CHAPTER 85

2K 178 43
                                    

RECAP

Wayanta halsey ta dauko suka dauki selfies. Daddare zayya ta dauko diary dinta ta fara rubutu:

MONDAY– 6 JUNE

Yau nazo sabon makaranta na kuma wallahi kyau gareshi gashi nayi kawa mai suna halsey saide akwai wata banziya wai ita vanessa amma zanyi maganinta idan ta shiga sabga ta.


CONTINUATION

Halsey ne tace zayya ki tashi muje muci abinci, zayya tace okay tare da rufe diary dinta suka fita. A layin siyan abinci ma haka aka dinga kallonta itako babu abinda ya shafeta.

Cikin dare suna bacci sukaji ansaki key a kofar dakinsu za'a bude. Textbook zayya ta dauka yayinda halsey ta dauki takalmi. Zayya ne ta bude tare da rafka ma Wanda ke bakin kofan textbook ashe hostel incharge ce ta kawo musu roommate dinsu me suna "na yeonsil" yar southern Korea ce.

Washe gari aka fara karatu zayya da taga ba gane komai take ba kawai tayi kwanciyarta.
Mafarki ta fara yi wai gata a kwace sanye da  kayan snow white sai  ga yarima yazo ya sumbace ta murmushi tayi ta fara bude idonta a hankali amma me tana bude idonta ta soma ihu tsabar muninsa.

Aiko ihun ta kwalla a gaske tana mai goge bakinta da tufarda da yawu bai tsaya a ko ina ba sai fuskar malamin su yayinda kowa ya tsura Mata ido.

Detention ticket (tikitin ladabtarwa) aka yanka Mata, cikin harshen hausa tace kai nikam na shiga uku tun ranar farko zan fara shiga detention? Malamin nasu Dan Korea ne yace kimin shiru kamin yaci gaba da darasi.

Lokacin break suka shiga ban daki domin gyara kwalliyar su kamar yadda kukasan al'adar farin fata. Watsawa fuskarta ruwa tayi tare da sauke ajiyan zuciya tace in tambayeki mana halsey.

Idan mutum yayi mafarkin Dan sarki me hakan ke nufi? Halsey tace me kukayi dashi a mafarkin? Dan Sosa kai tayi tace kawai rike hannu mukayi. Tunani halsey tayi tace nide ban gane ba. Yeonsil dake kan shadda idan ta fadi ko wani kalma sai tayi nishi tace hakan na nufin zaki hadu da masoyinki a gaske. Juyowa sukayi su duka biyu suka kalli kofar ban dakin da take sai ki kake fatatata ta saki zawo.

Zayya kuwa gira daya ta daga ta ce WAYE SHI?.......
Bayan an tashi gaba daya zayya tayi sneaking ta fita daga makaranta ta siyo popcorn tana tafe tanacin abinta. A hanyarta na dawowa makaranta tayi Tuntube ya zube hakan yasa ranta ya baci ga su halsey na kiranta wai tayi sauri ta dawo kar a gane batanan. Tuno baki tayi tana tafiya tana kwallo da duk abinda ke gabanta.

Sahir ke take totir din motansa me budadden sama kawai yake Dan ya samu yancin watayawa babu speed limit a Nigeria shiyasa ma yaki fitowa tare da safwan.

Zayya kuwa wani gwangwani ta gani a gabanta cikin nauyin zuciya tayi shot dashi bai fada a ko ina ba sai goshin sahir aiko ya daki streetlight Wanda hakan yasa ya fara habo yayinda taci gaba da tafiyarta tanaji kamar tayi kuka.

Fitowa yayi tare da daukan gwangwanin dadin abun hanyar babu kowa. Yace hey! Ke ! Ke me UNIFORM! Juyowa tayi cikin harshen turanci yace bakida hankali ne? Tace kai kuma waye kai? Yace waye ni? Mamallakin wancan motar tare da nunawa da yatsarsa. Tace toh sai akayi yaya? Me alakata a ciki? Ta fadi haka fuskarta na nuna alamun rashin fahimtan inda ya dosa

Iska ya furzar tare da nuna Mata gwangwanin yace ke kika jefar da wannan? Tace bani bace. Yace amma ke kikayi kwallo dashi ko ta daga kai. Cikin masifa yace kaji karamar yar iska kin dauka lamarinnan wasa ne? Saura kiris ki kasheni !

Itama cikin daga murya da canja Fuskar abin tausayi zuwa yatsine tace me kake nufi ? ai ba da gangan nayi ba. Kuma wallahi ka fita daga idona na rufe Dan yanzu haka raina a bace yake.

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now