CHAPTER 9

3.1K 212 17
                                    

Juyowa yazeed yayi ya kalli zakiyya
yace oh gush! look at the mess you caused!
Minal ko lokacin da ta d'aga idonta taga Wanda ya watsa mata ruwa ya juya yana magana da wata(saboda motar Ba ita yake using ba babu tinted)abin ya mugu bata haushi

Minal ta fara magana a hankali lallai ma mutuminnan ya watsa mini ruwa sannan ya tsaya magana da budurwarsa?

Mikewa tayi zata zazzaga masa rashin mutunci daidai lokacin me motan nan ya fito yazeed dake shirin fitowa shima yace bawan Allah kayi hakuri....

Mutumin ne yayi saurin katseshi ta hanyar Cewa wa make gaji Kamar captain yazeed murmushi yazeed yayi yace nine Dan Allah a Duba ma asarar da Nayi sai inbiya ga card dina ya fadi hakan yana kokarin bawa katinsa mutumin yace ka barshi kawai yallabai ai paint nema ya Dan kurje Gaskiya Muna alfari dakai a ka sannan Allah ya kara yi maka jagora yazeed yace ameen amma dan Allah ko wannan ne ka karba mutumin yace waneni ranka shi Dade kuda kuka bamu rayuwarku Dan kukaremu shine har sai na karbi kudinka Dan ka gurjemin mota?ai kake wallahi Ba Komai sai alolacin ya lura da zakiyya cikin fara'a yace ina wuni madam ? Ya tsine tayi kamin kasa kasa tace lafiya tana mai kauda kai.
Dariya mutuminne ya dauke yace ranka shi Dade zamu iya yin selfie? Murmushi yazeed yayi yace Ba matsala. Quick selfie mutumin ya musu sannan ya Shiga motarsa yana mamakin abinda zakiyya tamai dukda ko bai Santa Ba amma da alamu tanada alaja da yazeed din.

Yazeed ko da ya mance da ya watsawa minal ruwa dukda ko laifinta ne tana tafiya ahankali akan titi amma shima harda laifinsa daya biyewa zakiyya ya kunna motarsa zai wuce minal tayi saurin riko hannun kofar

sauke glass yace baiwar Allah dan Allah Kiyi hakuri ban lura bane wallahi hankalina ne ya sauke Daga titin amma kema hada laifinki kina tsallaka titi bakya kallo ki kula Dan Allah

ya fadi haka yayinda ya zabgawa zakiyya harara yana kokarin Ciro kudin a aljihunsa.

ganin zakiyya ta fashe da dariya, abin ya kara bawa minal haushi

Su watsa mata ruwa amma ko su kallo Inda take yarda wani tsayawa Suna surutu da photo da wani mutumi sai kace Yan film bayan sun gama Iskancin nasu zasu ta fita rikosu shine ya wani kwame a mota yana bata hakuri
Sannan budurwarsa tana mata dariya

kwafa minal tayi kamin ta kama kwankwaso ta fara jijjiga tayi kicin kicin da ido

Tace wallahi Allah ya isa na ya za'ayi Ku watsan ruwa kuma kunai mini dariya

Babu abinda yazeed ya tsana Kamar ayi masa Allah ya isa
Hakan yasa shi mugun mamaki amma ganin fiskanta kwalliyar ta cabe bakinnan sai yalki yake Kamar tasha man gyada

Abin ya basa dariya amma ya shanye,50k ya miko mata yace gashi ki siya sabulu kije a Duba ki kiji kanwata ?

Minal tace me kuddin zai min kuma babu wani batun Kanwarka ni karkayi min zakin baki Dan bazaiyi aiki Anan Ba. Ta fadi hakan sannan ta murkutsa baki

The girl is now getting on his nerves

He just pressed his car accelerator trying to leave

Not yet Mr.yazeed abdulmajeed

Wani tsalle minal ta daka ta sake rike hannun kofarsa

Zakiyya babu abinda take sai dariya Dan ita ganin clown takeyiwa minal,fadan nasu yana kayatar da ita hakan yasa ta dauko wayarta ta fara video.

Malam ya zaka watsamin ruwa ka kusa bigeni har na fadi kasa amma ka hakimce a mota kana miko mini kudi me zanyi da kudinka?ai fitowa zakayi ka Duba Lpy ta.

Fitowa yayi a harzuke

Kusa da ita yazo ta daga kanta

Wai Wai Wai wannan dakyar in takai kafadansa ma tabdi

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now