CHAPTER 66

3.2K 209 9
                                    

Hospital din dasu ayush suke suka fara zuwa nanma likitan yace baza'a iya moving dinta ba saide nanda Dan wani lokaci yazeed yace karka damu wannan da kake gani  ya kware a fannin shiyasa na kirawoshi yazo har kasannan so he can take care of her condition. Doctorn yace mr yazeed are trying to say mu bazamu iya aikin mu bane ? Yazeed yace ba haka nake Nufi ba. Inaso be dai ayi moving dinta hospital da take akwai komai and tight security. Dr yace ok I will try my best domin keyi moving dinta amma yanzu Kam mashkur yace can I check on her? Dr. Yace that's against the rule tunda ba a hospital dinnan kake aiki ba sannan permission da aka baka is only restricted to (iyakarsa)FIRST CLASS MULTI SPECIALIST ne idan ba under emergency ba wato bukatar gaggawa.

Yana gama fadin haka ya wucesu tare da shigewa office dinsa dama saga dakin da ayush ke kwance ya fito.

Kebewa gefe yazeed da mashkur sukayi Dan yau ba'a taho da luku guy ba.
Acewar yazeed ya zauna ya angonce.

Kuskus suka fara mashkur yace nifa ban yarda da likitan nan ba. Idan ba haka ba ya za'ayi yace baza'a iya moving coma patient zuwa wani hospital ba alhalin she is out of danger?
Wanda akwai risk ma shine idan za'a fitarta waje kuma shima za'a iya. Yazeed yace ni dama can bai kwanta min arai ba so abinda zamuyi mu dauki abunmu mu mayar gida sai ka kuka da ita sauran sai a barsu a hospital Dincan ko kaga za'a ragewa my zakiyya wahala ma.
Mashkur yace haka zamuyi nan suka sanarda mom tace hakan ma yayi Dan kallon da likitan ke Mata bai kwanta Mata ba domin kallon banza take Mata na yan iska domin akallon da yake Mata babu alamun aure yake sonta dashi.

Ran yazeed ne yayi mugun baci Dakyar suka lallabashi ya huce. Koda suka fadawa dr din tuburewa yayi aishi Sam Baza'a fitarda ita daga nan ba yazeed ne yayi kwalarsa tare da yarfa mai tafi sanda bakinshi ya fashe yace na baka 30min a shirya komai domin mayar da ita gida. Zamuyi arranging komai kaji ko? Da sauri ya daga kai yazeed yace maza maza go to work.

Kafin minti 30 an shirya komai sannan aka hadasu da nurse yazeed yace bayaso zasu iya kula da ita sannan zasu dauko nurse daga asubitin da suke zuwa wato FIRST CLASS kuma kabilar China ce ma.

Aiko haka akayi bayan an mayar da ita gida tare da nurse dinta akace mom da minal su zauna a gida ujili ujilin yayi  yawa. Minal ce ta lallabo zakiya akan taje tayi su Wanda ta shirya taci su abinci ba musu tayi koda ta fara cin abinci kawai sai ta fashe da kuka a tsorace minal da yaranta sukayo kanta suna tambayan lafiya tace tunda nake ban taba cin abinci mai dadin wannan ba saide abin takaicin ni ko abinci ban iya dafawa ba amma yarinya kamarki ta iya sai yanzu nake nadamar rayuwar da nayi a baya dadina daya Danayi nadama run lokaci bai kuremin ba yake yar uwata amina shin zaki koyamin rayuwar zaman aure? Daga kai minal tayi zakiyya ta kuma cewa shin zaki koyamin addini na? Minal tace da izinin Allah sauko wa kasa tayi ta rike kafafun minal tana fadin na roke ki da Allah ki yafe min duk cin mutuncin da na miki.

Dagota minal tayi ta sauri tana fadin babu abinda kikamin Wanda naji haushi ma na yafe miki tun da dadewa Allah ya yafe mana Baki daya daganan suka rungume juna cikin farin ciki. Mom dake sama tana kallonsu ta share guntun kwallarta yayinda su sahir suka fara tsalle da waka suna fadin mommy da mommy sun zama kawaye!
mommy da mommy sun zama kawaye!!

Dariya su minal sukayi kamin zakiyya ta share kwallarta taci gaba da cin abinci can tace toh yanzu kamin komi ya kankama mu fara karatun me zaki fadamin Wanda idan na rike bazan tabe ba.
Murmushi minal tayi tace idan akace Allah ya hana Kaza ko annabi ya hana toh karkiyi komin dadinsa domin zaki iya mutuwa kina aikatashi akwai situation da idan kamar Ansaki kiyi ok a kasheki toh idan fada akace kiyi sai ki fada amma niyarki ta kasance a tsarkake idan ko aikatawa akasa ki kiyi misali kisa to karkiyi gara a kasheki saboda ta iya yuwuwa Wanda akasa ki kashe din rayuwarsa tafi taki anfani ma al'umma toh kinga gara ki mutu da ya mutu kinga kenan Kamar kin ceci Ranshi ne kuma kinyi shahada tunda kasheki akayi. Manzon Allah (SAW) yace Duk Wanda ya cecin ran mumini Kamar duniya ya ceta sannan duk Wanda ya kashe mumini toh kamar ya kashe duniya ne baki dayanta.

Ajiyan zuciya zakiyya tayi tace amma na gode Allah ya saka da khairi Niko zanyi riko da wannan shawara taki su sahir sukace muma zamuyi. Rungume su minal tayi tace Allah ya muku albarka zakiyya ma rungumesu tayi baki daya harda minal.

Karan fashewar glass yasa su tsorata suka kalli inda sautin ya taho.........

🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀

Su yazeed Suna zuwa hospital suka wuce ward dinsu. Gaishe da ummie suka Shiga yi suka samu Dr Muhammad ma na ciki. Gaisawa sukayi sannan suka wuce room din da aka ajiye Jennifer. Tayi baki dukda ko dama ba wani hasken arziki gareta ba.

Dudduba su heart beat dinta yayi yaga Is normal sannan some part na brain dinta ya fara functioning she can hear and understand but she can't react.

Dan haka yaja hannun yazeed suka fice yace dude gaskiya addua dinku is very strong ka duba kagani ummie ta tashi and there is a chance Zan iya tashar da Jennifer dinnan. All I need is mu fada Mata wani Abu dazaiyi shocking dinta back to reality tunda dama shock ne yasa ta shiga coma.

Yazeed yace ai da nasan shine zai farkarta da nayi tun da dadewa mashkur yace it might work Nacema ba guarantee na baka ba.

Suna shiga dakin yazeed ya kausasa Murraytare da cewa lukman kuyita dukanta harsai ta tashi ta fadamin Wanda yasata ta zuba mana poison.

Dukan abubuwa suka farayi Kamar dai ana jibgan mutum. Can yazeed yace sa bindiga ka harbe min ita yayinda yake kallon mashkur Wanda ke masa thumbs up alamun tana reacting. Belt yazeed ya ciro ya dakarkare ya laftawa dayan empty gadon dake dakin ki kake Tauuu kamar karan bindiga atake  ta Mike tana shure shure daganan tafara tana fadin kayi Hakuri sir ! Karka kasheni  I promise na manta ! Ka Tausaya karka kasheni. Har ta hada gumi saboda tsoran mutuwa mashkur yace calm down Kinji  wani kararrawa ya dannan before 1min sai ga nurse ta shigo yace ta samo ruwa da sauri ta matso ta kawo ta bata tana mamakin yadda Jennifer ta tashi domin a nasu analysis da sukayi sai nanda 3 months zata farka. Lallai mashkur yasan aikinsa Allah ya gani tun rananda ta fara ganishi taji ya kwanta Mata aranta amma yanzu kam sonshi takeyi.

Bayan Jennifer ta natsu suka zauna a gefenta take ta fara tsurewa kwantar Mata da hankali yazeed yayi ya nuna cewa ba abinda zaiyi Mata. Tambayan duniyannan sun Mata wa yasata amma ta kasa tunawa atake mashkur yasa akayi dakin duba kwakwalwa da ita koda ya duba yes ta Sami memory lost amma kuma babu abinda ya Sami kwakwalwarta dazaiyi causing memory lost din. Wannan Abu shi ya daure masa kai abinda bai sani ba Kuwa shine tsafin da akayi Mata shi ya hanata tunawa kuma bazata taba tunawa ba koda kuwa zataga Wanda yasata aikinne haka yazeed yanaji yana gani ya hakura ya barta danshi tausayi ta bashi ga guilty feelings dake damunshi Dan a ganinshi saboda dukanta da akayi ne yasa ta rasa some part of memory dinta .

Dukda cewa tayi kokarin ta kashesu still baiji dadi ba. Haka suka kama hanyan gida jiki  a Sanyaye.

Na sadaukar da wannan page ga dukkan masoya na Allah ya barmy tare

Takuce karamarsu babbarsu

Miss Untichlobanty 💕

18th January, 2020.

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now