CHAPTER 65

3.3K 241 44
                                    

MASU COMMENTING INA GODIYA ALLAH YA SAKA DA ALKHAIRI NA GODE DA KAUNA.

MASU VOTING KUMA NA GODE ALLAH YA BARMU TARE KU DAURE A DINGA COMMENTING

YAN LABE SANNUNKU TUNDA NI BAN GANKU TA HANYAR COMMENT KO VOTING BA AI BAZAN GANEKU BA

ASHA KARATU LAFIYA

Bayan sun gama hotunansu su sahir ma sukace a watsa musu haka ko akayi suka dinga selfies masu kyau tunda yanzu bazai yiwu a dauki hoton ba dama sahir ne ke daukansu.

Abincin su suka dibo harda su sahir suka zauna a kasa suka lafci jellof din taliyarsu. Safwan ne ya zauna a cinyan minal tare da rungumeta yace aunty minal kakci yabu dani dan Allah, ina conki. Brother kaima kana conta ko ? Daga kai sahir yayi. Murmushi minal tayi tace nima ina sanku kuma bazan rabu daku ba kunji yaran albarka. Safwan yace aunty minal ni a dakinki zan kwana. Safwan yace brother ka manta daddy Cewa yayi mu dinga ce mata mommy? Zaro ido sahir din yayi yace hakane fa na manta ne. Hira suka cigaba dayi abinsu kamin bayan sunyi sallan magrib suka Koma gida.

Tambayansu minal tayi ko sunada home work su kace mata ai sunyi Hutu Al Qur'an ta dauko ta zaunar dasu tace su karanta mata har zuwa Inda suke sai ta kara musu.

Safwan ne ya kalli sahir yace yaya sahir wannan din diccinayi (dictionary) ne?
Hararansa yayi yace dictionary akace. Nazari ya fara yi saboda tambayan Dan uwan nasa kamin yace nima ban saniba sannan ya kalli minal yace momy ai mu bama karanta dictionary a makaranta.

Kallon mamaki minal ke binsu wato Suna nufin basu masan Qur'an ba?
Shafa kan sahir din tayi tare da murmushi tace wannan ba dictionary bane. Wannan littafin addini musulunci ne. Kar duniya babu littafi me tsarki da muhimmanci irinsa kuma yanada anfani ga rayuwar mu baki daya. Da badan shi ba da abubuwa sun tabarbare mana shi yake nusar damu abinda ya dace muyi.

Kallon kurulla suke mata da alamu Suna shanye information din ne. Safwan wato karamin yace momy kinaso kice min shi Kamar guide ne?
Tace good boy you are smart shi din guide ne.
Jinjina kai yayi yace aiko mommy Idan haka ne Daga yau kullum sai na kayantashi kuma Nayi alkawari zanyi aiki daci dadai gwaigwado.
Sahir yace nima haka na miki alkawari momy.
Dadi minal taji sosai ganin yadda yaran ke son karatun addini kuma itama tayi alkawari zata yi dai dai gwargwadon ta wajen koyar dasu.

Shaking hannunsa tayi tace Toh zamu fara haddacewa yanzu zanga Wanda zai Riga haddacewa duka kuma banida burin daya wuce Idan kun haddace in koya muku fassaransa sannan zamu dinga yin saura littafai sau 2 a sati sauran 5 days kuma na al Qur'an ne.

Dadi sukaji safwan yayi saurin rarumar Qur'anin ya bude Jade fuska yayi yayinda minal ta karba tace safwan my boy yara basa taba Qur'an izu sittin kaji. Yace momy menene izu 60 kuma? Tace zan fada muku yana Qur'an yake amma dai izu sittin shine complete Qur'an oya Ku gyara zama mu fara.

Nan fa minal ta fara musu Daga suratul fatiha amma abinda ya bata mamaki shine har sun haddace Bismillah da aya uku. Idonta har cikowa yayi da haiwaye na tausayin yadda rayuwarsu ta kusa tabarbarewa saboda ba'a nuna musu addini ba dukda ko Suna da kai me Kyau. Lallai tabbas akwai abinda Allah ke nufi dasu daya hadasu fatanta dai Allah yasa alkhairi ne.

Sahir ne yace Toh momy me yasa aka rubuta kur'anin bada English alphabet ba. Tace saboda bada English aka sauketa ba an sauke ne a larabci. Safwan yace Arabic kenan tace eh yace amma ai ni ban iya Arabic alphabet ba lokacin da nacewa daddy na ya koya mana sanda muke London yace bayada anfani a garemu kuma bayida lokacin mu muje uwar mu ta koya mana kuma da mukaje muka sami mommy mukace ta koya mana tace bata iya ba.

Jikin minal ne yayi sanyi taji ta tausaya musu. Dukda batasan labarinsu ba tasan sun Shiga gararari gunjin kukan da taji ne ya dawo da ita Daga tunanin da ta shiga. Ganin su tayi rungume da juna Suna kuka.

Safwan yace wallahi dadynmu baya sonmu ya tsanemu kuma momyn mu ma ta tafi ta barmuuu😭😭😭 rungumesu minal tayi tare da basu hakuri sannan tace karsu zamu ai suma iyayensu ne ita da zakiyya momynsu ne kuma yazeed dadynsu ne.

Sallah ta koya musu tare da fada musu with time zasu koyi komai da akeyi a cikin sallah Karfe 9 tayi musu wanka tana cikim shafa musu mai yazeed ya Shiga fuskan shagwaba yayi mata yace kin barni ni daya yarannan sun kwacemin ke. Dariya tayi tace gaba daddy karatu fa mukeyi yazeed yace haba? yara na Ku tabba kun maida hankali kunji. Mommy kizo muje daki.

Tace daddy ka shirya sahir toh saboda mu tafi da wuri tunda shi na shafa shi. Cuku cuku yazeed ya dinga yi da kayan har minal ta gama Shirya safwan sai dariya suke masa safwan yace daddy kanaso inyi maka karatun da mommy ta koyamin? Yace eh kamin muji karanta mai yayi sahir ma yayi yace good good very good for my sahir and safwan. Ku kwanta Kuyi bacci. Safwan ne ya rike hannun minal tare da mata puppy eyes yace momy dake zan kwana. Yazeed ne ya lallabasu tare da musu alkawari kamin su tashi Daga bacci minal zatazo kamin suka hakura.

Koda suka Koma daki suna rufe kofa yazeed yayi hugging minal tare da fadin i missed you baby. Murmushi tayi tace me too.

Zaunar da ita yayi a bakin gado sannan ya mata godiya akan yanda ta rike amanan su sahir.

Murmushi ya mata yace sweetheart rufe idonki. Zan baki surprise.
Rufe idon tayi can yace open your eyes tana budewa ya mika mata form karba tayi ta Duba taga na jamb ne Dana WAEC da NECO tsalle ta daka ta rungumeshi tare da fadin Alhamdulillah zan Koma makaranta.

Dadi yaji aranta yaja kumatunta yace baby girl da Nasan komawa makaranta zai saki wannan farin cikin da na mayar dake tun randa na auroki.

Karatunsu su kayi bayan sun cika form sannan suka kwanta yazeed na fada mata zai tafi wani mission yaso ace da ita zashi amma bazai yuwu ba saboda rananda zai tafi ranan za'a fara WAEC shagwaba ta dinga yi masa har sukayi bacci.

Da sassafe taje ta tashesu safwan sukayi sallah sannan suka Koma bacci.
Dawowa tayi ta kwanta around 7 ta daura breakfast tare da hada na Yan hospital. By 10 kowa ya gama shiru anci breakfast sannan suka hadu a parlour domin tafiya asubiti su Mashkur sai santin abincin suke.

Yazeed ne ya nufi kofa ya juyo ya tabbatar kowa bata kallonshi sai ya kashe wa minal ido tare da blowing kiss abinda bai saniba shine kowa yana fakonsa Dan haka aka fashe masa da dariya ya Daga kai ya fice yana mai danne dariyarsa.

Fans Kiyi hakuri wallahi na zama busy daya wa ne shiyasa chapter din babu yawa love you all

Ga channel Dina na YouTube fatan zakiyi subscribing.
https://www.youtube.com/channel/UCjE7XttaGFjEBamBPDRNCbg

Takuce karamarsu babbarsu

Miss Untichlobanty 💕

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now