CHAPTER 70

3.5K 214 53
                                    

Rufe ido zakiyya tayi sakon da sumaiya ke aika Mata na ratsa and then it click to her Cewa wannan abin zunubi babba.
Babu shiri ta hankadeta tare da cewa me haka sumaiya ina maman taki take? Dariya summy ta sheke dashi tace shegiya ni. Ji muryarki yadda kike magana kamar yar kwaya tsabar jarabar Dana tado miki, wa yace miki inada uwa?Matsowa tayi kusa da ita tana yauki tare da shafo Fuskar zakiyya tace haba my zaky basai mun tsaya muna ja inja ba. Mari zakiyya ta yarfa Mata tace kin bani kunya wallahi am ashamed ashe ke fasika ce ban sani ba?kazama,dakikiya kuma jahila? Ke nayi miki kama da yar iska ne? Dariya summy itama tayi tace hmmm lallai ma zakiyya bakisanni ba.

Marinta ta Rama tare da cewa ince ke wayaiya gaki matar manya ko? Kiyita dressing kina bude tsiraici, toh kin budo ni kuma na gani kuma ya min,kuma sai na samu. Tsaki zakiyya taja ta dauko key din da summy ta ajiye ta bude kofar tana kokarin fita summy tace me zakice idan nace kina sa kafarki wajen dakinnan zaki rasa uwarki.
A zafafe zakiyya ta juyo tace ke banson hauka kina jina ko? Karki kuskura kisa uwata a shirmennan naki. Dariya summy ta fashe dashi da kaji amon sautinta babu imani a cikinsa. Tace uhmm su hajiya zakiyya manya!dariya ta kuma fashewa dashi sai lokacin zakiyya ta lura cewa summy ta girmeta sosai,sannan ko dacewa basuyi a matsayin kawaye ba. Zuwa yanzu daga skin tight sai bra ne a jikin summy Wanda zakiyya bata ma San yaushe ta cire kayan ba. Kallon jikinta yayi taga hijab dinta ne ya yamutse.

Kauda kai tayi daga kallon summy dake tunkarota hannunta rike da tablet, nuno Mata video call ne. Mamanta ne a daure a wani store ta jigata sosai da alamu duka aka Mata bakinta har yau yake tsiyayarwa. Tace zakiyya ki taimaka ko me sukeso kiyi musu. Zasu kasheni ke daya zaki iya cetona. Ki taimaka ko biya musu bukatarsu ! Karki tuna abubuwan danayi miki a baya nasan ban kasance uwa ta gari a gare ki ba. Nayi miki alkawari bazan sake ba zan nuna miki soyayya ta uwa wacce ko wacce a diya ke bukata...

Lokacin zakiyya ta Dade da jikewa da hawaye itakam ta shiga uku tana tsaka me wuya ta bangare daya ran mahaifiyarta dayan bangare kuwa hakkin Allah. Shiru tayi tana tuno maganganun da tayi da minal wata kila zata samu mafita a ciki.
Summy tace kamin na kirga 3 ki yankee shawara. Bindiga aka saita Akan mommy take ta fara cewa don Allah Allah zakiyya dan Allah.

Summy tace 1............. dogon nazari zakiyya ta fara shin mommy ta cancanci ta sabawa Allah saboda ta cecota? Idan ma ta ceceta akwai probability cewa bata tuba. Toh amma uwa ce fa uwa?

Summy tace 2.......... yanzu idan tana cikin sabawa Allah ita da mommyn suka mutu dukansu fa ? Asara bibbiyu kenan. Kai Anya kuwa momy ba so take ta danna kaina a ruwa ba in mutu ina madigo ta mutu tana mushrika? Ajiyan zuciya ta sauke tunowa da yadda mahaifiyar Tata ta dinga bin bokaye har kwanciya tayi dasu duk saboda ta hana mahaifinsu yi Mata kishiya.

TAUUUUUUU !! Taji hakan yasa ta tsorata sosai ta saki tablet dake hannunta summy tayi saurin cafewa tare da cewa ke ya haka zakiyi min asara. Kallon cikin wayan tayi tace wow ji yadda kwakwalwarta ya fito. Don Allah ku fasamin cikin ko naji dadi a raina. Saukar bullet kakeji tace ku cire hanjin ku saka roba zan aikashi wani gur koda ta juyo ta kalli inda zakiyya take tuni ta sume. Tabe baki tayi tace ke kika jiyo dama nima ba bukatarki nake ba. Wayarta ta dauko ta danna Kira ringing 4 yayi kamin aka dauka. Tace hmmm AI tayi taurin kai Dan haka dayan option din mukabi. Allah keson ya ceci Aurenta. Kyaci tayi tace wallahi madam naso ace ta bada hadin kai na rakashe kuma wallahi na saita camera din yadda zai daukemu dakyau da kawai sai mu rife fuskana my sambadawa mijin. Tsaki aka ta dayan bangaren tare da cewa barta hakan ma ya isheta zamuyi tunanin wani abin. Dariya ta kyalkyale dashi tace zakiyya wallahi ko kinki ko kinso sai kin rsbu da yazeed.

Summy tace ma ya zamuyi da ita? Tace Kira su kyankyaso kice su dauketa su yar a wajajen gidanta amma karsu karasa saboda kinsan security din wajen. Suyi using wayanta suyi contacting din wani yazo ya dauke ta sai su ajiye Mata a wajen. Summy tace okay amma kamin a mayar da ita zan iya ......... kingane AI.

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now