan Nayi Suna ko wani Abu ba. Na fara rubutu ne domin na fadakar kuma na nishadantar kinga Idan har wasu bazasu karanta su karu dashi na Toh ba anfani ai.

Anyway enjoy!

🌹🍀TO YAZEED🌹🍀
Q1. yazeed shin kana ganin minal zata soka?
A. Kaji wata tambaya to dama Dan wa akeyin littafin badan Inda ita bane? So na wajibun.

Q2. Yaushe ka fara son minal ?
A .nima ban saniba Gaskiya.

Q3. zaka saki zaliha a nan gaba
(Yazeed yana harara) so kike untichlobanty ta shafeni a labarin saboda na bada Satan answer?

Q4. Waye kake ganin yake muku Muna furci a gida ?

A. Da nasani zan bata lokacin wajen kawo likita Dan yayi wa Jenifer magani ta warke ta fada min ne?

Me tambaya:Allah ya baka hakuri.

Q5. Idan ka kama me hada maka zafi a gidan ka me zaka mata? Ooooo kun fiya tambaya wallahi. Ke untichlobanty ki kwashe wa dannan fans din namu Kuyi gaba.

Untichlobanty: (kasa kasa) kaifa Ba ubana bane balle ka bani umarni ko ka tsare ni.

Yazeed: me kikace?

Untichlobanty:(ina tutturo baki) banyi magana Ba. Sisters kuzo mu tafi wajen minal

🌹🍀TO MINAL🌹🍀
Q1. Ya kike jin zamanki da yazeed?
A. Gaskiya Ba laifi Dan ban taba tunanin rayuwa zata yi mana dadi Ba.

Q2. Wa kike ganin itace makiyiyar Ku?
A. Aunty zakiyya kowa zai fara zarga Toh amma ai harda ita a ciki kuma nata yafi yawa.

Q3. Waike bakya kishin zakiyya ne?
A. Inayi mana amma ya na iya dole na danni zuciya inyi hakuri wata rana sai labari.

Q4. Ya kikaji sanda yazeed ya fara sunbatarki ?
A. (Cikin jin kunya)Wani Abu naji yana mini yawo ajikina sannan ya ratsa ko wani lungu da sako.

Untichlobanty:(cikeda karadi) muma dai Allah ya kaimu lokacin mu🙌

Kowa ya kuramin ido...

Untichlobanty: ina..ina nufin Allah ya nuna mana lokacin bikin su....su ya Abubakar (Sosa Keta tareda kallon gefe)

Q5. Ya kike ganin zata kasance tsakanin zaliha da lukman?
A.(gutsiran Awara, tattaunawa)

Untichlobanty: minal bakiji sister tana tambayanki bane?

Minal:(sake gutsiran awara tareda kurba zobo) tunda gasu a gabanku sai Ku tambayesu ai.

Untichlobanty: Dan sammin awaran Toh

Minal:(harara Kamar zata kasheni)

Untichlobanty: sisters muyi gaba ko?

🌹🍀TO ZAKIYYA🌹🍀
Q1. Sannu zakiyya ya jikin?
A. Tambayata kukazoyi ko ya jiki?
Mai tambaya: Allah ya baki hakuri.

Q2.Wa kike ganin ya kona miki shagonki?
A. (Cikin Daga murya)Masoyin mutum zai rabashi da arzikinshi ne? Kunsan dole makiyinane mana. Mtsw waya sani ma ko dangin shegiyar nan ne?

Minal:wallahi ni Ba shegiya bace

Zakiyya: ke zan faffasa miki baki.

Yazeed: order please!

Zakiyya and minal: (hararan juna)

Q3. Bakyajin kishin minal ne?
A. Mtsw ji wani tambayan banza! A woman with class like me ne zanji wani Abu Wai kishin minal? You are not serious. Next question please.

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now